𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan mace suka samu saɓani da mijinta saita gaishe shi yaki amsawa, ta tambayeshi zata gaida mahaifiyarta nan ma yaki amsa mata, shin zata iya tambayar iyayensa insun ba ta izini saitaje, hakan yayi dai-dai acikin musulunci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله
Malamai sunyi
ittifaƙi
a kan haramcin fitar mace ba tare da lalura ba, ko wajabcin shari'a, ba tare da
izinin mijinta ba, suna kirga matan dasuke aikata hakan cikin kangararrun
mutane, baudaddu.
Ya zo a cikin
Mausu'ah fiƙhiyyah
(19/107)
Asali shi ne
mata an Umarcesune dasu lazimci gidajensu, kuma an hanasu fita, bai halatta ga
mace tafita ba saida izinin mijinta.
Ibnu hajar haitami
ya ce: Kod a mace ta takura wajan
ziyartar mahaifiyarta za ta fita da
izinin mijinta ba tare da kwalliya ba.
Ibnu hajar asƙalani
yaruwaito daka nawawi wajan ta'aliƙin hadisin (Idan matayenku suka nemi
izininku zuwa masallaci da daddare kuyi musu izini) ya ce: yakafa hujja dashi
cewa mace bazata fita daka gidan mijintaba saida izininsa, saboda an fuskantar
da izinin ga mazajensu.
Hakama budurwa
bazata fita daka gidaba saida izinin waliyyinta mahaifinta ko ɗan'uwanta wanda dai yake kula
da tarbiyyarta, musamman saboda lalacewar zamani dacanjawar al'amura, wajibine
ga waliyyinta ya ɗauki
wannan nauyin ya kiyaye amanar dake wajansa, tayanda zai haɗu da Allah yaladabtar da
ita ya ba ta tarbiyya ya kyautata mata ya ba ta ilmi, Abin da yake tilas awajan
budurwa shi ne ta kiyaye kada ta saɓa
masa a kan irin wadannan abubuwan, dama cikin duk wani kyakkyawan aiki, kada
tafita saida izininsa.
Saboda haka
izinin fitar mace ko ina ne zata yana hannun mijinta ba iyayensa ba, iyaye ba su da ikon baki izinin kifita
a maimakon mijinki wannan ya saɓa
da koyarwar musulunci.
Saidai bai
halatta gashi miji insun samu saɓani
da matarsa ta dawo kuma tanayi masa biyayya ya ce zai cigaba dafushi a kan saɓanin harta gai da shi ya ƙi amsawa wannan baya daka cikin koyarwa ta
musulunci kuma laifi ne kuskure ne ya kamata mazaje masu irin wannan mugun hali
suji tsoran Allah su gyara, Allah madaukakin Sarki ya ce:
... فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا عَلَيْهِنَّ سَبِيلً ...
Idan Suka dawo
sunayi muku biyayya bayan kunsamu saɓani
kada kubijiro musu dawata hanyar ta musgunawa da ramuwar gayya.
A bisa Abin da
ya gabata yaharamta a kan mata sudunga fita ba tare da izinin waliyyansu ba,
matan aure da 'yan mata.
Iyay ba su da
ikon baiwa surukarsu izinin fita, saidai ta bi hanyoyi na lumana da mutunci
dasanin ya kamata ta karkato da zuciyar mijin nata harya hakura ya ba ta izini.
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan ƙwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.