Ticker

Shin Ya Halasta In Yi Kitso Da Wiwi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaika malam don Allah ya halasta in yi Kitso da wiwi? Ma'ana in sa shi a cikin man kitso.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu. Ya tabbata a hadisi cewa Manzon Allah ya ce: Duk abu mai sa maye giya ce, duk abu mai sa maye haramun ne. Kamar yadda Albukhariy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta (2003).

Wiwi kuma yana daga cikin abubuwan da ake hukunta su a matsayin kayan maye, don haka ita ma giya ce, hukuncinsu ɗaya dai-dai-wa-daida. Sannan Allah Ta'ala a cikin Alƙur'ani ya bayyana giya a matsayin najasa ce a aya ta (90) da ke suratul Ma'ida.

Malamai sun yi saɓani a game da najasar da ake nufi a wannan aya, wasu malaman suna ganin siffanta giya da Allah ya yi da najasar da ke wannan aya tana nufin najasa ce ta ma'ana ba ta haƙiƙa ba, don haka suke ganin ko da giya ta taɓa jikin mutum ba dole ne sai ya wanke ba, saboda su a fahimtarsu ba najasa ce da idan ta taɓa jikin mutum sai ya wanke ba.

jumhur ɗin malamai kuma suna da fahimtar duk wanda giya ta taɓa jikinsa dole ne sai ya wanke hannunsa domin najasa ce ta taɓa jikinsa, saboda a fahimtarsu ita giya najasa ce ta haƙiƙa ba ta ma'ana ba. Kuma wannan fahimtar ita ce ke da rinjaye.

A bisa wannan dalili, sai ya zama bai halasta a sanya wiwi a kai a yi kitso da shi ba, saboda wiwi giya ce, giya kuma najasa ce, kuma ba ya halasta a shafa najasa da gangan a jiki.

Don ƙarin bayani a duba Fataawá Nurun Alad Darb (7/2), na Ibn Uthaimeen.

Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments