Wata Rana (001)

    Wata rana a farko farkon shekarun 1980s, muna zaune a garkar mai garinmu (Birnin Magaji dake cikin Jihar Zamfara a halin yanzu) bayan an kammala Sallar Isha'i sai ga wata mata tazo da ƙorafi game da mijinta a wajen mai garin namu(Ɗan Alin Birnin Magaji, Alhaji Muhammad Mode Usman a lokacin ya na matsayin Dagaci. Ya yi sarauta daga shekarar 1945 zuwa rasuwarsa a watan Oktoban shekarar 2005) cewa ta na son a raba aurensu. Ɗan Ali ya dalla mata tocilan ya tambaye ta wane ne mijin nata, ta gaya masa, ya sake tambayar ta me ya sa ta ke neman a raba auren nasu, ta ce ta dai gaji ba ta iyawa.

    Nan take ya aika aka zo da mijin da kuma iyayen wannan matar a gabansa. Ya sake tambayar ta bahasi, sai ta gaya masa cewa suna zaune tare da mijinta ne a cikin gidansu(mijin) na gado, kenan akwai magidanta da iyalansu a ciki da yawa. Ya ce ya na barin ki da yunwa ko tsumma ko kwaÉ—ayi ko rashin zamantakewar aure ne? Ta ce ko alama, ya ce to wace irin matsala ce mai nauyi haka har kike neman rabuwa dashi? Ta ce duk cikin mazauna wannan gida da suke a ciki ita ce kurum ke tu'ammali da Tsabar Dawa wajen yin fura da kuma Tuwo saboda haka ta gaji da wannan abin kunya.

    ÆŠan Ali ya ce madalla, ya aika a cikin gidansa a zo mashi da fura, aka shiga aka karÉ“o fura a cikin kwano aka kawo masa. Ya shanye kusan rabin kwanon furar nan, sannan ya ajiye kwanon a Æ™asa, ya dalla tocilan a cikin kwanon ya ce tun da matar tana tu'ammali da tsabar dawa za ta iya gane fura idan ta dawa ce, ta ce masa haÆ™iÆ™a, ya ce to ta duba wannan furar me ce? Ta ce  furar dawa ce, ya ce mata da ÆŠan Ali da iyayenki wa ne ne ya fi girma a garin nan? Ta ce ÆŠan Ali ne mafi girma, ya ce ke lura furar dawa ya ke sha a gidansa ballantana ke ki ce baki son tu'ammali da dawa ko? Ta ce eh Allah ya baka nasara, ya ce to ba za raba ki da mijin ki kan wannan dalili ba, na mayar dake É—akinki kuma daga yau kada in sake jin irin wannan magana. Ya juya wajen iyayenta ya ce masu ku dinga tsawata ma yaranku domin kaucewa irin waÉ—an nan Æ™ananan maganganu. Allah ya yi maku albarka, miji da iyayen matar suka yi godiya suka tashi.

    Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    Daga Taskar

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com

    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.