Muhammad
1. Shin zaku
barni na shaƙata
ne kokwa dai?
Sai nayi ƙwaƙuduba gami da hatsaniya.
2. Ni ne kaɗai mai zuge tsinke kai
guda,
Ni ke zama
sarki a waƙeƙeniya.
3. Ni ne nake
kutufo da alƙalami
idan-
Aka ambace ni sukanyi watsin watsiya.
4. Ni ne kaɗai kayin dubu ɗaya ba jira,
Ni ne nake
wanke shirinsu gaba ɗaya.
5. Ni ɗai ka furta guda tazam
tamkar dubu,
Su sunyi-sunyi
su tazaga kan ya ƙiya.
6. Sun ambace
ni suna ganin dai-dai dasu,
Sai aljaninsu
yace da su "ni ban iya" .
7. Suka zo gare
ni suna ta neman lamuni,
Har zabiyar ga
tana ta neman yafiya.
8. Wai ni ina
suke ne mawaƙan
kokwa dai?
Sun lallaɓa sun zagaye ta mazagaya.
9. Yau dai ina
tsaye kyam gabanku saman dubu,
Zan ɗauki bulala kamar mai
zaniya.
10. Duk wanda
zai yi amo saman mai yin amo,
To babu shakka
zai ji saukar tsamiya.
Aminu(Abu Isah
Asshankidy)
11. Kai Dan
tsaya yaro staya nan don kaji,
Domin a nan da
Akwai gwaninka a ƙafiya.
12. Ni ne
idan har nayyi baiti na guda,
To in nayo
jama'ar garin mu ya zagaya.
13. Duka basu
gane mai nace a cikin batun,
Domin kwa
baitin ya zamo ya Wahainiya.
14. Sai sui
zaton na ce kaza Amma kwa ni,
Maganar da nai
nasan akwaita akwai wuya.
15. Sai dai su
dawo nan wuri na don suji,
Domin kwa
Hausar tasu Sam ba lafiya.
16. Ni ne mawaƙa ke
jira domin su ji,
Ni ne kasumi na
ka neman yafiya.
17. Domin kwa
yasan in na ɗau Alƙallami,
Kashin sa ya
bushe da zar na dulmiya.
18. Ni ne
sarakai ke Kira domin na yo.
Waƙe gare
su ya zam karaɗe
Duniya.
19. In har na
ce yau za na yo alfahhari,
To ba batun
wani ma ya buɗe
Idaniya.
20. Domin kwa
komai zai faɗa bai kai
ya ni.
Domin kwa manzo
ne fa ni gun ƙafiya.
Muhammad(Maisugar)
21. Kai dakata
kaji nifa na ja sansani,
Na kutsa kai a
cikin taɓo da cikin ƙaya.
22. Na danna
kai na inda ma baka zato,
Na shallake
nisan dare sarƙaƙiya.
23. Na taka
tsauni na bi dukka kwazazzaɓai,
Na taka rami
kan taɗai da ƙarangiya.
24. Na samu
taron sha'ira daga nesa ma,
Suka ce dani
"mun barka mun san ka iya".
25. Ballantana
sauro da ke bin lunguna,
Don
tsince-tsince da rana wai shi jan wuya.
26. Ni ne karen
bana na wuce zomon bana,
Koda cikin kogi
na kan saka rariya.
27. Zan so ku
tambayi ƴan'uwa
na saman dare,
Wannan dake tafiya
da sanyin safiya.
28. Ko ramukan
da suke wuyar tsotse ruwa,
Na sha ruwa
daga zabako da maɗaciya.
29. Na maida alƙalami
dubu harafi guda,
Ni ne ka sharen
ƙulafutan
su da tsintsiya.
30. Waƙa gida
na ne a barni na wataya,
Ni ne kaɗai sarkin ta ko da
Tsiya-tsiya.
Aminu(Abu Isah
Asshankidy)
31. Kai wanne
zance ne kake ba kan gado?,
Daga jinsa ya
fi kama ace Tatsuniya.
32. Wane mutum
wane mutum kowa yake,
Ya iso garen
koda gidansu da Zabiya.
33. Ni ne nake
waƙe
cikin sa a guda,
Haka zata zo
wal-wal kamar dai Walkiya.
34. In sha'irai
suka jita sai sun kwaikwaya,
Yaro ka zauna
kar ka zam mai tankiya.
35. Tun can
fagen Waƙa
fa ni na gagara,
Wasu sha'irai
suka so suyi min Kurciya.
36. Sai dai fa
kash! ai sun riga sun makkara,
Bokansu ya ce
tuntuni ni na iya.
37. Sui haƙƙuri
domin kwa ni ne Kan gaba,
Ba Mai wuce ni
idan ina nan Duniya.
38. Suka zo
garen suka durkusa suka mika Kai,
Don na zamo can
Kan gaba lamba Ɗaya.
39. Kar dai ku
manta tun a can na fada muku,
Ni akka baiwa ƙafiya
ko kun ƙiya.
40. Ban San
yabon Kai na a bainar jamm'a,
Domin hakan shi
ne ka tada hatsaniya.
Muhammad(Maisugar)
41. Wai kai ina
ka fice da har aka san ka ma?
Zai dai fi kyau
ka tsaya gida ka ci taliya.
42. Ni ne ka
yin sauti ya farfasa ganguna,
Ni ne ka yin
magana a tsaida hatsaniya.
43. Harni ka ke
tankawa in nai baituka,
Lallai fa yaron
nan kana da ƙiriniya.
44. Yau zan kaɗe ƙurar da ke ruɗa ta ka,
Na sanar da kai
bam-ban zuma da maɗaciya.
45. Don ni
sahara koguna nan ne gida,
Yara da mata
sunka jurar kwalliya.
46. Hular sarautar ƙafiya na ƙaƙaba,
Na sa fara na
sa baƙa
wata koriya.
47. Daga nai
kiran baiti guda sai ga ɗari,
Suka ce da ni
don Allah kar kayi turjiya.
48. Kafin na
ankara sai dubu suka hallara,
Suka ce da ni
"mu ma muna daɗa
godiya" .
49. Yaro ka
bini a hankali don na wuce-
Shata wurin waƙar da
ba ɗirkaniya.
50. Na zarce
‘yan koren mawaƙan zamani,
Na san Mu'azu,
Aƙilu
kaji mazan jiya.
51. Na san
Sa'adu gwani wurin zuba baituka,
Ballantana Ala
da ke mini rakkiya.
52. Ni sunka
bauta ko ga waƙar in sukai,
Balle su Hauwa
gwaram ɗiya jaririya.
53. To
dukkaninsu kana aje su wuri guda,
Dolen su ne da
muƙarrabansu
su sunkuya.
54. Su fake da
baiti na guda da na ƙirƙira,
Su tsaya su karɓi tabarraki suyi kwaikwaya.
55. Kalle ni
nan a cikin ido na mai ka ga,
Na kwan dubu ba
gyangyaɗi ga idaniya.
56. Zo kalli
takalman da ke bin ramuka,
Ko su sukanyi
dubu haɗewar ƙafiya.
57. Ni ɗai ka cinna wuta a kundin
baituka,
Kafin subahi na
zubo wa zai iya?.
58. Damar ka
yanzu ka bini sannu a hankali,
Da na saka ka cikin mawaƙa ka
iya.
59. Shin za ka
tashi ka tattare ne ko ko dai?
Sai na saka
yaran ga sun maka dariya.
60. Waƙa gida
na ne a barni na fantama,
Ni ne kaɗai sarkin da babu
sarauniya.
Aminu(Abu Isah
Asshankidy)
61. Shin wanga
waƙe
ne ko ko hakan?
Maganarka ce
don duk ciki kwakyariya.
62. Wake batun
wani sha'iri in dai dani,
Ni ne nake
watse shirusu gaba daya.
63. Domin idan
har nayyi baiti na guda,
A cikin dare
tuni ya bazu kan safiya.
64. Lambar yabo
aka ban nace ni bani so,
Domin kwa ni
wahayi ake min kun jiya.
65. Ya zakayo
waƙe
ka zan dai dai dani?
Kai haƙƙuri
ya ɗan uwa don na iya.
66. Ni ne nake
waƙar
siyasa don kuji,
Wasu ma suyo
koyi waɗansu su
rairaya.
67. Dukkan
fagen waƙe
fa ni duk na iya,
Jigonta duk na
yo fice ban zamiya.
68. A fage na
so ni ne ka waƙe sai ka ce,
Majnunu laila
shugaba tun can jiya.
69. A fagen
Habaici ko ko zambo Kar ka yo,
Wasa dani domin
kwa zanma kwaf ɗaya.
70. Waƙe wuri
na ni fa koda shan ruwa-
Ya fi shi domin
shan ruwa da akwai wuya.
71. Ita ko da
zar na buɗe baki zaku
ji,
Baiti
guda,baiti dubu ba Turjiya.
72. Ga tambaya
amsarta ban domin nasan,
Kai sha'iri
kake wanda yassan ƙafiya.
73. Shin
sha'irai nawa ne a can suka san da kai?
Suka ce “da
kyau waƙarka
tai” ba Tankiya.
74. Ko da kwa
mun duba Bama same su ba,
Baka cikin Duk
sha'irai fa gaba ɗaya.
75. Kai haƙƙuri
ya ɗan uwa kai
laddabi,
Don in kayo
wasa dani ka malgaya.
76. Don
sha'irai basa barin mai ja dani,
Wane mutum ya
wuce yaje ga samaniya.
77. Karma ka
fara batun ka zam dai dai da ni,
Domin kwa kuka
zakayo da idaniya.
78. Duk
sha'irai sunzo garen sun miƙa kai,
Suka ce gwani
kayyo tayi dan ka iya.
79. Domin haka ya
ɗan uwa ga shawara,
Kai haƙƙuri
kai ma ka miƙo
min wuya.
80. In kaƙi bi
to Sha'irai sun bi maka,
Ni ne ka mulkin
duniyar yin ƙafiya.
Daga Alƙalamin
Muhammad Muktar
(Maisugar)
Da
Aminu Sani Uba (Abu Isah Asshankidy)
aminusaniuba229@gmail.com
08162293321, 09123098967, 07034370481
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.