Labarin Bala'i Da Abokin Tafiyarsa

    Bala'i ya tashi zai yi tafiya, sai ya nemi abokin tafiya.

    Ciwo ya ce zan bi ka. Bala'i ya ce ban yarda da kai ba. Domin kai da an sha magani sai ka É“ace, kuma wanda duk ka shafe shi, zai samu lada.

    Gobara ta zo ta ce za ta bi shi. Sai ya ce, ban aminta da ke ba. Domin ke idan kin gama aiki sai a sake share wuri a cigaba da rayuwa.

    Sai ga Bashi ya iso yana yi wa kansa kirari: "Ni ke hana mutum barci, in hana shi zuwa masallaci, in sakar masa ciwo marar dalili, in sa shi ƙarya da saɓa alƙawari, in jefa shi gidan kaso, in ya mutu in gaji gidansa da iyalinsa, sannan ba zan bar shi ba sai na tsaya da shi wurin hisabi a gaban Allah!"

    Nan take Bala'i ya ce zo mu tafi tare, tabbas kai ne abokin tafiyata. Babu abokin tafiya in ba kai ba.

    Ya Allahu Ya Ar-razzakku Ya Al-wahhabu ka raba mu da musibar bashi.

    Daga Taskar:
    Prof. Mansur Ibrahim Sokoto, mni

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.