Maganin Sanyi Da Saurin Inzali

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Salamu alaikum Tambaya ta ita ce. Dan Allah Malam inaso ayimin cikakken bayani akan maganin Sanyi da kuma maganin saurin yin Inzali.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalam.. Duk da cewa bakayi cikakken bayanin irin sanyin da yake damunka ba, Kuma baka bayyana irin alamomin da kake ji ajikinka ba, to amma in sanyin da ya shafi cikinka ne ko Ƙirji, ka yawaita amfani da tafarnuwa acikin abincinka, sannan ka rika shafa Man tafarnuwar ajikinka.

    Idan kuma sanyi ne irin na Cutar nan wacce ake dauka ta hanyar Jima'i, ka yawaita amfani da Garin ganyen Raihan da Alhilteet, da Ganyen Na'a-Na'a, ka rika yin surace dasu kana sha kana wanka, in Shã Allahu zaka rabu dashi. Koma wanne irin sanyi ne indai kayi wannan za'a dace. in Shã Allãh.

    Maganin Saurin Inzali Ka gwada wannan: ka nemi Garin wani magani ana kiransa da suna KAMOUN ka gaurayashi da Man shanu, ka rika shafawa ajikin al'aurarka, Minti 20 kafin kaje wajen Matarka.

    Idan zaka je wajen Matar taka sai ka samu ruwan dumi ka wanke al'aurarka sosai, Sannan kaje. In Shã Allahu za'a dace.

    Allah ya sawwaƙe

     ​​Abdulkadeer Umar Alshinkafawy

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vZOO

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.