Aikau Jikan Tayawo

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Aikau Jikan Tayawo

    Malam Musa almajiri ne kuma manomi ana kiransa Aikau, shi ma a garin  Sububu yake kuma É—an’uwan Amali ne, yadda zumuncin yake shi ne mahaifiyar Aikau ita ce ‘yar macce shi kuma Amali shi ne É—an namiji, wato abokan wasan juna ne.

     

     G/WaÆ™a : Ya riÆ™a noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen[1] hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Ya riƙa noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da gida,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Dabgi[2] mai hwashin Æ™asa, É—an Isah.

    ‘Y/Amshi: Ya riÆ™a noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Riƙa kada gona ta kwana ɗan Mamman,

      : Jagu[3] mai awon Æ™asa É—an Isah.

     ‘Y/Amshi   : RiÆ™a kada noma ya kwana,

    : ÆŠan Mamman,

      : Gyado[4] mai awon Æ™asa,

     

     Jagora: Kana yi ma gona kamar gudun Æ™ato. x2

      : In ya hangi gobara,

    : Har in yaz zan gidan su tak kama,

      : Ban san mai tare shi ba,

        ‘Y/Amshi: Rannan ko galbi[5] as saman hanya,

      : Sai dai yai Æ™ire biyu.

      : Ya riÆ™a noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

       

    Jagora: In dai sallah ka kai  bar tsahi,

    : Ba ka dai gadi yinta ba.

    : In kuma tsahin ka kai ka bar sallah,

    : Ka san ba su gamuwa.

        ‘Y/Amshi: Ku diba idanun mutum kamar maye,

      : Jawur ba su da hwari.

      : Ya riÆ™a noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

        

    Jagora: In dai sallah ka kai  bar tsahi,

    : Ba ka dai gadi yinta ba.

    : In kuma tsahin ka kai ka bar sallah,

    : Ka san ba su gamuwa.

        ‘Y/Amshi: Ku diba idanun mutum kamar maye,

      : Jawur ba su da hwari.

      : Ya riÆ™a noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

       Jagora: Aikau har inda nig ganai arne,

    : Bai san yau da gobe ba.x2

        ‘Y/Amshi: Da duk kac ce yau da gobe Sai Allah,

    : Sai dai yai ta dariya.

     

      Jagora: Kuma ba shi zuwa idi,

       ‘Y/Amshi: Bai zuwa Jumu’a,

      : Kada ‘yanyara su ganai.

      : Ya riÆ™a noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

      Jagora: RiÆ™a kada gona ta kwana É—an Mamman,

      : Jagu[6] mai jiran ruwa É—an Isah.

       ‘Y/Amshi: RiÆ™a kada gona ta kwana É—an Mamman,

      : Gyado mai awon Æ™asa.

     

      Jagora: Yarinya za ta kai hura daji,

      : Tad dace da Dugumi,

      : Tac ce Aikau irin gidan Mamman,

      : Aikau ba ka dariya!

        ‘Y/Amshi: Yac ce bari don kak ki sa ni in dara,

      : In watce maku maza!

    : Ya riƙa noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Tac ce Aikau ba ka dariya,

      : Arne ko diddigin da munka iya,

      : Ban ce ka iya shi ba,

      : Arne ko kwarmaton da munka iya,

      : Ban ce ka iya shi ba,

      : Aikau ko jangirad da munka iya,

      : Ban ce ka iya shi ba,

      : Koko Aikau ba ka da gira?

       ‘Y/Amshi: Yana da giratai rashin kulawa ne,

      : Bai koma ma kanku ba.

    : Ya riƙa noma,

      : Da gaskiya na Bakwai,

    : Bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

      Jagora: Ai yau da ka ja wan Bakwai ga noma,

       ‘Y/Amshi: Ƙara ka dace da Æ™addara,

    : Ta hana maka halin zuwa gida.

     

      Jagora: Ai yau da ka ja wan Bakwai ga noma,

       ‘Y/Amshi: Ƙara ka hau goriba ka hwaÉ—i ka suma,

    : A hesa maka ruwa,

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      : Na Bakwai bai saba da zama,

      : Aikau jikan Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

      Jagora: Ni dai aikau yadda nig ganai,

    : Ya yi tabi’a[7] bakwai hwara,

       ‘Y/Amshi: Kuma ya yi tabi’a bakwai baÆ™a.x2

     

      Jagora: Tabi’a Aikau hwara guda,

    : Ya kira ka ya miƙa maka tuwo,

       ‘Y/Amshi: In kac ci ya miÆ™a maka hura.

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      : Na bakwai bai saba zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kukelin hwashin Æ™asa.

     

     Jagora: Tabi’ar Aikau hwara guda,

    : Ya kira ka ya É—amra[8] maka hatsi.

      ‘Y/Amshi: Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      : Na bakwai bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Tabi’ar Aikau hwara guda sawo maka,

      : Doki kana hawa,

      ‘Y/Amshi: Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      : Na bakwai bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Tabi’ar Aikau hwara guda,

    : Ya zuba maka kubta kana ƙawa.

    : Tabi’ar Aikau hwara guda,

    : Ya gama ka da kuÉ—in kashi kuma.

    : Tabi’ar Aikau hwara guda,

      ‘Y/Amshi: Anne ba ka san yi da ba da wani.

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya,

     : Na bakwai bai saba ba da zama,

      : Aikau jikan Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen  hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Tabi’ar Aikau baÆ™a guda,

    : Ya sakamma su tsutsa ga karkara,

     ‘Y/Amshi: Ta kashe musu shikka suna gani,

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      ; Na bakwai bai saba ba da zama,

      : Aikau jikin Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

     Jagora: Tabi’ar Aikau baÆ™a guda,

    : Ya sakam maka ciwon barin gida,

      ‘Y/Amshi: Kuma ba ka biÉ—a kai ta dawara[9].

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      ; Na bakwai bai saba da zama,

      : Aikau jikan Tayawo É—an Maman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Tabi’ar Aikau baÆ™a guda,

       : Ya sakam maka ciwo ga damana,

     ‘Y/Amshi: Kowa na daji kana gida,

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya, ,

      : Na bakwai bai saba da zama, ,

      : Aikau jikan Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

    Jagora: Tabi’ar Aikau baÆ™a guda,

    : Ya kira ka ya nuna ga aljana,

    ‘Y/Amshi: Ta riÆ™e ka ta tsotce maka jini,

     

         Jagora: Tabi’ar Aikau baÆ™a gudu,

      : Dab baya garai baya dibuwa.

    ‘Y/Amshi: In kad dubai kai ta dunduni[10],

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      : Aikau jikan Tayawo É—an Mamman,

      : Kunkelen hwashin Æ™asa.

     

         Jagora: Kyawon yaro ya auri yarinya,

      : Shi ak kyau hakanga dai.

    : Kyawon yaro shi auri yarinya,

    : Ga kyawonta ga hali.

    : Kyawon yaro ya auri yarinya,

    : Ga kyawo da natsuwa,

    ; Kuma dus sadda yas shigo É—akin,

    : Ta zanna mashi gado.

    : Kuma dus sadda tag ganai É—akin,

    : Ga shanya tana yi mai,

    : Sai ta yi ban hihhike[11],

    : Ta kyabta idonta,

    : Ta É—auka mashi  gira.

    : In wani wayau gareshi ta anshe,

    : Rannan bashi da shiya,

    ; Sai ka ga yaro shina rawa da haɓa,

    : Ta hyaÉ—a shi ga gado.

    : Ba ta bari nai hita cikin É—akin,

    : Sai ta ƙoshi da shiya,

    : To ko ta bashshi ya hito É—akin,

    : Ba shawad da zai gani.

     ‘Y/Amshi: Ai duw wata shawa tana cikin,

      : ÆŠakin dawo wa yakai maza.

      : Ya riÆ™a noma da gaskiya,

      : Na bakwai bai saba ba da zama,

    : Aikau jikan  Tayawo É—an Mamman,

    : Kunkelen hwashin ƙasa.

     

         Jagora: Kyawon yaro ya auri yarinya,

      : Shi ak kyau hakanga dai,

     ‘Y/Amshi: Baran wani ya kwashi raÆ™umad daji,

      : Bai gane ma kanta ba,

      : Ba ta da kyau,

    : Ta kare ga kunkuru,

      : Ga Æ™aton ciki kuma.



    [1]  Ƙato mai Æ™arfi

    [2]  Wata dabba ce mai haÆ™ora zage-zage, mai tonon Æ™asa da haÆ™oransa ya shige da sauri idan an koro shi za a kama shi.

    [3]  Wata dabba ce mai tonon rame da sauri.

    [4]  Wata dabba ce mai haÆ™ora zago-zago, wanda yake amfani das u wajen tonon rami idan an biyo shi sai ya shige cikin Æ™asa.

    [5]  Sanke, wasu itace da ake gittawa a garke don kar shanu su fita.

    [6]  Wata dabba ce mai tonon rame da sauri.

    [7]  ÆŠabi’a.

    [8]  Ya baka kyautar hatsi.

    [9]  Tafiya a ruÉ—e wadda mutum bai sai inda ya nufa ba.

    [10]  Makanta ko rashin gani sosai

    [11]  Jan hankalin don tayar da sha’awar saduwa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.