Cite this article as: Abdullahi, M. & Abdulƙadir, Z. (2023). Nazari A Kan Wasan Kwaikwayo Duniya Makaranta Na Gidan Rediyon Jihar Zamfara. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 205-209. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.024.
Daga
Musa Abdullahi
Department of Languages
and Culture,
Federal University, Gusau, Zamfara, Nigeria
08037765415
musaabdullahi@fugusau.edu.ng
DA
Zainab Abdulƙadir
Department of Languages
and Culture,
Federal University, Gusau, Zamfara, Nigeria
08032901257
Tsakure
Wannan bincike ya yi nazari ne a kan wasan kwaikwayon “Duniya
Makaranta” na gidan rediyon Jihar
Zamfara. Kamar yadda masu iya magana ke cewa “Duniya makaranta” ta fara ne tun
daga ranar da mutum ya faɗo duniya har zuwa komawarsa ga ubangijinsa, tana ɗauke da dukkan gwagwarmayar da ɗan’Adam kan yi a rayuwarsa ta yau-da-kullum na farin ciki
ko baƙin ciki, yakan zamo darasi ga ɗan’Adam don taimaka ma kanshi gobe. Wannan bincike ya yi nazari ne a kan
wasu sigogin wasan da muhimmancinta, matsaloli da kuma hanyoyin warware matsala.
Fitilun Kalmomi: Wasan Kwaikwayo, Gidan
Rediyo, Duniya Makaranta
1.0 Gabatarwa
Wasan kwaikwayo na Hausa, fage ne da ya taɓo dukkan harkokin da suka shafi rayuwar ɗan’Adam ta yau da kullum, domin yana bayyana wa mai kallo
ko mai sauraro ko karatu, hanyoyin rayuwar jama’a ta fuskar sana’o’insu. Masana
adabin Hausa da suka yi nazari akan wasan kwaikwayo sun yi ƙoƙari sun fito da ma’anar wasan
kwaikwayo.
Ɗangambo (1984) ya ce
“Wasa ne da ake ginashi don kwaikwayon wani labari ko wata matsala ta rayuwar
da ake son nusarwa ga jama’a cikin sifar yaƙini ko kuma a rubutashi”. Yahaya,
(1978) ya bayyana wasan kwaikwayo da cewa; “Wasan kwaikwayon na nuni ne da
aikata wani abu musamman a dandali domin yasa nishaɗi ga masu kallo ko ya raunanar masu da zuciya”.
Rediyo na ɗaya daga cikin hanyoyin sadarwa na
zamani da ake amfani dasu domin faɗakarwa da ilmantarwa ga jama’a akan wasu manufofi na gwamnati ko wata
sabuwar halayar rayuwar al’umma da ta shigo kuma take wanzuwa a cikin ƙasa. Ta hanyar rediyo
ake shirya wasanin kwaikwayo daban-daban domin wayar da kan jama’a, a ciki kuwa
har da wasan “Duniya Makaranta” da ake gudanarwa a gidan rediyon Jihar Zamfara.
Umar, (2012), ya rawaito faɗar Welmeit (2006: 1196) da yake cewa: “Rediyo kaface ta isar da saƙonni ga jama’a waɗanda ke zaune wurare daban-daban ba tare da ganin mai ba
da saƙon kai tsaye ba”. Oxford Dictionary (1995), ya bayyana “ma’anar rediyo da
shiraruwa ne na yaɗa labarai, zuwa ga masu sauraro waɗanda suka haɗa da jawo ra’ayin jama’a da kuma
wasanin gida da waje”.
Wasan kwaikwayo shi ne wasan da ake shiryashi domin kwaikwayon halayen
mutane ko dabbobi ko aljannu da nufin anunama jama’a su ilmantu ko su wa’azantu
ko su gargaɗu ko kuma su samu nishaɗi. Abin nufi shi ne duk wasan da aka yi koyi da halayen
kuma aka nunama jama’a to shi ne wasan kwaikwayo.
Chinwieze (1976) ya ce; “Wasan kwaikwayo wani ɓangaren adabi ne da ke samar da aikin shaƙatawa ta yin sojan gona
kamar kamanci a aikace ko a magance ko a rubuce kuma a wasance”.
Duniya Makaranta
Idan aka kalli waɗannan kalmomi guda biyu, wato “Duniya” da “Makaranta” za a ga cewa suna ƙunshe da ma’anoni
daban-daban kamar haka; Kamar yadda bincike ya nuna cewa; kalmar Duniya tana
nufin faɗin ta baki ɗaya, wanda ya ƙunshi doron ƙasa da sararin samaniya da kuma dukkan halittun da ke
ciki, waɗanda Allah a cikin ikonsa ya
halitta. Makaranta kuma tana nufin wuri ne da ake koyo da koyarwa, wuri ne na ɗaukar ilimin fannona daban-daban domin ƙaruwa ga ɗan’Adam.
1.1 Muhallin Bincike
Magaji (2004), Muhalli shi ne wurin da mutum ya kan tanada domin fakewa da
kuma samun kariya daga abubuwan da za su iya cutar da shi.
Gidan Rediyon Jihar Zamfara shi ne muhallin binciken mu, yana nan kusa ga
sabuwar kasuwa da ke Gusau daga yamma, yana da ofisoshi na bene wanda ake
gudanar da ayyuka daban-daban na jama’a.
1.2 Dabarun Bincike
Wannan bincike ya kammala ne ta hanyar hira da masu gudanar da wasan domin
jin ta bakinsu game da yadda suke gabatar da wasan, sannan kuma an yi amfani da
kallo ko lura. Haka kuma an nazarci littattafai irin littattafan wasan
kwaikwayo daban-daban domin zasu taimaka, haka kuma da amfani da kundayen
digiri waɗanda za su yi mana jagoranci game da
bincikenmu.
1.3 Kafurwar Gidan Rediyon Jihar Zamfara
Gidan Rediyon Jihar Zamfara, asalinsa daga Rima Rediyo ne na Jihar
Sakkwato. An ƙirƙiro Jihar Zamfara a shekarar (1996) sai aka samar da gidan rediyo a Jihar
Zamfara. A inda aka naɗa mata manajan farko Injiniya Mamman Maru, wanda ya mayar da tashar zuwa
babban zango da ake kira (am), sai Alh. Garba Tunau Mafara a (2004), Gidan
Rediyon Jihar Zamfara ya fara shirye-shirye a matsayin tasha mai ƙaramin zango (FM) a
(1996) a shekarar (1997) ya soma aiki daga ƙarfe 5:15 na safiya zuwa 11:00 na
dare.
Gidan Rediyon Jihar Zamfara ya fara watsa shirye-shiryensa a zamanin gwamnatin
Kanar Jibril Bala Yakubu, gwamnatin farko ta soja a Jihar Zamfara. Haka kuma
wannan gidan rediyon na da na’urori masu gajeren zango na 567khz.
1.4 Yadda ake Gudanar da Wasan Duniya Makaranta a Taƙaice
Akwai matakai da dama da ake bi wajen gudanar da wasan, waɗannan matakai ga su kamar haka:
a.
A kan me za a yi wasan?
Kafin su fara wasan ‘yan wasan su kan zauna ne su tattauna akan me za a
gabatar da wasan, idan akan siyasa ne ko lafiya ko tattalin arziki ko
zamantakewa ta harkokin yau da kullum, sai aƙirƙira ma wasan suna ta hanyar
tattaunawa.
b.
Jigon Wasa
Bayan an fito da jigon wasan ne da sunan da za a sakama wasan ne to, sai a
fito da jigon wasan watau saƙon da wasan ke isarwa. Daga nan sai mutane da zasu
gudanar da wasan. Daga ƙarshe kafin a gudanar da wasan ana buƙatar a yi bitar wasar kafin a gabatar da wasan.
1.5.1 Wasu daga cikin Jigogin Wasan
Ga wasu daga jigogin wasan kamar haka:
1.
Wasan zafin Nema: Wannan
wasa na nuni ne ga illar jahilci ga rayuwar mutum, da kuma nuni akan illar
watsi da sana’a.
A wannan wasa an nuna Mirsisi ya yi jahilci a inda yake ɗaukar cewa keƙƙega ya samu kuɗi don haka shi ma ta kowacehanya sai ya yi kuɗi saboda jahilci, sannan kuma an yi
faɗakarwa game da sana’a a inda ake
nuna cewa Mirsisi ya yi watsi da sana’arsa saboda raina sana’arsa da ya yi don
yana ganin cewa ba ta kawo kuɗi da wuri.
A taƙaice wannan wasa ta zafin nema tana faɗakarwa ne akan cewa kada mutum ya ce shi sai ya yi kuɗi sannan kuma kada mutum ya yi watsi da sana’arsa ko kuma
ka da ya raina sana’arsa.
2.
Wasan Gyara Kayanka –
Wannan wasa ta gyara kayanka ta nuna irin yadda direbobi ke tuƙi kan hanya ba bisa ƙa’ida ba, da yadda hakan
ke haifar da matsaloli a cikin al’umma har ma da rashe-rashen rayukka. Sannan
kuma an nuna yadda ‘yan (Road Safety) masu kula da hanya ke yi wa al’umma matuƙa mota cin zarafi, domin
kuma mutanen da ke bin doka yawanci su suke tarewa akan hanya.
A wannan wasa dai an fito da laifin kowanne daga cikinsu wanda kuma daga ƙarshe kowa ya gyara
halinsa.
3.
Wasan ƙarya Fure Take: A wannan
wasa ta ƙarya fure take, an yi nuni da illar rashin gaskiya da kuma muhimmancin
amana. A nan an nuna yadda mirsisi da albasa suka tsaya akan sai sun haɗa tantabara da wanda ba ta so, kuma ba tare da shawarar mai riƙon tantabara ba, wato Ƙeƙƙega mijin Albasa.
Shi kuma Ƙeƙƙega mijin Albasa ya tsaya tsayin daka ya nuna shi abin da Tantabara take so
ko kuma wanda take so shi zai aura mata, ya nuna cewa shi ba ya mata auren
dole, saboda Tantabara amana ce gare shi. A inda daga ƙarshe Mirsisi da Albasa dai suka yi
kunya.
4.
Wasan Sallah Mai Yawan
Baya: Wannan wasa anyi ta ne bayan shagulgulan sallah da ake yi, inda ake nuni
da yadda jama’a ke ƙoƙari wajen ganin cewa sun yi hidindimu kanta. Hakan yana saka wani ko ba ya
da shi ya ce lallai sai ya yi ya kai ga shiga cin bashi, hakan ne ya sa aka
saka ma wasar suna Sallah mai yawan baya.
1.5.2 Mutanen da suka fara wasan Duniya Makaranta:
1.
Abdullahi Birnin Magaji
2.
Adamu Abdullahi Kanoma
3.
Adamu Abdullahi
4.
Alhaji Shu’aibu Dangulbi
5.
Garba Galadima
6.
Hajiya Halima Bakwai
Gulubba
7.
Isah Galadima Nahuche
8.
Isah Na Banga-Banga
9.
Jamila Abdullahi Liba
10.
Margayiya Hajiya Miyatti
11.
Sadiya Dauda
12.
Sani Bello
13.
Suwaiba Dauda
14.
Shehu Muhammad ‘Yar ƙofa
15.
Shehu Mai Baƙin-mai
16.
Umaru Mai Doki
1.5.3 Tasirin Wasan Ga Al’umma:
Idan aka ce muhimmanci ana nufin amfani, kuma mun san cewa kusan duk wani
abu dole ne a ce yana da muhimmanci, musamman ma irin wannan wanda yake amfani
da tarin al’ummar da suke sauraron wannan wasan na duniya makaranta.
Don haka, wasan kwaikwayon duniya makaranta yana da muhimmanci matuƙa musamman ga al’ummar
jihar Zamfara domin suna amfani da hanyoyi da dama wajen isar da saƙonni ga al’ummar kamar
haka:
i.
Duniya Makaranta yana da
muhimmanci hanya ce mai faɗa da alfasha da kuma almubazzaranci
ii.
Hanya ce ta inganta
dangantaka da ƙarfafa zumunci tsakanin yan wasa da jama’a.
iii.
Hanya ce ta wayar da kan
al’umma wajen sanar da al’umma abubuwa da suka shige masu cikin duhu.
iv.
Hanya ce ta neman abin
rayuwa watau samun aikin yi wanda za a dogara da kai.
v.
Hanya ce ta ƙara haɓaka harshe da ƙara kalmomi da fito da dabarun sarrafa harshe kamar karin magana, shaguɓe, habaici.
1.5.4 Tasirin
Wasan Ga ‘Yan Wasan
1.
Shirin Duniya Makaranta
ya taimaka sosai wajen ƙarfafa zumunci tsakanin ‘yan wasa da jama’a
2.
Hanyace ta samar da abin
yi da dogara da kai, watau aikin yi ga marasa aikin yi.
3.
Hanya ce ta ƙara haɓɓaka harshe da ƙara kalmomi
4.
Hanya ce ta hikimar
shirya taɗi da hira da amfanar da mai harshe
5.
Hanya ce ta samar da kuɗaɗen shiga ga ma’aikatar rediyo ita kanta
6.
Hanya ce da za ta
taimaka wa ɗalibai ƙwarai musamman masu nazarin Harshe a
Jami’o’i da kwalejoji.
1.5.5 Matsaloli da Wasan ke Fuskanta
Kusan dukkan wani aiki da ake yi akan fuskanci kalubale gareshi, haka yake
a fannin wasan “Duniya Makaranta”.
i.
Rashin dawowar ɗan wasa
ii.
Matsalar rashin kayan
aiki
iii.
Matsalar rashin kuɗi
iv.
MatsalarwutarLantarki
1.5.6 Hanyoyin Warware Matsala
Haƙuri kan kuɗi, watau sun yi ƙoƙar wajen sadaukar da karfinsu wajen
gudanar da wasan. Saboda ‘yan wasan su na yin ƙoƙari wajen yi ba don a basu kuɗi ba, sannan ko da sunyi zasu saka kuɗin su ne wajen ganin cewa komai ya yi yanda ake so.Sun bayyana cewa wani
lokaci idan buƙatar kuɗi ya taso sai dai wani ya yi cikin
aljihunsa domin ganin an gabatar da wasan.
1.5.7 Ra’ayoyin Masu Sauraren Wasan
i. Sani Muhammad
ii. Abubakar Maitakara
iii. Sa’adu Umar Bukkuyum
Sani Muhammad; ya ce wannan wasa yana faɗakarwa, ilmantarwa da kuma nishaɗantarwa ga al’umma musamman ta ɓangaren gwamnati suna kariya gareta domin wani lokaci
gwamnati ba ta aiwatar da wani abu ba, amma sai su faɗakar a kan abin domin gwamnati ta gyara.
Malam Abubakar Maitakara cewa ya yi, “ni dai ina sauraron wannan wasan matuƙa in har ina zaune, don
kusan duk lokuttan da ake wannan wasan na sani, a gaskiya yana karantarwa ga
jama’a da kuma faɗakarwa ga ita kanta gwamnatin
Zamfara. Ina ƙara ba masu aiwatar da wasan goyon baya domin ƙara inganta wasan ga masu sauraro ya
yi daidai kamar yadda ya kamata.
Mal. Sa’adu Umar Bukkuyum; ya ce “Ni ke gabatar da wasan, wannan wasan yana
ƙayatarwa da kuma nishaɗantarwa ga al’ummar Jihar Zamfara, har ma da maƙwabtanta, a ko yaushe mutane suna
jin daɗin wannan wasan sosai, wasu daga
cikinsu suna ba da shawarwari na cewa ya kamata a ƙara inganta wannan wasan.
1.8 Sakamakon Bincike
Wannan bincike ya gano cewa shirin duniya makaranta ya fi tasiri akan
mutanen karkara da kuma matan aure da gwamnatin jahar Zamfara.
Kasancewar galibin shirin ya fi mai da
hankali ne ga sana’oi
da ayyuka na mutanen karkara,
kamar noma da
kiyo da dai sauransu.
Wannan ya sa mutanen karkara su ka
fi maida hankali sosai wajen sauraron wannan shirin na duniya makaranta
a duk ranakkun
da ake yin shirin.
Mafi yawancin mutanen karkara galibi aikinsu noma kuma aikin noma aiki
ne na lokaci
da zaran sun gama aikin sai yazamana basu
da wani aiki
da ya fi shi, sai dai zaman gida kawai su ke yi.
Wannan zaman
da suke yi yana
basu dama ta sauraron rediyo
ta yadda zakatarar mutanen har jiran lokacin shirin su ke yi.
Wannan ne yasa a
lokacin da a ke gudanar
da was an masu yawan bugowa mutanen karkara
ne, shi yasa masu
yin shirin na duniya makaranta suka
fi yin shi akan al’amurran
da suka danganci mutanen karkara.
Ta fuskar matan aure kuwa,
shirin yana
da tasiri ƙwarai da gaske, domin kasancewarsu masu zaman gida,
don haka zaman gidan
da suke yi ya na basu dama
ta sauraren rediyo
da kuma bin kadin shirin na kowane lokaci,
ta hanyar sauraron wannan shirin zaka taras da mace
ta daina abin
da take yi wanda ba na dai-daiba,
ya na faɗakar
da su, kuma ya na nishaɗantar
da su, haka kuma ya na wa’azantar
da su.
Shirin duniya makaranta yana faɗakarwa
da nishaɗantarwa
da wa’azantarwa da ma hanyar samun kuɗi ga masu
yin wasan. Shirin yana faɗakarwa sosai
ta fuskar gabatar
da shirin kan wani
sabon al’amari da ya shigo duk suna amfani da wannan dammar sai su yi shiri
a kan shi.
Shirin kuma yataimaka ta hanyar samar da aikin yi gamarasa aikin yi.
Bugu da ƙari wasan duniya makaranta yana wayarwa al’umma kai game da manufofin gwamnati kan demokaradiya, haka kuma yana ba da dama ga ‘yansiyasa su ziyarcesu domin su yi tsokaci game da al’ummuran siyasa ta wannan zamani.
1.7 Kammalawa
Wannan bincike ya yi nazari ne akan wasan kwaikwayo “Duniya Makaranta” na
gidan rediyon Jihar Zamfara” da ma’anar wasan kwaikwayo, Rediyo da kuma ma’anar
Duniya Makaranta, a wannan muƙala munyi bayanai akan kafuwar gidan rediyon Jihar
Zamfara, yadda aka gudanar da wasan a taƙaice. Haka kuma ta kawo wasu jigogin wasan mutanen da
suka fara gabatar da wasan. Wannan muƙala ta kawo muhimmancin wasan ga al’umma, matsaloli da
kuma hanyoyin da ake bi wajen gudanar da wasan da ra’ayoyin wasu masu sauraro.
Manazarta
1. Bello, (1992): “Wasan
Kwaikwayo na Hausa” Zaria Published by Northern Nigeria Publishing Company
Ltd..
2. Bunza,
A.M (2004) Waƙaƙƙen ƙa’idojin
Rubutun Hausa Lagos Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.
3.
Ɗangambo, H. (1984) “Wasanni Don yara” Kano Centre of
Research and Publishing Company.
4.
Yahaya da Wasu, (1992):
“Darussan Hausa Littafi na uku. Ibadan University Press Plc.
5. Yar Aduwa T.M (2007):
Wasan Kwaikwayo na Hausa; Kano Nauoinsa da sigoginsa. Usman Al-Amin Publishing
Company;– Nigeria.
6. Zagga N.M (1988); Salo
da Jigo da Tsarin Al’adun Hausawa a Wasan Idon Matambayi “Kundin digiri na
Farko, Sashen Nazarin Harsunan Nigeria, Jami’a Usman Ɗanfodiyo Sakkwato.
7.
Zaria, M. (1989)
Gudummawar Kafofin Watsa Labarai wajen bunƙasa Harshen Hausa” Muƙalar da aka gabatar a
taron ƙarawa juna sani a Jami’ar Bayero ta Kano.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.