Wani Muhimmin Tarihin Bunguɗu

    "Dag ga minsharik'i ham mingaribi,
    Kowa aj jikan Ɗ/hodiyo
    Dole ya ba da aminci Bunguɗu,
    An shirya haka tun kakanni,

    Gogarma raba kaya
    Shehu na S/Rwahi na Malan Attoh.

    Daga Waƙar Marigayi Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu ta biyu.

    *Sarkin Rwahi/Sarkin Rafin Kwaikwai, watau Dagacin wani Ƙauyen Bunguɗu da ake kira Kwaikwai (yanzu gunduma ce a Masarautar Bunguɗu). Malan/Malam Attoh kuma Alhaji  Attahiru ɗan Sarkin Fulanin Bunguɗu Kure wanda ya haifi Sarkin Fulanin Bunguɗu na yanzu, Alhaji Hassan Attahiru. Tsohon Ɗan Boko ne domin har Wakilin Majalisar Wakilai ta Tarraya yay yi a Ikko a lokacin Siyasar Jamhuriya ta ɗaya a ƙarƙashin Jam'iyyar NPC ta su Sardaunan Sakkwato. Allah ya jiƙan su da rahama, amin.

    Watau daga iyakar Daular Usmaniya farkon ta zuwa ƙarshen ta tun daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi wanda shi ne jagoran gidan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi har zuwa sauran masu sarauta daga wannan tsatson( "kowa aj jikan Ɗanhodiyo..) dole su yarda su amince, su  kyautata, su kuma ci gaba da riƙe hulɗar dake tsakanin gidansu da gidansu Ɗanmadamin Sakkwato na Bunguɗu, watau gidan Sarkin Fulanin Bunguɗu, saboda me? Saboda wannan hulɗa ta samo asali ne tun daga Kakannin su da suka yi tarayya a Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniya (Gidan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da Gidan Malam Ɗan Zundumi wanda shi ne Sarkin Fulanin Bunguɗu na farko.

    A wannan gwagwarmaya fitaccen Sarki daga wannan zuriya ta Sarkin Fulanin Bunguɗu da ya taka muhimmiyar rawa shi ne Sarkin Fulani Muhammadu Bachiri wanda tare da shi da Malam Muhammadu Sambo Ɗan Ashafa na Gusau da Malam Muhammadu Da'e/Daɗi na Maru da Malam Muhammadu Namoda na Ƙauran Namoda ne suka kula da yankin Zamfara amadadin masu jihadi.

    Malamin Waƙa ya taskace wannan tare/hulɗa ce tsakanin Gidan Mujaddadi da Gidan Sarautar Bunguɗu domin fitowa da daraja da girman wanda ya waƙe. Allah ya jiƙan magabatanmu, amin.

    Daga Taskar

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.