Ya Ya Kamata Na Yi Da Ribar Bankin Da Na Amsa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman Sunna akan kuɗin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi ya buɗe account ɗin da za'a dinga saka masa kuɗin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda bai daina ci ba à cikin aya ta 275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka zo bayanta:

    الَّذِينَ يَأْكُلُونَ الرِّبَا لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ الَّذِي يَتَخَبَّطُهُ الشَّيْطَانُ مِنَ الْمَسِّ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوا إِنَّمَا الْبَيْعُ مِثْلُ الرِّبَا ۗ وَأَحَلَّ اللَّهُ الْبَيْعَ وَحَرَّمَ الرِّبَا ۚ فَمَنْ جَاءَهُ مَوْعِظَةٌ مِنْ رَبِّهِ فَانْتَهَىٰ فَلَهُ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُ إِلَى اللَّهِ ۖ وَمَنْ عَادَ فَأُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ

    Wadanda suke cin ribã ba su tashi, fãce kamar yadda wanda da Shaiɗan yake ɗimautarwa daga shafa yake tashi. Wancan, dõmin lalle ne sun ce: "Ciniki kamar riba yake."Kuma Allah Ya halatta ciniki kuma Ya haramta riba. To, wanda wa´azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'annan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne. (Suratul-Bakara Aya ta 275)

    يَمْحَقُ اللَّهُ الرِّبَا وَيُرْبِي الصَّدَقَاتِ ۗ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ كُلَّ كَفَّارٍ أَثِيمٍ

    Allah Yana shãfe albarkar riba, kuma Yana ƙãra sadakõki. Kuma Allah bã Ya son dukan mai yawan kãfirci, mai zunubi. (Suratul-Bakara Aya ta 276)

    Annabi ya la'anci mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi ingantacce.

    Idan mutum ya amshi Interest ɗin Banki to ya wajaba ya tuba ga Allah da niyyar ba zai sake amsa ba, tun da Allah ya Hana.

    A zance mafi inganci zai iya amfani da kuɗin wajan yin aikin da zai amfani jama'a kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za su bi su wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce.

    Wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu.

    Allah ne mafi sani.

    Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.