TUNA BAYA: Wani lokaci in mace ta tuno rayuwarta ta baya yadda ta sha zama ba miji ba wani mai tayawa, ga sa'o'inta sun sami mazajensu sun yi gaba, ita tana zaune a gida ba mai ƙwanƙwasa ƙofa bare ta bude masa ya shigo, duk lokacin da wani ya zo hannunta dole za ta kama shi gamgam, yadda kowa ta sami miji ta yi aure ita ma ga nata ya zo, lokaci ya yi alhamdu lillah. Don haka idonta gaba daya yana kansa, ya zama wani bangare na rayuwarta da ba za ta yi sakwa-sakwa da shi ba. Don wani abu da zai kusanci rayuwarsu dole a taka masa burki ko ya yake kuwa.
To bare a ce wata na neman raba shi biyu ta bar
mata rabi bayan da ta sakankance cewa nata ne ita kadai. Da zarar maigidan ya
fara kalle-kalle, ko wata ta dan fara shiga idanunsa, a matsayinsa na da namiji, nan ne uwargida za ta ga cewa to fa
ya karya mata jin daɗinta,
ya ƙwace mata gidan da ta dade tana burinsa to ta samu ga shi zai raba shi
biyu, ko kuma wata na neman ƙwace mata, yanzu yaƙin ƙwatar 'yanci za ta yi
tunda gida dai gidanta ne, miji kuma nata ne, mai kusantarta ƙwacen
miji ya kawo ta dole a yaƙe ta. Duk abin da za ta yi kishi ne.
Duk In ta waiwaya baya ta tuno zaman da ta yi ba
mijin, da yadda wata ke ƙoƙarin karbe shi nan ne yaƙin zai shigo, amma da
gaske yadda take tunanin haka abin yake? Gwara ma a ce wata ce ta sha wahala a
hannun kishiyar mamanta har ta samu ta yi aure ta bar gidan, kuma tana jin daɗin inda take zaune, hankalinta a kwance,
to fa tunda kishiyar mamanta ta gasa ta, gani take ba wata kishiya da take
mutuniyar arziƙi. Komai ta gani za ta yi ƙoƙarin kwatanta shi ne da
masaniyarta ta baya.
In sakin mamanta aka yi za ta riƙa
ganin maza ba su da tabbas in ma har akwai din to bai wuce bananta ba, shi ma
gashinan ya saki mahaifiyarta. Za ta yi ƙoƙarin yi wa mahaifiyar hanzari a duk abin
da ta gani. Shi kuma mahaifin ta dauko laifukan duniyannan ta dora masa. To in
mahaifinta ya yi irin wannan munin a idonta wani namijin ne zai tsira? Ita ma
maigidanta zai iya sakinta, 'ya'yanta za su koma hannun kishiyarta ke nan, su
ma ta yi musu irin abin da kishiyar mamanta ta yi mata. Don haka gwara a nuna
mata cewa bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne. Duk abin da za ta yi a
wurin kishi ne.
Wata za ta ce "Yadda mamana ta rasu na koma
hannun kishiyarta ta gallaza min, ni ma in na mutu haka marayuna za su koma
hannun kishiyata ita za ta riƙe su ke nan ta yi musu abin da aka yi min ko abin
da na ga ana yi a wasu gidaje?" Masomin kishin ke nan, a kullum za ta
kalli kishiyarta da wannan idon, sau tari takan kasa mallakar kanta ta sai ta
nuna a aikace. Da zarar kishiyar ta fahimci haka za ta ce ba ta son ta, sai ta
fara yin baya-baya da ita. Babban abin da zai nuna wa mutane ke nan cewa akwai
kishi a tsakaninsu. Mai wayau a cikinsu takan yi ƙoƙarin boyewa har mutane
su gane cewa ga wace take yi. Don yakan faru, sau da yawa a kan dauki laifi a
ba mai gaskiya saboda dayar ta iya tako sosai.
Ba wadannan kadai ba, wace ta girma a gaban
babanta amma kamar marainiya, ko kamar 'yar aiki har ta yi aure, zai yi wahala
ka iya gamsar da ita cewa akwai mutanen kirki a tsakankanin kiyoshi. Duk
lokacin da za ta kalli kishiyarta nan take za ta tuno abin da ya faru da ita a
baya, mata kuma ba sa iya boye abin da yake cikinsu, ko ba kishiyarta a wurin
za ta sauke a kan kowa nata, ba ƙawaye ba har 'ya'ya ma, in wancan tana da 'ya duk
wata wahala ta aikin gida ita za ta dandana, koda kuwa diyar masu gida kusa ba
ta yin komai. A irin wannan hali ba yadda za a ce dan bora ba zai sami matsala
da dan mowa ba. Shi ma kishi zai sami wurin shiga.
Wata ma sam ba ta zauna da kishiyar ba, mijin ne
dai ya ce zai ƙara aure ita kuma ba ta amince da wace za a auro
ba, haka za a yi ta ƙwamawa har su kai ga rabuwa, in ta tashi fita sai
ta kwashe 'ya'yanta gaba daya da hujjar cewa ba ta yarda wata mata ta cutar
mata da yara ba, sai ta fara ƙoƙarin tura musu tsoron zama da kishiyarta, ta baƙanta
ubansu a idonsu, to ko an ce wa yaran su koma can, za su ce sam ba za su rabu
da mahaifiyarsu ba. Don ƙarya da gaskiya za ta harhada har yaran su fahimci
cewa lallai kishiyar warsu dinnan ba kamar uwarsu ba ce rayuwarsu kuma ba za ta
yi kyau ba matuƙar suna hannunta.
In dai wannan din ta ci nasarar raba 'ya'yanta da
kishiyarta, saura tsakaninsu da mahaifinsu, shi ma ba za ta bari su shaƙu da
shi ba don ma kar ya bullo mata ta inda ba ta zata ba ya kwashe su. To fa in
suka girma a hannun mahaifiyarsu bayan ga ubansu da rai kuma yana tare da wata
matar dole kishi ya kurdado, in sun ga kishiyar mahaifiyarsu ko 'ya'yanta to fa
maganar da ake ta gaya musu ce za ta zo musu. Har su yi aure wannan abin na
zuciyarsu, su ma za su fara tsoron kishiya, ko kuma su fara tunanin yadda za su
yi maganinta tunda babu alkhairi a duk inda take. Ba wani abu ya jawo haka ba
sai tuna baya.
A nan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.