Ticker

Aikin Ganin Annabi

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Aikin Ganin Annabi

Ya bismilla zamu roƙo ga Ubangiji,

Annabi ya Rasulu mai ceto lahira.

Jahillai ka tambaya wai mu gaya masu,

Wani aikin sa a samu ganin Annabi.

Shi aikin ganin Muhammadu da yawa yake,

Kai azumi ka fidda zakka ka rage faɗa,

Ka rage bin san maƙwabci da itatuwa,

Ranar lahira makwabcinka zumunka ne,

Ko nan duniya maƙwabcinka zumunka ne,

Jirgi ɗan Amina alkawarin duniya.

Macce tana gidan miji ba ta zama kurum,

Ta laga ɗan gyale tana yawon duniya,

Yau ga duniyag ga mai ɓadda ɗiyan Adam,

Jirgi ɗan Amina alkawarin duniya.

Jariri da hurhura ga shi yana gudu,

Kowane dudduge yana fidda wuta tasa.


Post a Comment

0 Comments