Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Abdulkarimu
A garin Maɗwacci ne Abdulkarimu yake, na
yamma ga Rini ta ƙaramar hukumar Bakura. Ya
shahara da noma na hatsi, Amali ya kula shi ya kai masa waƙa.
G/Waƙa : Ko da rani ba ya zama gida,
: Gidan Karimun Za
ni wurin
: Kiɗi.
Jagora: In
dai da dama,
: Dama dawo[1]
akai,
‘Y/Amshi:
In babu dama sai a yi dangana,
: Ko da rani ba ya zama gida,
: Gidan Karimun za
ni wurin
: Kiɗi.
Jagora: Ku ɗan rage
mani in hwaɗi mai : dawo,
‘Y/Amshi: Ku
ɗan rage mani,
: In hwaɗi mai dawo,
Jagora: Ina
dawon yake?
: Ina dawon yake?
‘Y/Amshi:
Ina dawon yake?
: ‘Yammani in ƙuta[2].
: Ko da rani ba ya
zama gida,
: Gidan Karimun,
: Za ni wurin kiɗi.
Jagora: In dai ana dara hid da uwa akai. ‘Y/Amshi: Lalle irin haka gane maza
akai,
Jagora: In dai ana haka,
: Gane maza mukai,
‘Y/Amshi: Lalle
irin haka,
: Gane maza mukai,
: Ko da rani ba ya zama gida,
: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.
Jagora: Ku na Arewa,
: Da ku da na nan kudu,
: Na Yamma,
: Da ku jama’ag Gabas,
: Maza da mata
kui mani gahwara.
‘Y/Amshi: Amali gobe gida yaka son zuwa.
: Ko da rani ba ya zama gida,
: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.
Jagora:
Abdu Karimun,
: Abdu Karimun,
‘Y/Amshi: Hatta[3]
tahiyakka,
: Kama da ta Rabi’u.
Jagora:
Ko maganakka,
: Kama da ta Rabi’u,
‘Y/Amshi: Ko maganakka,
: Kama da ta Rabi’u.
: Ko da rani ba ya
zama gida,
: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.
Jagora: Masu
zuwa haji kui ta zuwa haji,
‘Y/Amshi: In
don karen ɓuki[4],
: Ba ya zuwa haji,
: Sai dai ya
sami gyaɗa,
: Ya yi ƙanƙara,
: Ko da rani ba ya
zama gida,
: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.
Jagora: Ina Kulun take?
: Hauwa Kulun Kulu,
‘Y/Amshi: Hauwa
Kulun Kulu,
: Ke gwadi kin aje[5],
: Da ke da Dammo,
: Kui mani : taimaka,
: Ko da rani ba ya zama gida,
: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.
Jagora: Masu zuwa haji kui ta zuwa haji,
‘Y/Amshi: In dan karen ɓuki,
: Ba ya zuwa haji,
: Sai dai ya
sami gyaɗa,
: Ya yi ƙanƙara,
: Ko da rani ba ya
zama gida,
: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.