Ticker

Dajimma Gojen Mutanen Raha

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ɗajimma Gojen Mutanen Raha

 

G/Waƙa: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen[1] mutanen Raha.

 

Jagora: Arna da kaka kuna shan giya.

‘Y/ Amshi: Sai da rani ku ce baku ƙaunag giya.

 

Jagora: To arna da kaka[2] kuna shan giya.

‘Y/ Amshi: Sai da rani ku ce baku ƙaunar giya.

 

Jagora: A to arne ka gaji dogon hatsi.

‘Y/ Amshi: To ba a ba ka bindi ba daka riƙe.

 

Jagora: A to kasan kowaɗ ɗau watsiyar dubu.

‘Y/ Amshi: To da gero da dawa cikawa yakai.

Jagora: To yi man gafara.

‘Y/ Amshi: Ce ma Ɗanjimma Goje wucewa ni kai,

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Goje mutanen Raha.

 

Jagora: Ka ga duk hankalin mai kiɗi ya wuce.

‘Y/ Amshi: To ba’a bashi dokin kiɗi ya ciba.

 

Jagora: To arna da kaka kuna shan giya.

‘Y/ Amshi: To ga rani kunce baku ƙaunar giya.

 

Jagora: Giwa na ɗebe wake na ɗebe maiwa,

: Da kalgo da ƙirya zahewa yakai.

‘Y/ Amshi: In ka kai garai inga sayyu sama,

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Goje gayya da kai ba’ayin gargare.

‘Y/ Amshi: To wuce taka kuyya wucewa a kai.

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Ku ce masa in da doki kiɗawa nikai.

‘Y/ Amshi : In kuma babu doki  ina mai kiɗi.

 

Jagora: Ku ce masa in da samu ina mai kiɗi

‘Y/ Amshi: In babu samu kiɗawa nikai.

 

Jagora: Kai kuji an ba ka ruwan hwarau-hwarau[3].

‘Y/ Amshi: Wai ya hambare baya shan ɗarwaye,

: To bari ko abincin rasawa yakai,

: Ya kama aiki gamawa ya kai.

 

Jagora: Alkali Sa’idu Allah riƙama riƙo,

: Alkali Sa’idu Allah riƙama riƙo.

‘Y/ Amshi: Alkali Sa’idu Allah riƙama riƙo.

 

Jagora: In dai na roƙi Allah jiyawa shikai

‘Y/ Amshi: In dai na roƙi Allah jiyawa shikai

 

Jagora: Alkali Sa’idu Allah riƙama .

‘Y/ Amshi: Alkali Sa’idu Allah riƙama shikai.

 

Jagora: Da Kwando da Kwando  ana gardama.

‘Y/ Amshi: Yanzu Kwando guda na zuwa lahira,

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: To arna da kaka kuna shan giya.

‘Y/ Amshi: Sai da rani ku ce ba ku ƙaunar giya.

 

Jagora: A to arne ka gaji dubun hatci.

‘Y/ Amshi: To ba’a ba ka bindi ba da ka riƙe.

 

Jagora: Tunda ko Ɗan mu’abban Raha ya hwaɗi.

‘Y/ Amshi: Taka ka hau[4] zai shirin sai mani.

:: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Nagode Bude mai bindiga.

‘Y/ Amshi: Bude girma ya ƙara ka ban rammaka.

 

Jagora: Inda duk yag ga nama bigewa yakai.

‘Y/ Amshi: Inda duk yag ga nama bigewa yakai,

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Kaga banza ibadar mutan Ɗan ali,

: Duk dai ibadar biri ce su kai.

‘Y/ Amshi: Wanda yat tashi sallah da walki yakai,

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Daudun kurya muna shawara,

: Dauri dai kace ba ka son Ɗan ali,

: Yi hushi dasu basu yin ko kwabo,

: Jikan Shehun duk bai riƙon Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: To kuzan dai da iya mutan Ɗan ali.

 

Jagora: To da tciya da raga.

‘Y/ Amshi: Suna Ɗan ali.

 

Jagora: To kuma cin amana.

‘Y/ Amshi: Tana Ɗan ali.

 

Jagora: Duk da baƙin talauci.

‘Y/ Amshi: Yana Ɗan'ali.

 

Jagora: Ka ga rashin ragowa.

‘Y/ Amshi : Yana Ɗan ali.

 

Jagora: Duk dai kazaƙ ƙwarai ba ta yin gurdumu.

‘Y/ Amshi : Maccen ƙwarai ba ta yi Ɗan ali,

: Tunda matansu ɗibar miya dai sukai,

: Ji man kutolon[5] maɗebin miya,

: Ka samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Kafirawa mutan Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: Don kun buwai Shehu Dan Hodiyo,

: Ko ni buwayar kiɗi na ku kai.

 

Jagora: Duk wanda yat taka kashin mutan Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: To sai ya yi cibi ga babba kafa,

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Allahu kullun ta roƙo nikai,

: Allahu kullun jiya man ya kai.

‘Y/ Amshi: To Ka hisshe mu sherin mutan Ɗan ali,

 

Jagora: Allah sarki.

‘Y/ Amshi: Ka hisshe mu sherin mutan Ɗan ali,

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: To ku jama’a ina Bagudun Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: Babban mutum bai shigewa duhu,

: To da hannu kamar mai kiɗin kuntugi,

: Ya samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Sarkin fawan mutan Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: Baki nai kamar mai kiɗin kuntugi.

 

Jagora: Sun fara shegen halin Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: Don ga ibin mai kiwo ya mutu,

: Bawa har sun ka ƙwace kwabo nai takwas.

: Ya samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Ɗan gigala za muna Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: To wallahi ya bar zuwa Ɗan ali.

Jagora:  Bawa taho da kai zamu na Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: To wallahi ya bar zuwa Ɗan ali.

 

Jagora : Iro taho da kai zamu na Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: To wallahi ya bar zuwa Ɗan ali.

 

 Jagora: Kai Mudi da kai zamu na Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: To wallahi ya bar zuwa Ɗan ali.

 

Jagora: Ku ‘yan kallo ina mai zuwa Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: Ɗan ali inda Allan matcata[6] yake.

: Ya samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Allah in dai da ni zaka yin shawara.

‘Y/ Amshi: Haliƙu ko ruwa ba a yi Ɗan ali.

 

Jagora: Allah in dai da ni zaka yin shawara.

‘Y/ Amshi: Haliƙu ko ruwa ba ka yi Ɗan ali,

: Ko sun yi shuka macewa ta kai,

: Jalla ko haihuwa ba a yi Ɗan ali.

: Ya samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Arna da kaka kuna shan giya.

‘Y/ Amshi: Sai da rani ku ce baku ƙaunar giya.

 

Jagora: Kowa ya ce man hwaɗa yaz zaka.

‘Y/ Amshi: Kowa ya ce man hwaɗa yaz zaka.

 

Jagora: Kowa ya ce man hwaɗa yaz zaka.

‘Y/ Amshi: To hadda Landan da bakin bahar.

 

Jagora: Rantse da Allah bugawa ka kai.

‘Y/ Amshi: Kai ko rantse da Allah fada kaz zaka.

 

Jagora: Sarkin askin mutan Ɗan ali,

: Kullun ya ce man hwaɗa yaz zaka.

‘Y/ Amshi: To wane har ga Allah bugawa ya kai.

 

 Jagora: Ko Garba ƙato nufi nai mu kai.

‘Y/ Amshi: To shi ah wakilin maɗeban miya.

: Ya samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Kai ina Garba dogo ina Ɗan Kudum,

‘Y/ Amshi: Kai taho ban ka sha ga dawo ya zaka.

: Ya samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Arna ga kaka kuna shan giya.

‘Y/ Amshi: Sai ga rani ku ce baku ƙaunar giya,

: Ya samu aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.

 

Jagora: Kai ku ji godabe[7] ya biya Ɗan ali,

: An ko yi hanyar shiga Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: Na ɓata da sarkin tashar Ɗan ali.

 

Jagora: Ni na ɓata da sarkin tashar Ɗan ali.

‘Y/ Amshi: Ni na ɓata da sarkin tashar Ɗan ali.

 

Jagora: Kun san wanceni sarkin tasha ya mutu.

‘Y/ Amshi: Yanzu an sake sarkin tasha Ɗan ali.

 

Jagora: Kun san wanceni[8] sarkin tasha ya mutu.

‘Y/ Amshi: Yanzu an sake sarkin tasha Ɗan ali.

 

Jagora: Inda ni iske sarkin tasha Ɗan ali.

: Da hannu ga munta yana ƙwalƙwala.

‘Y/ Amshi: Ko da ya hwalka tusa tashar ta hwashe.

: Ya kama aiki gamawa yakai,

: Ɗanjimma Gojen mutanen Raha.



[1]  Babban manomi mai noma abin aiki da hannunsa.

[2]  Lokacin da aka fara ɗebe kayan amfanin gona.

[3]  Ruwan da aka zuba wa fura don ƙari kasha ƙisa, Farau-farau.

[4]  Doki tare da sirdinsa, wanda iyakar mutum hawa ba tare da wata wahala ba.

[5]  Ƙugu/kwankwaso/kunkuru.

[6]  Matsyata wato mutanen dab a su da arziki.

[7]  Titin mota.

[8]  Kamar mutun y ace wancan.

Post a Comment

0 Comments