Tatsuniyar Hausa

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Tatsuniyar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Tatsuniyar Hausa

    Tatsuniyar Hausa 

    Wannan littafi mai suna “Tatsuniyar Hausa” an rubuta shi ne don a yi waiwaye adon tafiya a kan abin da ya shafi tarbiyyar ‘ya’yan Hausawa. Tun lokacin da Hausawa suke cikin Maguzanci har farkon shigowar addinin Musulunci a Æ™asar Hausa, tatsuniya tana cikin makarantun farko, da ‘ya’yan Hausawa ke koyon dangogin tarbiyya, kamar ladabi da biyayya, tsare gaskiya, barin yin Æ™arya a cikin zance, taimakon juna, rashin haÉ—ama da sauransu.

    Haka kuma tatsuniyoyi a wancan lokacin suna samar da nishaÉ—i na musamman ga Hausawa, ta hanyar ban dariya da waÉ—ansu al’adun da suke tare da su, kamar na É—aure gizo don gudun mutum ya yi É—emuwa (makuwa) da koyar da tsafta da sauran muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullum.   

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.