Alamci

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Alamci

    Salon alamci shi ne inda mawaƙi zai ambaci wani abu da nufin ya wakilci wani abu da bai ambaci sunansa ba, amma ya kasance mutane suna sane da wakilcin. Misali kamar naɗi a matsayin sarauta. Dumfawa, (2002).

    Alamci dabara ce ta bayyana wani abu ta hanyar ba shi wata alama wadda za ta tsaya a maimakonsa. ÆŠangambo, (2007)

    Wato ke nan Idan mawaƙi ya bayyana wani abu ta hanyar ambaton wata kalma ko wani zance da za a iya hango abin da yake nufi ta dubin kalamin ko kalmar, to ana kiran wannan salo alamtarwa. Misali:

     Jagora: Kanta Æ™waÆ™wal, Æ™waÆ™wal Æ™waÆ™wal babu gashi,

     Amshi: To

     Jagora: Ko guiwar amali ta fi shi manga.

     (WaÆ™ar Ƙazama : Inno mai bara Sabuwar hanya)

    Manga wani nau’in gyaran gashi ne na gargajiya da mafi yawa mata masu yalwar gashin kai ke yi. A É—an waÆ™ar da ya gabata mawaÆ™in na cewa gwiwar amalin raÆ™umi ta fi kan mace Æ™azama gashi. Sai dai a maimakon ya kira sunan gashi sai ya kira sunan wani abu da sai da gashi ake iya yinsa ya danganta shi ga gwiwar raÆ™umi. Wato ke nan kalmar ‘manga’ alamci ne na gashi wanda gwiwar amalin raÆ™umi ta É—ara kan Æ™azamar mace da shi.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.