Ticker

6/recent/ticker-posts

Abara Dan ‘Yakkolo

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Abara Ɗan ‘Yakkolo

 

G/Waƙa: Mai alamar aiki,

: Abara ɗan ‘Yakkolo.

 

 Jagora: Ya matsa ma aikin daji,

 ‘Y/ Amshi: Yanzu gari yai kwana.

: Mai alamar aiki,

: Abara ɗan ‘Yakkolo.

 

 Jagora: Gona ta biya[1] ka,

 ‘Y/ Amshi: Tai maka dawa Abara tai maka gero,

: Mai alamar aiki,

: Abara ɗan ‘Yakkolo.

 

 Jagora: Maza akwai tserewa[2].

 ‘Y/ Amshi: A rabu da ƙaryar banza.

 

 Jagora: Kunne na gani.

 ‘Y/ Amshi: Kaho ya tsere,

: Baya da damac cim mai,

: Mai alamar aik,i

: Abara ɗan ‘Yakkolo.

 

 Jagora: Abara ya yi man abun mamaki,

 ‘Y/ Amshi: Ga lokacin aure nai.

 

 Jagora: Goma goma har sau goma.

 ‘Y/ Amshi: Ga lokacin ‘Yakkolo.

 

 Jagora: ‘Yakkolo tana yiman alheri.

 ‘Y/ Amshi: Ta zaka[3] tai man komi,

: Mai alamar aiki,

: Abara ɗan ‘Yakkolo.

 

 Jagora: ‘Yakkolo ta yi batun mai geme.

 ‘Y/ Amshi: Bata yi batun banza ba.

 

Jagora: Lallai ta yi batun mai gemu.

 ‘Y/ Amshi: Bata yi batun mata ba.

 

 Jagora: Ashe batun ki ya zama dutse[4].

 ‘Y/ Amshi: Bata yi batun banza ba.

: Mai alamar aiki,

: Abara ɗan ‘Yakkolo,



[1]  Samar da amfanin gona mai nagarta.

[2]  Fifiko.

[3]  Zowa, wato mutum ya zo daga wani wuri.

[4]  Gaskiya ko tabbas

Post a Comment

0 Comments