Ticker

Agwada Birni

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Agwada Birni

 G/Waƙa: Haba yara,

: Mu koma Agwada ya hix2

 

 Jagora: Tun ban je Agwada ba,

: Ana labarin Agwada birnix2

: An ce Agwada dawa,

: Kuma an ce agwada gero,

: An ce Agwada ilmi,

: Kuma sun ce Agwada maiwa,

: Sun ce Agwada naira,

: Kuma an ce Agwada shanu.

 

Jagora : Haba yara,

: Mu koma agwada birni,

: Da na je Agwada,

: In gwada masu,

: Waƙa da kiɗa tsintsa[1],x2

: Mutanen Agwada sun gwada,

: Muna aikinsu zuwa gona.

 

  Jagora: Da naje Agwada na ɗaya,

: Sai ga dame ɗari,

: Had da bakwa daidai,

: Suka bai wa bahago Sani,

: Kuma ga wan tauzan[2] ka riƙa,

: Saboda nono da suga kullun.

 

  Jagora: Cikon na biyu,

:Na koma zuwa hira,

: Sai ga dame ɗari,

:Had da bakwa daidai,

: Suka baiwa Bahago sani,

: Kuma ga wan tauzan ka riƙa,

: Saboda nono da suga kullun.

 

 Jagora: Kuma na ukku,

: Na sake zuwa hira,

: Sai ga dame ɗari,

: Had da bakwa daidai,

: Suka baiwa Bahago Sani,

: Kuma ga wan tauzan ka riƙa,

: Saboda nono da suga kullun.

 

 Jagora: Ba ni koma zuwa gona.x2

: Na huta da yini rana.

: Idan na ji yunwa Agwada niy yi.

: Ko ba ni ba,

: Ni mai waƙa da kiɗi Sani,

: Ko kai ka ji yunwa,

: A gwada maka hanyar,

: Agwada birni,

: Da ka je Agwada,

:Su gwada maka shago,

: Da dawon[3] gero,

: Da nono da suga kai ɗai.

 

Jagora: Haba yara,

: Mu koma Agwada birni.

: Yaƙi noman sarki,

: Inji Sani bahagon Inno,

: Aikin tafiya,

: Falke aka bar ma da mutane nai,

: Yaƙi noman sarki,

: Inji Sani bahagon Inno,

: Aikin tafiya,

: Falke aka bar ma da mutane nai,

: Sha’anin duniya,

: Kowa ya bi hanyar da yake tsira,

: Sha’anin duniya,

: Kowa yabi hanyar da take kai,

: Ko waƙ ƙi ka da ɗa,

: Ya gane ka da jikanka

: Kana tawai[4],

: Kuma baya da halin,

: Ya taɓa ma shi.

 

  Jagora: Sha’anion duniya,

: Kowa da masoyinsa yake kuri

: Ko Mamman da masoyana.

 

Jagora: Sha’anin duniya,

: Kowa da masoyinsa yake ƙarya,

: Ko Mamman da masoya na,

 

Jagora: A bayar a rasa,

: Ita ke hana yaro kaji motsi nai,

: A bayar a rasa,

: Ita ke hana raggo kaji motsi nai.

: Allah waddan samun raggo,

: Bai ci ba bai sha ba,

: Bai tcere ma abokai ba.

 

  Jagora: Haba yara,

: Mu koma Agwada birni.

: Amadu rikiji ɗan Cindo.

: Amadu rikiji na gode ma,

: Zakin Agwada ka biya[5],

: Ka taimaki gangata.

: Ina ɗan mutuwa?

: Yara ina Ɗan mutuwa Ada?

: Mai fetur mutumin Sani.

: Sale Ɗan Maidaji,

: Allah ya kiyaye ka.

: Sale ɗan Maidaji,

: Ka taimaki gangata.

: Sarkin maƙera na gode mai,

: Allah ya kiyaye ka.

 

 Jagora: Musa na Sale,

: Allah ya kiyaye ka.

: Na Binta a gaishe ka,

: Sannu na Saratu na gode ma,

: Baban Saratu ka kyauta,

: Ka kyauta ma ƙanen Inno,

: Yada kai mani,

: Ka taimaki[6] gangata.

 

  Jagora: Alhaji Sani Ɗanƙwari,

: Allah ya kiyaye ka,

: Sannu na Balki,

: Ka taimaki ganga ta.

: Haba yara,

: Ku koma Agwada ya fi.

: Yaƙi noma sarki,

: Inji Sani bahagon Inno.x2

: Aikin tafiya,

: Falke aka barma da mutane nai.

: Haba yara,

: Ku koma agwada birni.

: Sannu Ɗan Halima na gode ma,

: Ɗan Halima na gode,

: Ka kyauta ma ƙanen Inno.

: Sha’aibu shuti na gode ma,

: Sannu Sha’aibu shuti,

: Mutumin Sani,

: Wada kai mani,

: Allah ya kiyaye ka.

 

  Jagora: Kansilan Agwada na gode,

: Ka taimaki ganga ta.

: Na tuna Audu,

: Magajin Agwada sabo,

: Darzaza Bahagon[7] gulbi,

: Ka ci gwani dudda jirage nai,

: Na san ba ka barin bami,

: Yada kai mani,

: Ka taimaki gangata.

: Na so ku haɗa min,

: Waƙa da kiɗin noma.

: Haba yara ku koma Agwada,

: Haba yara mu koma agwada.

 

Jagora: Tun ban je Agwada ba,

: Ana labarin Agwada birni,x2

: An ce Agwada naira,

: Kuma an ce Agwada gero,

: An ce Agwada dawa,

: Kuma an ce Agwada maiwa,

: An ce Agwada ilimi,

: Kuma an ce Agwada…….

: Haba yara,

: Ku koma Agwada birni,x2

: Daga Maiyama idan han na tashi,

: Na kama gabas daidai

: Sai hanyar Agwada,

: Daga Maiyama idan han na tashi,

: Na kama gabas daidai

: Sai hanyar agwada,

: Haba yara mu koma Agwada,

: Sun gwada mani,

: Sun taimaki gangata.

: To ku tashi mu koma Agwada.

: Ina ɗan mutuwa?

: Ka kyauta ma ƙanen Inno.

: Sannu Ɗanmutuwa[8] Ada,

: Mai fetur mutunen Sani,

: To ku tashi,

: Mu koma Agwada birni.

: Haba yara,

:Ku koma Agwada ya fi.



[1]  Iri ɗaya babu garwayi.

[2]  Naira dubu ɗaya yake nufi, ya ari Turanci ne (wato one thousand).

[3]  Dunƙulen fura wanda ba a dama ba.

[4]  Girgiza yaro don yi masa wasa.

[5]  Yin kyauta.

[6]  Bayar da Karin kuɗi

[7]  Babban rafi mai wuyar tsallakewa saboda zurfi da igiyoyin ruwa.

[8]  Sunansa Adamu ana ce masa Ɗanmutuwa saboda sana’arsa ta sayar da man fetur saboda yana haddasa gobara.

Post a Comment

0 Comments