𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Na yi tsarin iyali ne. Sai a
watan farko na ga al’adata, a wata na biyu kuma ban yi ba. Daga baya kuma sai
ga jini har kwanaki huɗu, to
yaya matsayin sallah da azumi?
Ni matar aure ce, ina yin haila kwana shida. Amma
da na haihu kuma na je aka yi mini tsarin iyali, sai jinin ya koma kwanaki
ashirin! To zan iya cigaba da ibada da mu’amalar aure ko sai bayan jinin ya ɗauke?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Gudun aukuwar irin waɗannan matsalolin ya sa malamai suka ƙyamaci
bin irin waɗannan
hanyoyin na zamani don tsarin iyali in dai ba da wata larura mai ƙarfi
ba, kamar yadda muka yi bayani a cikin amsar tambayar da ta gabata akan kayyade
haihuwa.
Amma a kan wannan matsalar sai a ce: Jinin da ke
fitowa ga mata nau’i uku ne: Haila da Nifasi da Istihaala.
(1) Haila jinin da ya zo ne haka nan kawai ba da
wani dalili na rashin lafiya ba, sannan kuma da kansa yake fitowa a lokacinsa,
ba janyo shi ake yi ba.
(2) Nifasi kuwa shi ne wanda ya zo saboda dalilin
haihuwa.
(3) Istihaala kuwa shi ne wanda ya auku saboda
rashin lafiya, ko jin ciwo a cikin wata jijiyar mahaifa, da sani ko ba da sanin
macen ba.
Don haka, duk jinin da aka tabbatar ba haila ba ne
kuma ba nifasi ba ne, to babu abin da ya rage sai dai a ba shi matsayin
istihaala kawai.
Istihaala dai ba ya hana abubuwan da haila da
Nifasi suke hanawa na sallah da azumi da mu’amalar tarayya a tsakanin
ma’aurata.
Allaah ya ƙara mana fahimta.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.