Aikin Ganin Annabi

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Aikin Ganin Annabi

    Ya bismilla zamu roƙo ga Ubangiji,

    Annabi ya Rasulu mai ceto lahira.

    Jahillai ka tambaya wai mu gaya masu,

    Wani aikin sa a samu ganin Annabi.

    Shi aikin ganin Muhammadu da yawa yake,

    Kai azumi ka fidda zakka ka rage faÉ—a,

    Ka rage bin san maƙwabci da itatuwa,

    Ranar lahira makwabcinka zumunka ne,

    Ko nan duniya maƙwabcinka zumunka ne,

    Jirgi É—an Amina alkawarin duniya.

    Macce tana gidan miji ba ta zama kurum,

    Ta laga É—an gyale tana yawon duniya,

    Yau ga duniyag ga mai É“adda É—iyan Adam,

    Jirgi É—an Amina alkawarin duniya.

    Jariri da hurhura ga shi yana gudu,

    Kowane dudduge yana fidda wuta tasa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.