Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarbiya a Falsafar Al’ada

Cite this article as: Dangulbi, A.R. (2023). Tarbiya a Falsafar Al’ada. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, (2)2, 214-218. www.doi.org/10.36349/tjllc.2023.v02i02.026.

Tarbiya a Falsafar Al’ada

Aliyu Rabi’u Dangulbi
Department of Languages and Cultures,
Federal Uni
versity Gusau, Zamfara, Nigeria

Tsakure

Al’ummar Hausawa sun daɗe suna gudanar da harkokin rayuwarsu kamar yadda al’adarsu ta tanada. Kowace al’umma haka ake sa ran takasance tana alfahari da al’adunta. Tarbiya tana daga cikin daɗaɗɗiyar al’adar Hausawa wadda ta yi tasirin gaske a zukatansu. Bahaushe mutum ne mai zurfin tunani, wanda yake tsayawa ya ƙirƙiro wa kansa abin da zai amfane shi a tsawon rayuwarsa a duniya. Don haka sai ya samar wa kansa hanyoyin tarbiyantar da ‘ya’yansa a al’adance kafi zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Hanyoyinsun haɗa da tatsuniyoyi da labaran hikima da hikayoyi da camfe-camfe da sauransu. Wannan hikima ta taimaka wajen hana yara aikata wani abu da ya saɓa wa al’adar mutanen da ake Magana a kansu. Ta yi ƙoƙarin kawar da miyagun al’adu waɗanda suka saɓa wa koyarwar al’adun Hausawa. Ta kyautata zamantakewa da biyayya ga iyaye da shugabanni da barin wasu miyagun ɗabi’u da al’ada ta kyamata, kafi zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Haka kuma addinin musulunci ya taka rawa wajen gyara halaye da ɗabi’u na rashin tarbiya da al’adar Hausawa ta yi hani da aikatasu. Kamar rashin biyayya ga iyaye da rashin girmama manya da shugabanni da sata da zina da sauran halaye marasa kyau. Dalilin haka ya sa wannan takarda za ta yi tsokaci a kan tasirin da addinin musulunci ya yi wajen kyautata kyawawan ɗabi’u da halaye na gari da al’adar Hausawa ta horas kuma aka tarbiyantu da su. Haka kuma mu dubi yadda baƙin al’adu suka gurɓata tarbiyar ‘ya’yan Hausawa musamman a kan shaye-shayen muyagun ƙwayoyi da sauran abubuwa na rashin ɗa’a.

Fitilun Kalmomi: Al’ada, Tarbiyya, Zamantakewa

Gabatarwa

A al’adance, Hausawa suna amfani da matakan tarbiyantar da ‘ya’yansu domin a sami ingantacciyar al’umma da za a riƙa alfahari da ita. Hakiƙa, idan muka dubi wannan bayani da ya gabata muka kuma waiwayi irin zaman da Hausawa suka yi kafin shigowar addinin musulunci da wannan zamani, watau lokacin da suka yi cikakken riƙo da kyakkyawar tarbiyarsu wadda take koyar da yin biyayya ga dokokin al’ada da suka shafi girmama iyaye da shuganni da bin gaskiya da riƙon amana. Haka kuma da sadar da zumunci da taimakon juna, da riƙon sana’o’i da juriya da jarunta, da nuna kunya da kara, da kyakkyawar mu’amala a tsakaninsu. Sannan, idan aka kwatanta tarbiyar da, da halin da ‘ya’yan Hausawa suke ciki a yau, sai a ga cewa, koyarwar da Hausawa suka yi wa ‘ya’yansu ta hanyar amfani da ƙirƙirarrun labarai masu koyar da halaye na gari da camfe-camfe ta taɓarɓare. Misali a yau an wayi gari ƙarami ba ya yi wa nagaba da shi biyayya. Idan wata yar matsala ko rashin jittuwa ta faru a tsakaninsu, ƙaramin ba ya jin kunyar cin mutuncin wanda ya girme shi ko da kuwa ya kai tsarar mahaifinsa. Wannan rashin ɗa’a ya saɓa wa koyarwar tarbiyar al’adar Hausaa ta da.

A halin da ake ciki a yau, iyaye sun koma ‘ya’ya, don kuwa ‘ya’yan suna juya su yadda suke so. Zaman banza da yaudara da cuta da yin bangar siyasa ga ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa sun zama abubuwan yi a wannan zamani. Haka kuma rashin gaskiya da cin amana sun zamo ruwan dare, kuma ba abin kunya ba ne ga ‘ya’yan Hausawa. Faɗawa cikin irin wannan hali ga dukkan al’ummar da ta san ciwon kanta, abubuwa ne da suke buƙatar dubawa domin samun mafita. Idan har ana son mafita, to dole ne a koma ga koyarwar tarbiyar Hausawa kamar yadda al’adarsu ta yarda da kuma koyarwa ta addinin musulunci wadda ta yi tasirin gaske cikin al’ada da ita kanta tarbiyar Hausawa. Wannan takarda za ta yi tsokaci ne a kan wasu daga cikin hanyoyin tarbiyar Hausawa na gargajiya waɗanda ke da alaƙa da addinin musulunci da suka haɗa da kiyaye dokokin addini (Abbati M Mailittafan musulunci) da girmama nagaba, da dogaro da kai da kuma gaskiya da riƙon amana, da sadar da zumunta da kuma kyautata yanayin suturar da muke sawa a jikinmu.

 

Tarbiya A Falsafar Al’ada

Tun kafin zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa, Hausawa suke gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya. wanda ya haifar da kyakkyawan tsaro a cikin al’umma. Idan aka ce falsafa, ana nufin zurfafa tunani a ƙirƙiro wani abu da babu shi, amma mai amfani domin a samar wa kai wata matsaya ko hanyar da za a bi a kawar da wata matsa. Bahaushe ya zurfafa tunaninsa wajen ƙirƙiro wa kansa hanyoyin tarbiyantar da ‘ya’yansa ta hanyar zaman ba da ƙirƙirarren labari, da tatsuniya, da kuma camfi; domin ya kange ‘ya’yansa daga yawace- yawacen banza da zuwa wuraren da ba su dace ba. Wannan tunane da Bahaushe ya yi na ƙirƙira hanyoyin kange ‘ya’yansa daga faɗawa cikin miyagun ɗabi’u da al’ada bat a yarda das u ba it ace falasar da ta haifar da tarbiyar ‘ya’yansa. Wato, al’adar Hausawa tana da dangantaka da tunanensu na ƙirƙiro hanyoyin horas da ‘ya’yansu ta hanyar gargajiya. Wannan ita ce falsafar da wannan takarda take ƙoƙarin fitowa da ita a al’adance.

Mece ce tarbiya

Tarbiya na nufin, hali na gari (CSLN, 2006: 428), wanda ya ƙunshi nagarta, wadda ta haɗa da haƙuri, da biyayya da gaskiya da riƙon amana, da sauƙin kai, da kirki, da kunya da kawaici, da sanin ya kamata da girmama nagaba.

Bakura (2013: 218) ya bayyana tarbiya da cewa, koyar da halina gari da kyautata rayuwar al’umma da shiryar da su zuwa ga halaye da ɗabi’u masu kyau da nagarta. Ya ƙara da cewa duk al’ummar da ta kasance haka, za ta zama mai kima da kwarjini da ganin mutuncin abokan hulɗa, da kuma bai wa kowa haƙƙinsa kamar yadda ya kamata. Yahaya da wasu (1992) da Tanko (1993) da Sa’id (2001) dukkansu sun yi ittifaƙi cewa, Tarbiya ta ƙunshi, renon jikin ɗan’Adam da ruhinsa da kyawawan abubuwa masu kamala da kowace al’umma za ta iya yin alfahari da su. Ɗangulbi (2013: 316) ya bayyana cewa, tarbiya ta ƙunshi ɗabi’u na gari, da kyawawan halaye da suka haɗa da biyayya ga iyaye, da girmama manya da kyautata wa dangi da sadar da zumunta da gaskiya da riƙon amana.

A taƙaice tarbiya ita ce koyar da ɗabi’u na gari da kyawawan halaye kamar yadda al’ada ta tanada. Duk al’ummar da ke son zaman lafiya da kwanciyar hankali ta kauce wa faɗawa cikin matsalar rashin tsaro, dole ne ta tarbiyantar da ‘ya’yanta su sami ci gaba mai ɗorewa ta hanyar biyar wasu matakai masu inganci da suka haɗa da kiyaye dokikin da al’ada da addini suka gindaya domin ta zama ta gari, abin koyi ga maƙwabta na kusa da na nesa. A al’adance Hausawa mutane ne masu ɗa’a da bin doka tun kafin zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Da addinin musulunci ya zo sai ya ƙara tabbatar da kyawawan halaye da ɗabi’u na gari da al’adar Hausawa ta yarda da ita. Sannan ya yi hani ga wasu ɗabi’u da halaye marasa kyau. Wannan ya nuna tarbiya wata aba ce, da al’ada da addini suka yarda da ita.

Kiyaye dokokin addini

Addinin gargajiya shi ne addinin da Maguzawa suka dogara gare shi, sannan Hausawa suka yarda da shi kafin zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Addinin gargajiya shi ne bauta wa wani abu wanda ba mahalicci ba, domin neman biyan buƙatarsu. Wannan hanyar bauta ta samo asali daga mutanen da suka fara zama a duniya. Wato su suka ƙirƙiro hanyar da za su riƙa bauta wa wani abu; domin samar kansu abin bautar da za ya jibinci al’amurran rayuwarsu. Mutum ya yarda akwai wanda ya halicce shi, amma yana da wuya ya sadu das hi kai tsaye. Dalilin haka ya say a zurfafa tunanensa don ya samar wa kansa hanyar bauta cikin sauƙi. Daga nan sai ta zama al’adar sauran ƙabilun da suke biye da su har ya zo ga al’ummar Hausawa.

Zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa ya kawo wa wannan hanyar bauta cikas, saboda Hausawa sun karɓi addinin musulunci suka watsar da bautar gumaka da bori da camfe-camfen gargajiya. Amma duk da haka wasu ba su watsar da wasu abubuwa da suka danganci addinin gargajiya ba, (Bunza 2009). Al’ummar Hausawa kafin shigowar addinin musulunci, da ma bayan zuwansa, mutane ne masu matuƙar biyayya ga dokokin addinin da suke bauta wa. Sallau (2001: 362), ya bayyana cewa, al’ummar Hausawa a lokacin da suke bautar addinin gargajiya suna matuƙar yin biyayya ga abubuwan da suke bauta wa. Suna tsoron saɓa masu don gudun kada su yi fushi da su, su saukar masu da wani bala’i. Har wa yau suna kyautata masu don neman yardarsu, yadda za su biya masu bukatunsu. Su kuma, su sanar da su abubuwan da ke tafe a shekara mai zuwa; idan na sharri ne, su taimaka masu yadda za su maganinsu. Wannan ya nuna mana cewa, ita tarbiya ta gari, tana kawo wa mai yin ta wani alheri da bai taɓa zaton samu ba a rayuwarsa. Misali, idan yaro ya zama mai ladabi da biyayya ga manya, sai ka ga har aure ake ba shi ba tare da wani dogon bincike ba. Haka kuma rashin tarbiya ta ƙwarai tana zama sanadiyar barin gari a koma wani, ko wata ƙasa inda ba wanda ya san shi. Misali, idan ya aikata wani abu da ya saɓa wa tarbiyar da al’ummarsa ta yarda da ita. Misali; aikata abin kunya da ya shafi zina da sata, ko wani abu maras kyau a cikin al’ummarsa ta Hausawa.

Da addinin musulunci ya karɓu a kasar Hausa sai ya yi hani ga aikata irin waɗancan abubuwa da al’adar Hausa ta yi hani da aikata su. Saboda aikata su saɓa wa dokokin Addinin musulunci ne. A al’adar Hausawa sai budurwa ta kai shekara goma sha uku zuwa sha takwas a wasu wurare sannan a yi mata aure. Wato, an tabbatar da ta balaga kenan. A al’adance a ƙasar Hausa, an yarda idan saurayi yana neman budurwa aure ya je tsarince wurinta. Wato ya je gidansu ya kwana a ɗakinta tare da ita a kan shimfiɗa ɗaya, ko ita ta je gidan saurayinta ta kwana tare da shi. Amma al’adar Hausawa ba ta yarda ya ko taɓa jikinta ba, balle ma har ya aikata wani abu da ita ba, (Zina ko lalata). Idan ya kuskura ya taɓa ta, ko ya yi ƙoƙarin yin lalata da ita, to ya shiga uku ya lalace, domin za ta ɗora sunansa a faifai a dandalin wasarsu. Ta rera masa waƙa ta ɓatanci kowa ya jiya. Wannan cin mutunci aka yi masa zai zama sanadiyar barin garinsu, ya shiga duniya har abada saboda da saɓa wa ƙa’idar tarbiyar al’adar Hausawa.

Haka kuma ba zai ƙara samun budurwa da zai aura ba a wannan yanki na su ba. Dalilin haka ya sa wasu mutane da suka aikata irin wannan ɗabi’a ta fitsara, ( fasiƙanci ko lalata) da budurwa, suke gudu su bar ƙasarsu baki ɗaya. Sukanje inda ba wanda ya san inda suka fito, balle har a san dalilin da ya rabo su da garinsu. Wannan hukunci shi ne ya yi daidai ga namiji.

Idan aka sami budurwa ta yi lalata (zina), to tana fuskantar hukunci mai tsanani wanda ka iya zama sanadiyar mutuwarta. Hukuncin ya danganta daga abin bautar gidansu; domin kowane gida suna da irin abun da suke bautawa. Da farko za a kira ta a tambaye ta ko ta san ɗa namiji? Idan ta amsa cewa ta san ɗa namiji, shi ke nan ta jawo wa kanta da dukkan zuri’arta abin kunya, sai a rage yawan dukiyar aurenta. Idan kuma ta amsa cewa ba ta san ɗa namiji ba, daga nan sai mahaifanta su bi hanyar tsafi don a gano gaskiyar maganarta, wato zargin da ake yi mata na yin lalata. Idan aka gane ƙarya take yi tsafin gidansu zai yanke mata hukunci mai tsanani musamman ya kashe ta.

Irin wannan hukunci ya yi daidai da dokokin da addinin musulunci ya zo da su game hukuncin da ya kamata a yi wa wanda ya aikata lalata (zina). A cikin Alƙur’ani mai girma (sura ta 17: 32}, Allah mai girma da ɗaukaka yana cewa:

kuma kada ku kusanci zina, lallai ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya (17: 32) (Gummi, 1974: 419)

Wannan aya tana tarbiyantar da Ɗan’adam da kada ma ya kusanci alfasha, watau zina. Al’adar Hausawa ta kyamaci duk wani abu da zai haifar da lalata da mace. Dalilin haka aka tanadi hukunci mai tsanani ta hanyar kisa ko hukunci mai kama da wannan kamar yadda muka riga muka gani a baya. Dangane da irin wannan hukunci da al’ada ta tanada wa mai aikata zina, ya sa addinin musulunci bai kauce wa wannan al’ada ba, sai ma ya ƙara jaddada dokokin da suka haramta zina da kuma hukuncin day a dace ga aikata ta. Inda Allah (SWA) a cikin alƙur’ani, (sura ta 24 aya ta 2- 3), yake cewa:

“Mazinaciya da mazinaci, to ku yi bulala ga kowane ɗaya daga garesu, bulala ɗari, kuma kada tausayi ya kama ku game da su a cikin addinin Allah, idan kun kasance kuna yin imani da Allah da ranar lahira, kuma wani yankin jama’a daga muminai, suhalarci azabarsu (Gummi 1979: 528).

Wannan hukunci na waɗanda ba su taɓa yin aure ba ne, amma waɗanda suka yi aure, nasu hukunci shi ne a jefe su har sumutu. Bayan sharuɗɗan sun cika kamar yadda yake ga sunna, kuma wannan ga haƙƙin ‘ya’ya ne, amma ba yi hukuncinsu bulala hamsin kawai.

Da waɗannan misalai daga Alƙur’ani ya isa mu fahimci cewa tarbiya a al’adar Hausawa abu ce da musulunci ya yarda da ita kamar yadda ya bayyana a misalai da suka gabata.

Shigowar baƙin al’adu a ƙasar Hausa

Hulɗa da zamantakewa wuri ɗaya da hulɗa da addini da kuma kasuwanci su ne abubuwan da ke haifar da shigowar baƙin al’adu a cikin wasu al’adun jama’ar da suke hulɗa da su. Abubuwan da ke haifar da kyakkyawar mu’amala tsakanin al’ummomi daban-daban sun haɗa da al’adar jinƙai da taimako da kula da haƙƙin makwabtaka. Waɗannan abubuwa duka Hausawa suna kula da su kafin shigowar baƙin al’adu a ƙasar Hausa. Wato, karar sadar da zumunci da reno da riƙon ‘ya’ya ‘yan uwa duka ɗabi’u ne na Bahaushe wajen inganta tarbiyarsa da ta al’ummar Hausawa baki ɗaya.

Shigowar baƙin al’adu ya yi sanadiyar taɓarɓarewar tarbiyar ‘ya’yan Hausawa ta fuskoki da dama. Misali ta fuskar sutura, biyayya ga shugabanni, da iyaye. (Ɗangulbi, 2013;320). Haka tarbiyar kara da riƙon ‘ya’yan dangi da sadar da zumunci sun ƙaura a dalilin shugowar baƙin al’adu a ƙasar Hausa da Turawa ‘yan mulkin mallaka suka zo da su ta hanyar ilimin zamani. Idan muka ɗauki suturar Hausawa sai mu ga cewa Hausawa suna da tarbiyar yin amfani da kammalalliyar sutura wadda ke rufe masu tsiraici da jikinsu domin su rarrabe kansu da sauran ƙabilu. Yanayin suturar Bahaushe yakan so ya sanya babbar riga da jamfa da hula ko rawani. Haka kuma wani lokaci yakan sanya taguwa ko kaftani da wando da hula saboda ya bayyanar da al’adarsa kammalalliya. Amma a halin yanzu da baƙin al’adu na sanya sutura mai nuna tsiraici kamar wando (suwaga) da ɗinkin matsu da mata suke sa wad a sauransu suka mamaye ƙasar Hausa sai al’adar sanya sutura ta gari mai kare mutuncin maza da mata ta sauya. ‘Ya’yan Hausawa suka fara amfani da kayan da turawa da ‘yan kanzagensu suka zo da su domin su gurɓata tarbiyar da al’ada da addinin musulunci suka yarda da su. Yin haka ya saɓa wa tarbiyarmu ta kamala. Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi kira ga al’ummar Hausawa da su riƙi al’adunsu na gargajiya. Domin riƙo da al’adun gargajiya wata tarbiya ce ta girmama al’ada. Ɗanƙwairo yana cewa:

Jagora: Mu bi al’adunmunagargajiya

AmshiKar mu sake mu manta

Jagora: Abin ga da takaici

Sai ka ga ɗanmusulmi (Bahaushe)

Da wandonyaɗiguda

Ga ‘yas shat yasa a wuyanai

Ba hulla ga kai nai

Aljihunaibatasbaha

Amshi: Sai kwalinsigari

Jagora: Ka ga aljihunaibatasbaha

AmshiSai kwalinSigari

Jagora: Ku kau matanmu da aɗ ɗiyan musulmi (Hausawa)

Ku zan ki yin lulluɓi

Ban da sayen sikyat da ‘yak kanti

Kuna yawo rariya – rariya

AmshiAbin ga ya ba mu kunya

(Ɗanƙwairo, Mu bi Al’adunmu na Gargajiya)

Makaɗa Ɗanƙwairo yana gargaɗin Hausawa da su guji sanya sutura da ba ta kamala ba, wai don su nuna sun waye. Sanya irin suturar da Bature da ‘yan kanzagensa suka zo da ita, walaƙanci ne, da watsar da tarbiyar da al’adunmu da addinimu suka koya mana.

A halin yanzu ‘ya’yan Hausawa sun rikiɗe sun zama kamar ‘ya’yan arna ko Turawa wajen amfani da wando suwaga da matsattsun kaya da ke bayyanar da tsiraicinsu a fili. Haka su ma mata ‘ya’yan Hausawa sun zama kamar comfort ko Ɓictoria ta fuskar suturar da suke sakawa da ke bayyana siffofinsu da tsiraicinsu a fili a sanadiyar cuɗanya ko hulɗa da suke yi da baƙin al’adu. Babu ɗa’a da biyayya ga iyaye, balle su girmama shugabanni.

Sakamakon bincike

Wannan bincike ya yi ƙoƙarin gano cewa, tarbiya a falsafar al’ada, takarda ce da ta bayyana zurfaffen tunanen Bahaushe wajen ƙirƙiro hanyoyin horas da ‘ya’yansa tun kafin zuwan addinin musulunci a ƙasar Hausa. Hausawa sun taka rawa wajen riƙe dokokin da addininsu na gargajiya suka tanada, musamman hani da horo, da yin biyayya ga magabata da iyaye. Sannan sun ta’allaƙa dokokin al’ada da na musulunci, ba su yi watsi da su ba. Bugu da ƙari, takardar ta gano cewa, sakaci na iyaye da jahilci su suka taimaka wa Hausawa suka yi watsi da hanyoyinsu na gargaiya da na addinin musulunci wajen tarbiyar ‘ya’yansu. Al’adun Turawa da ‘yan kanzagensu suka yi tasiri wajen ruguza koyarwar al’ada da addinin musulunci, saboda rungumar baƙin al’adu na Turawa da Hausawa suka yi.

Kammalawa

Al’adar Hausawa ta tanadi kyawawan ɗabi’u da ladabi da biyayya da girmama magabata domin tabbatar da samun kyakkyawan zaman lafiya da al’umma ta gari, wadda za a riƙa koyi da ita. Haka ba zai samu ba, sai an sami kyakkyawar zamantakewa ta hanyar bin ƙa’idojin da al’adar Hausawa da addinin musulunci suka tanada.

 Al’adar Hausawa tana koyar da tarbiya ta gari musamman ga ‘ya’yansu domin su tashi cikin rayuwa da za su zama abin so ga kowa. Bahaushe mutum ne mai kiyaye dokoki da ƙa’idojin da al’adarsa da addininsa suka gindaya masa wajen gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum. Sai dai shigowar baƙin al’adu sun taimaka wajen rushe kyakyawan gini da Hausawa suka yi a baya na koyar da kyawawan ɗabi’u ga ‘ya’yansu. na kunya da ɗa’a da girmama magabata da sadar da zumunta, da kula da haƙƙin makwabtaka. Ya kamata hukumomi da al’ummar Hausawa da iyaye, da malaman addini su ƙara zage dantse wajen ƙoƙarin yin nasihohi da wa’azi da gargaɗi domin ceto ‘ya’yanmu daga halin da suka faɗa na koyi da halaye da ɗabi’u da suka saɓa wa tarbiyar da al’adunmu da addininmu suka koya mana. Haka kuma iyaye su sa ido ga kallace-kallacen fina-finan batsa da ‘ya’yansu suke yi waɗanda ke ƙara gurɓace masu tarbiya.

A ƙarshe iyaye su ƙara kula da abokan da ‘ya’yansu suke tafiya tare da su, domin kada su yi koyi da miyagun ɗabi’u na shaye-shaye da sace-sace da fyaɗe da sauransu.

Manazarta

1.       Abbas Y. (2013) Zulunci: Tushen taɓarɓarewar Tarbiyyar Al’ummar Hausawa, Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi na ƙasa da ƙasa, a kan taɓarɓarewar al’adun Hausawa, Jami’ar Umaru Musa Yar’aduwa Katsina, June, 2013.

2.       Bakura A. R. (2013) “MusabbabinTaɓarɓarewar Tarbiya a ƙasar Hausa, Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa a kan taɓarɓarewar Al’adun Hausawa, a jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina, June, 2013.

3.       Bunza A. M. (2006) Gadon Feɗe Al-ada, Lagos, Tiwal Nigeria Ltd.

4.       CSNL (2006) Ƙamusun Hausa, Zaria, Bayero Uniɓersity Kano.

5.       Ɗangulbi A. R. (2013) Tasirin baƙin Al’adu ga taɓarɓarewarTarbiya da zumunta a Zamantakewar Hausawa a yau. Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa a kanTaɓarɓarewar Al’adun Hausawa, Umaru Musa ‘Yar’aduwa Uniɓersity, Katsina June, 2013.

6.       Ingawa, Z. S (1988) “Tasirin Musulunci da al’adun Gargajiya na Larabawa kan al’adun Hausawa’ Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilimi na Malamai da ɗalibai, sashen Harsunan Nijeriya jami’ar Bayero, Kano.

7.       Musa Ɗanƙwairo Maradun, Waƙar Al’adun Gargajiya da “Waƙar Yaƙi da Rashin Ɗa’a (Tarbiya).

8.       Sa’id B. (2001) Tarbiyya a Musulunci: Haƙƙin ‘ya’ya a kan iyaye da haƙƙin iyaye a kan ‘ya’ya, Kano Abbas Press Nig. Ltd. 

Post a Comment

0 Comments