Ticker

    Loading......

Kishi Rahama Ne Ko Azaba // 46 - Alamomin Kishin Mace Da 'Yar Uwanta

1) Kwaikwayo da ƙinsa: Yadda dawwamammen kwaikwayo yake alama na kishi haka guje masa gaba daya kan zama wata alamar dake nuna kishin, wato yadda mace za ta kishiyarta na yin wani abu sai ta fara kwaikwayonta koda ba za ta amfana da abin da take kwaikwayo ba, wasu matan ƙiri-ƙiri suke yi, misali in da wata za ta ga kishiyarta na sayar da gyada sai ta fara sayarwa ita ma, ba kasuwancin ne a gabanta ba ginshiƙi ne na kishi, yadda ake gane hakan kuwa sanya gasa a ciki wajen fuskantar masu sayan kayan, domin ba za ta iya boye abin da yake cikinta ba zai fito ta lafuzzanta yadda za ta riƙa gaya wa musu ita ga yadda take sana'arta a zo wurinta.

Ko ba haka ba ma za ta iya fitowa ta tsaya inda za ta fara ganin masu sayen kayan kafin su ƙarasa wurin kishiyar ta karbe, wani sa'in ta jefa wasu 'yan maganganu kafin ta wuce kishiyar, duk abin da za ta yi ƙoƙarinta kawai wancan ta tanka. Hakan ba zai ishe ta ba sai ta ƙara da gaya wa maƙwabta cewa kishiyar tata na baƙin cikin ta fara irin sana'ar ne kuma an fi son a zo wajenta, bayan ba wani abu da yake gaskiya a ciki. Buƙatarta ta dena wannan sana'ar ya zama ita kadai take yi. In ma kishiyar ta saduda ta bar mata sana'ar ta yi tunanin wata ta dauko don dai a zauna lafiya, yadda kowa da sana'arta daban, ba yuwuwa zai yi ba.

Matuƙar dai za ta ƙyalla ido ta ga kamar an fara gane ta kuma ana zuwa a saya, tsab ita ma za ta fara kawo wannan kayan, don burinta ba zai cika ba sai ta ga ta rufe kishiyar gaba daya ba wace ake maganarta sai ita, fatarta ta karbe komai kishiyar ta dawo ƙasanta, sabanin yadda masu sana'a iri daya kan yi in sun zauna a wuri guda, kowa kasuwa kawai yake nema ba ruwansa da wani. Ko a wannan ma mu maza muna da rauni babba ba ma iya yin abin da ya dace, da a ce za a sami tsayayyen namiji dake kallon abin da yake faruwa a gidansa kuma ya tsaya tsayin daka kan cewa kowa ta sana'arta ba ruwanta da abin da dayar take sayarwa tsab zai magance matsalar, amma da wahala mu iya yin hakan.

Sai dai mu zuba musu ido ko mu yi ta yadawa wance ce da laifi wance ta cika ƙorafi. Akwai abin da ake fadakarwa ne wanda ya kamata maza su fahimta, in aka dubi kasuwa za a ga cewa galibin masu sana'a iri daya a wuri guda suke zama, wani lokaci ma sukan yi kasuwarsu daban, kowa ke buƙatar nau'in wannan kayan can zai tafi, kuma kowa a cikinsu yana samun arziƙinsa ba tare da tsangwama ba, koda yake Allah SW kan fifita wani a kan wani amma za ka taras babu irin wannan kishin, koda kuwa mata ne ke kasuwancin ba maza ba. Dalilin haka kuwa don sana'ar an gina ta ne tun asali a kan kasuwanci ba a kan kishi ba, shi ya sa ba su nufin junansu da wani mummunan abu.

Zan ba da misali: Jiya na ga wani abin mamaki a wurin wasu 'yan mata 'yan shekara 13-14, suna sayar da mangwaro, na kira daya daga cikinsu sai na ga sauran biyun sun taso gaba daya, na ce "A'a ga wace na kira" da kanta ta ce ai haka muke yi malam ba komai duk wanda ya yi maka ka saya. Duk da haka nata kawai na duba na ba ta kudin, sai ta ce a raba za ta ba da na kaza wata dake kusa da ita ita ma ta ba da na kaza, ta gefen kuma in sun sake samun wani sai ta bayar. Tsakani da Allah ban yi niyyar saya da yawa ba, amma da abin ya ba ni sha'a na saya, ban kai gida ba na yi kyauta da wasu.

Wannan nau'i na kwaikwayo ba a kasuwanci kawai ya tsaya ba, harda kwalliya, misali yadda wancan take daurin kallabinta, ko saka jan-baki ko gazal, da ma irin ƙyallen da take sanyawa, ko irin dinkin da ake yi mata da sauransu. Za ka taras wata hatta turaren da ta ji kishiyarta na sakawa sai ta sayo shi ta saka. Maganar gaskiya yin hakan sam ba kuskure ba ne in ya kasance irin wanda mijin yake so kenan, wannan wani fage ne da kowa za ta zu ashutarta don kamo zuciyarsa da kula da ita, akwai lada akwai la'ada a yin hakan tunda manufar kyautata wa maigida ce.

Amma kash! Ba haka abin yake ba, gasa ce tsagwaronta, tunda wance ta sanya kaza ni mai zai hana ni saka irinsa? Irin wannan kishi na kwaikwayo daban, akwai wani nau'in kuma wanda kishiya ba za ta taba yarda su yi abu iri guda abikiyar zamanta ba, in wannan ta yi abu kaza ko wancan wani abin za ta yi daban, kamar dai maganar zama wuri guda, yadda wata ba ta ƙaunar a hada su, wata kuma ta ce ba ta yarda ba sai dai a hada su, kowa da fuskar da take fitowa da ita wurin aiwatar da kishinta.

Misalin wannan in mace ta yi niyyar yin tuwo miyar kuka, sai ta ji an ce kishiyarta ma abin da za ta yi kenan, in sha Allahu ba za a ci tuwonnan ba. Wata ko makaranta maigidan ya saka su ba za ta tafi ba, gwara ta mutu a jahila da dai su hadu a makaranta guda tare da kishiyarta. Sai nake ganin da ma a saye da sayarwa suka yi hakan kowa ta kama gabanta ta riƙe da ƙarfi Allah ya ba da sa'a, in da kishiyar za ta ce za ta sayar da kaza ita sai ta kama wani abin daban, to amma da yake kishin sabanin abin da ake buƙata ne ko tana saba mata a komai ba za ta saba mata a wurin kayan sayarwa ba. Shi kishi kamar yaƙi ne, kullum mutum na kallon gazawar wanda yake kishin da shi ne.

Akwai wace take ƙoƙari ganin yadda za ta baƙanta wa abokiyar zamanta in mijin ya kawo abu sai ta ce ai ya kawo da yawa bayan dayar na cewa ba ya isa, misali in dayar na amfani da manja kwalba daya a kwana hudu, sai ta ce ita sati biyu za ta yi tana aiki da shi, don dai kawai maigidan ya fahimci wancan zaluntarsa take yi. Shi ya sa Shari'a ta yi maza ta hana don kar a riƙa zaluntar wata. Wannan duka ba kwaikwayo ba ne saba wa abokiyar zama ne don a jefa ta rigima da maigidanta.

Har da haka akwai wace za ta riƙa kallon abokiyar zamanta tana ganin yadda take ma'amalla da mutane, in ta ga tana kyautata musu suna son ta sosai sai ita ma ta fara kyautata don samun wannan soyayyar, yin hakan ba aibu ba ne, don ba abin da yake da kama da cutar da wani a ciki. In dai gasa ta shi ciki ne, ya zama wata na yi don kare dayar yadda ba za a ga haskenta ba gaba daya shi ne abin ƙi. Wata rana ogana a wurin aiki ya so sayen fili zai yi makaranta, aka sama masa wani wuri mai kyau, sai dai ya yi kusa da wata makaranta mai dalibai irin namu, sai ya ce "Ba na shakkar za mu ƙwace masa dalibai. Ya yi shekaru da dama anan shi aka sani, bai dace ba mu zo baƙi mu raba dalibansa mu kwashi wasu" shi kenan kuma aka fasa sayen wurin.

A Nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments