Siffofin Da Suka Dace Mai Wa'azi Ya Siffantu Da Su!

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Allah ya taimaki malam. Dan Allah a yi min bayani a kan dabi'un da mai wa'azi zai siffantu da su?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salámu. 'yar uwa wa'azi aiki ne na kira zuwa ga Allah, kuma aiki ne na Annabawan Allah, kuma aiki ne na magada Annabawan Allah, sai hakan ya zama wajibi a kan mai wa'azi ya siffanta da kyawawan ɗabi'u da halaye da suka haɗa da:

    1. Ikhlasi: wato tsarkake ninya a cikin al'amuran mai wa'azi.

    2. Yin haƙuri a bisa cutarwar da zai gamu da su a harkar wa'azantarwa.

    3. Dole mai wa'azi ya zama yana da ingantaccen ilimi yalwatacce.

    4. Ya zamto mutum ne mai ƙanƙan da kai ba mai girman kai da ƙyamar mutane ba.

    5. Ya zamo mai kira zuwa ga Allah da Sunnar Manzon Allah ba tare da sa wata manufa ta ƙashin kai ba.

    6. Siffantuwa da gaskiya da riƙon amana a cikin al'amuran mai wa'az.

    7. Yin wa'azi ba tare da nuna ƙabilanci ba.

    8. Tausasa harahe wurin kira zuwa ga Allah, wato kada mai wa'azi ya siffantu da kalmomi masu tayar da zaune tsaye, har ta kai ga mutane su ƙi saurarensa.

    9. Dole mai wa'azi ya zamto mai tausayi da yin addu'a ga waɗanda yake kira zuwa ga Allah.

    10. Ya zamto ba mai saurin ɗaukar ramuwar gayya a abin da ya shafi ƙashinsa ba, sai idan an taɓa addinin Allah.

    Waɗannan ba su ke nan ba, idan aka tuntuɓi malamai za a sami ƙarin bayani, Allah ya sa mu dace.

    Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.