1. Ni da sunan kaliƙinmu,
Ga ya nan saƙo
garemu.
2. Yau da
mi'iyya nazo ni,
Zan batu ne kan ƙasarmu.
3. Ɗan uwa
zo nan kaji ni,
Dan mu zamto
kare kanmu.
4. Mun shiga
uku nan ƙasarmu,
Munyi kuka ba
a jinmu.
5. Munyi wayyo
munyi wayyo,
Babu mai kula
duk kiranmu.
6. Kar mu zargi
shuwagabanni,
Mu mukai cuta
wa kanmu.
7. Dan kwa
munce bamu zaɓar,
Wanda zai
gyaran ƙasarmu.
8. Mu nufin a
bamu Naira,
Sai mu bayar ƙurri'unmu.
9. Ba tsayawa
mui tunanin-
Yin hakan mai
zaya bamu.
10. Sai ilahu
ya zare hannu,
Sai ya barmu mu
ƙwaci
kanmu.
11. Ga shi ko
duk munyi laushi,
Har fita na gagararmu.
12. Gashi koda
munyi noma,
Bamu noman yaiishe mu.
13. Kasuwanci
babu riba,
Don kwa cuta ce
a ranmu.
14. Gashi bamu
ruƙon
amana,
Kunga mu muka
cuci kanmu.
15. Shugabanni
na gwaramu,
Basu ko tuna ƙauyukanmu.
16. Ko garin ma
ba ruwansu,
Babu tsarin
taimakonmu.
17. Ga shi koda
munyi boko,
Mun gama ba mai
kula mu.
18. Ku ku ce
kuma muyyi bokon,
Dan muyo gyaran
Ƙarsarmu.
19. Gashi munyo
babu aiki,
Ba sana'ar kare kanmu.
20. Daga nan
wasu sai fasadi,
Sai su
dawo sukkashemu.
21. Koda yaushe
sui fakonmu,
Dan su samu kuɗi wurinmu.
22. Ko a kawo
ko su yanka,
Ko su barmu da
rayuwarmu.
23. Amma kuwa
shi mutunci,
Sun zubarwa
‘yan uwanmu.
24. Sunyi fyade
aggaresu,
Sun buge su
cikin gidanmu.
25. Wani ma a
gaban ɗiya tai,
Ko iyali za su karmu.
26. Wani sa'in
subbugemu,
Ga iyali na ganinmu.
27. Ba su ikon
yin kataɓus,
Babu komai ‘yan
uwanmu.
28. Don kwa
mune ja wa kanmu
Don fa nan a cikin ƙasarmu-
29. Shugabanni
ba ruwansu,
Basu tausan
rayukanmu.
30. Ba ruwansu
mu kwan da yunwa,
Ko da jinya ajjikin
mu.
31. Ko karatu
nan ƙasarmu,
Dakkuɗinmu muke abinmu.
32. To idan mun
gane wannan,
Ba batun wai
za'a bamu-
33. Ayyuka a
cikin Ƙasarmu,
Sai mu dawo
taitayinmu.
34. Duk muzo mu
riƙe
sana'a
Don mu tsira da
rayuwarmu.
35. Kunga kenan
koda aiki,
Ko rashi nai ba
ruwanmu.
36. Zamu rayu
cikin salama,
Babu mai cin
zarrafinmu.
37. Babu me
cewa muzomu,
Don mu sheƙe ‘yan uwanmu.
38. Don muna da
kuɗin abinci,
Babu yunwa
ajjikinmu.
39. Daga nan
kuma babu ɓarna,
Ba kisan kai
accikinmu.
40. Ba batun
(kidnaf) cikinmu,
Mun riga mun
kare kanmu.
41. Shugabanni
ga ya saƙo,
Kar ku manta
kaliƙinmu.
42. Shi ya baku
riƙon
ƙarsarmu,
Don ku kare
rayukanmu.
43. Kunyi
kamfen dan mu baku-
Dangwalenmu ku
hau samanmu.
44. Kunyi Alƙawari
na ƙarya,
Zaku kare yan Ƙasarmu.
45. Zaku kauda
dukkan talauci,
Zaku yaye
fargabarmu.
46. Kana aiki
zaku bamu,
Ba zaman banza
cikinmu.
47. Haka nan
zamui karatu,
Babu ko sisi kuɗinmu.
48. Gashi yau a
cikin ƙasa
ta,.
Da kuɗin ya gagaremu.
49. Don karatun
yayi tsada,
Shin ina wai
zaku kaimu?
50. Ga shi
kunce lafiyarmu,
Babu mai kuka
cikinmu.
51. Ko kwa dama
kun faɗa ne,
Don kuyo cuta
garemu.
52. Haka nan
kuka ce ruwa ma,
Zai wadata
cikin garinmu.
53. Dukka kauye
dukka saƙo,
Zamu warwasa
rayuwarmu.
54. Ba wutar
(NEPA) ƙasarmu,
Gashi kunce
zamu Samu.
55. Ba wutar
kuma ba ruwan duk,
Munyi Two Zero
ku ji mu.
56. Ga ƙasarmu
da arziƙinta,
Kun riƙe sam
baku bamu.
57. Tituna sam
babu kyawu,
Can ga hanya
attaremu.
58. Ko kuɗi ko mui ta ranmu,
Ba ruwanku da
rayukanmu.
59. Ga shi
harkar nan ta noma,
Tallafin mu ba
a bamu.
60. Shugabanni
karku manta,
Ranstuwa kunyo
gabanmu.
61. Zaku
taimaki al'umarmu,
Aiyyuka kuma
zaku bamu.
62. Ga shi dai
Allahu yaso,
Kar kuyo nisa
ku barmu.
63. Kar ku tare
can Abuja,
Mu kwa nan ƙauye
ku barmu.
64. Mui ta
holoko abinmu,
Babu mai sisi
cikinmu.
65. Ga matasa
nata yawo,
Sun zamo
matsala garemu.
66. Su suke
dukkan fasadi,
Su suke sata
garinmu.
67. Ba sana'a
babu aiki,
Kaga kwai
matsala ƙasarmu.
68. Yan siyasa
kuiwa Allah,
Kar kuyo nisa
ku barmu.
69. Kun riga
kun ɗau Amana,
Kar ku bar
kishin Ƙasarmu.
70. Kui ta aiki
kui ta aiki,
Yin hakan ne
taimakonmu.
71. Daga nan
kuma zamu gane
Ɗan
halak waye cikinmu.
72. Zamu gane
mai Butulci,
Mai shirin cuta
garemu.
73. Wanda sam
sam baida kunya,
Za ya dawo nan
wurinmu.
74. Za ya zo
nema wajenmu,
Maga Mai bi nai
cikinmu.
75. Za ya gane
yan halak ne-
Mu ga duk mai
taimakonmu.
76. Ga mu dai
wai mu da yanci,
Ga ƙasashe
sun wuce mu.
77. Sunyi nisa
gamu baya,
Baku sam kishin
ƙasarmu.
78. Ga shi tare
anka bamu,
Dukka ‘yanci
mun zamo mu-
79. Ga mu can
mu ne a baya,
ba shirin gyara
ƙasarmu.
80. Can a farko
shugabanni,
Yan mazan jiya
masu sonmu.
81. Sunyi aiki
babu wasa,
Duk shirinsu
ginin ƙasarmu.
82. Jami'o'i
sun ginawa
Dan ginin goben
ƙasarmu.
83. Asbitoci
gasu nan duk,
Dan kulawar
lafiyarmu.
84. Kamfanoni
ko ina duk,
Ba zaman banza
cikinmu.
85. Babu sata
babu cuta,
Sunyi aiki
aggaremu.
86. Ga wasunsu
na ambace su,
Ɗan
tafawa uba wurinmu.
87. Shi ya sa ɗanba ta gyara,
Gashi yau mun
samu kanmu.
88. Babu shi
wasu sun kashe shi,
Sunyi cutarwa
garemu.
89. Amadi
Sardauna zaki,
Can yana nan
zuciyarmu.
90. Adu'ar
kairi muke mar,
Ya yi aiki nan ƙasarmu.
91. Ya ilahu
abun nufi na,
Gamu nan duk
‘yan Ƙasarmu.
92. Munyi roƙo duk
gareka,
Dan kwa kasan
duk halinmu.
93. Kar ka
barmu da namu wayo,
Ya gwaninmu ka taimakemu.
94. Daga ƙarshe
nai salati,
Gun Muhammadu
shugabanmu.
95. Har da Ali
dama sahabu,
Wanda su ne
fittilunmu.
96. Zana sa aya
na nisa,
Can fa Ringim
ne garinmu.
97. Nassarawa
unguwarmu,
Nan da kaje ga
gidanmu.
98. Gata nan
baiti Ɗari
cif,
Nayi bulala
garemu.
99. Ni Aminu ake kirana,
Mai burodi uba
garemu.
100. Hamdala
nai wa ilahi,
Kaliƙi
sarki gwaninmu.
ABU ISA
ASSHANKIDY
Aminu Sani Uba
Ringim
08162293321
Aminusaniuba229@gmail.com
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.