Ticker

Alkali Musa

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Alƙali Musa

A garin Gidan Rijiya Alkali Musa yake, wajen Batamna ta Galadi a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Shi ba alƙalin kotu ne ba mai shari’a, alƙali ne na ƙungiyar manoma. Yana noma kwarai da gaske kuma ya yi wa Amali kyauta sosai don haka ya yi masa wakar.

G/Waƙa : Koma gona,

   : A gaishe ka,

: Alkali Musa,

   : Komi nika so,

: Ga Musa,

   : Ya na nan an sai man.

 

   Jagora: Yau mi nika jikara? x2

   :Tunda ga Musa dai-dai.

   ‘Y/Amshi: Yau mi nika jikara[1]?

   :Tunda ga Musa dai-dai.

 

   Jagora: Jikan Ladan,

   : Mazan dangana gona Musa,

    ‘Y/Amshi: Musa a shige ga gona,

   : Ana murzak[2] kuyye,

: Koma gona,

   : A gaishe ka,

: Alkali Musa,

   : Komi nika so,

: Ga Musa,

   : Ya na miƙo man shi.

 

   Jagora: Doki nike so ga Musa, x2

   : Shina nan ya sai man,

   : In dai ga shi nan ga hili,

   : A ce shi yab basai,

   : Ni gak ka nuhwan da,

    ‘Y/Amshi: Kuɗin kashi,

   : Na bar masu,

: Koma gona,

: A gaishe ka alkali Musa,

: Komi nika so ga Musa,

: Ya na miƙo man shi.

 

   Jagora: Rana ta hwaɗi bai hwasa,

: Gabcen[3] kuyye ba,

: Raɓa ta jiɗa[4],

: Duk ta jike mai baya nai,

: Rana ta ɓaɓɓako dag gabas,

  : Ta cinno mai,

: Rana ta ci ka tasa ka yin ƙarkin baya,

    ‘Y/Amshi: Bai san gajiya ga gona ba,

   : Dunga sai swahe,

   : Koma gona,

   : A gaishe ka alkali Musa,

   : Komi ni ka so ga Musa,

   : Ya na miƙo man shi.

 

   Jagora: Rana ta hwaɗi bai hwasa,

: Horon kuyyai ba,

: Raɓa da jida dutta jiƙe,

: Mai baya nai,

: Rana ta ɓaɓɓako da gabas,

: Ta cinnomai,

: Rana ta cika ta saka yin,

: Ƙarhin baya,

    ‘Y/Amshi: Bai san gajiya ga gona ba,

   : Dunga[5] sai swahe[6],

   : Koma gona,

: A gaisheka alkali Musa,

: Komi ni ka so ga Musa,

: Yana miƙo man shi,

 

   Jagora: Ko yanzu Amali nib bar kiɗi,

: Komi ya yi,

: In na mutu ka kuce man,

: Mutane sun ɓassan[7],

: Na shedi karen gida,

: Ba ya wa kura komi,

: Shi mai sama tunda ya,

: San iyakak kwana na,

: Kuma ba ya rage su ko ya,

: Yi zwari[8] bai rage su sai na kai,

    ‘Y/Amshi: In na mutu ban da sauran,

   : Zuwa garkar kowa,

   : Koma gona,

   : A gaishe ka alkali Musa,

   : Komi nika so ga Musa,

: Yana miƙo man shi.

 

   Jagora: Randa dut ni mutu banda,

: Sauran kiɗi garkar kar kowa,

    ‘Y/Amshi: Koma gona,

  : A gaishe ka alkali Musa,

   : Komi ni ka so ga Musa,

: Yana miƙo man shi.



[1]  Shakku/kokwanto.

[2]  Noma

[3]  Noma na duƙe

[4]  Sauka.

[5]  Cigaba.

[6]  Safe.

[7]  Kashewa.

[8]  Haɗama

Post a Comment

0 Comments