𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalmu Alaikum, don malam a amsamin wannan tanbayar Matsalata ita ce idan na kwanta da mijina bana gamsuwa, meye mafita?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumussalam.
To yar uwa akwai banbanci tsakanin inzali na mace Dana namiji domin yanzu
matsalar da wasu mata ke ciki shi ne basajin lokacinda suke inzali kamar yanda
namiji ke sani kuma bisa binciken masana Abu ukune kan gaba wajen faruwan
wannan matsalar.
1. akwai
infection (ciwon sanyi) Wanda yake hana mace sanin lokacinda take inzali domin
maniyinta zai tsinke ya zama kamar ruwa zai rinka fitowa kaɗan kaɗan wata tana jin daɗi lokacin fitarsa wata kuma
kwata kwata babu abin da takeji na daɗi
amma mijinta zai iya jin daɗin
shima kafin ciwon yayi yawa saboda irin masu wannan matsalar koda maganin
ni'ima sukayi babu wani canji to a hankali saishima mijin yadena jin daɗinta kuma sauda dama abin
da ke kawo wannan matsalar shi ne wasa da farji lokacin mace tana budurwa ko
kuma saka abin da bashida Inganci to abin da za kiyi shi ne kirinka tsarkida
ruwan dumi da magarya aciki kuma kisamu garin hulba da gishiri kaɗan ki zuba a ruwan dumi
kina zama shima lalle za ki iya dafa ganyen danyensa dandano ba Zuma kinasha
sannan me irin wannan matsalar zata iya amfani da miski na matsi wato miskul
dahara tana matsi dashi.
2. Na biyu
akwai rashin gamsuwa da miji shima yana hana mace inzali domin wasu matan ana
dadewa kafin suyi zuwan kai to idan ya zama mijin bashida juriyar dadewa mace
sai taji kamar zaizo amma ba dama ko kuma kankantar gaban namjji baya shiga
gaban mace yanda ya kamata to babu damar tayi inzali to wannan matsalar daga
wajen mijinne suna iya wasanni sosai har saita kusa yin inzalin kafin afara
saduwa.
3. akwai
rashin sha'awa mace Wanda batajin sha'awar namiji komai dadewa ana saduwa da
ita bazatayi inzaliba irin wannan gaskiya ta dage dashan magungunan kara sha'awa
tare da ni'ima.
Allah ta'ala
yasa mudace.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.