Matsayin Auren Magidantan Da Basa Sallah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne matsayin magidantan da basa sallah, ko matar ko mijin yaya matsayin aurensu shin sun kafirta ko kuma suna a musulunci?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله والعاقبة للمتقين ولا عدوان إلا على الظالمين.

    Wajibine a kan mace tazabi miji nagari wanda tayarda da addininsa da dabi'unsa, haka shima wajibine yazabi wacce ya aminta da addininta da dabi'unta, sallah tana cikin mafi girman rukunai na musulunci ita cema rukuni nabiyu acikin rukunan musulunci, Bai halatta mace ko namiji tayarda da auren wanda baya sallah ba kuma yake wasa da ginshikin addinininsa ba.

    Idan mace ta auri wanda baya sallah kwata-kwata dangane da ingancin wannan auren akwai saɓanin malamai, jamhurdin malamai sukace auren ingantaccene domin wanda baya sallah bai kore wajabcinta ba hukuncinsa shi ne musulmi fasiƙi amma bai kafirta ba.

    Wasu malaman kuma sukace wannan auren lalataccene, Domin duk wanda baya sallah kwata-kwata kafirine ba musulmine ba.

    Saidai adukkanin halayen wacce ta auri wanda baya sallah amma yaƙudurce wajabcinta baya kafirta saboda baya sallah, ko kuma ita batasan wannan hukuncin ba, ko kuma agarinsu ana fatawane dacewa wanda baya sallah ba kafiri ba ne musulmine mai saɓo, saitayi biyayya gawanda ya ce mata bai kafirtaba daka cikin malaman garinsu, a irin wannan hali ba'a yi musu hukunci da lalacewar aurensu.

    Amma idan mijin yanayin sallah wani lokacin jefi-jefi wannan ba'ai masa hukunci daya kafirta.

    Shaikul Islam ibnu taimiyyah rahimahullah ya ce: Mafi yawa daka cikin mutane, amafiya yawan garuruwa basa kiyaye salloli guda biyar, kuma basa barin sallah gaba ɗaya, saidai wani lokaci su yi sallah wani lokaci kuma sudena sallah, waɗannan sune sukeda Imani da munafunci atare dasu, hukunce hukuncen musulunci nazahiri zasu gudana akansu, wajan cin gado dasauran hukunce-hukuncen musulunci, majmu'u fatawa (7/617).

    Idan miji yakasance amafi yawan halayensa baya sallah, abin da yake wajibi ga matarsa shi ne tayi masa nasiha dayi masa wa'azi da tsoratar dashi Allah, harsai yabar wannan zunubi maigirma, wanda kafircine awajan malamai masu yawa.

    Kuma kada tadebe tsammani wajan maimaita masa nasiha da wa'azi.

    Amma nasiha ga duk wacce mijinta baya sallah kwata-kwata shi ne idan zata iya hakura dashi tanemi wani to ta hakura taje ta auri wanda yake sallah, domin duk wanda baya sallah kwata-kwata kafirine.

    Atakaice dai shi ne ma'auratan dabasa sallah, idan kwata-kwata basa sallar babu shakka kafiraine, idan kuma sunayinta amma jefi-jefi wasu malaman sukace ba su kafirtaba, amma idan rashin yin sallar shi ne yafi yawa arayuwarsu nanma sunkafirta.

    Sannan matsayin aurensu yana nan ingantacce 'ya'yansu zasuci gadonsu duk wasu hukunce hukuncen musulunci zai gudana akansu da auren nasu.

    Idan su duka suka zama basa sallah wajibine ga makusantansu su yi musu nasiha da wa'azi dansu tuba sudawo suna sallah, idan ɗaya ya amsa ɗaya yaki amsawa wajibine araba aurensu, idan kuma mijine baya sallar abin da yafi gamatarsa taje tanemi wani mijin ta aura.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.