Ticker

Alasan Danreto Kanoma

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Alasan Ɗanreto Kanoma

 

G/ Waƙa: Mai rabo ga Allah,

: Sai tai duhu ya dawo daji.x2

 

Jagora: Alhaji Alasan Ɗanreto,

: Alhaji Alasan na Kanoma,

: Bata kalami mai abin mamaki,

: Rana mai raba ma kowa aiki,

: Alhaji ai ko ta gobe sai ta watce,

: Ai kartau bada gumba ka biya bashi,

: Alhaji jikan magaji ga ranakka,

 

Jagora: Alhaji mai kyauta kamab biyan albashi,

: Kowa ka ‘yamma saw guda ya samu,

: Ai duy yawan Kanoma babu kamak ka,

: Alhaji ka biya ni ka biya bashi,

: Alhaji Alasan Ɗanreto,

: Mutane am ba ka san,

  : Mai nuhway ya ba ka ba jiddun,

: Sai dai rad da Rabbana yab bashi,

: Ka ga kana gida ya tai ya kirai ka,

: Mijin Mairi ka biya ka kyauta,

: Rana mai raba ma kowa aiki,

: Na gaishe ka kandami sha ɗiba,

: Ai Alhaji Alasan yazan kuwara[1]

: Ya hi kwadarko,

: Ni kulu jirgin abara ɗai ka rigat ta,

 

Jagora : Amma maza ku maida gasa ƙarya,

: Ai hannu bai aje ba mi zai bai wa,

: Don haka kui nomada gaskiya,

: Kai maza kui nomada gaskiya,

: Ai noman adashe in kun gane,

: Alhaji Maiyara ya biya ya kyauta,

: Ai Alhaji Maiyara ya biya ya kyauta,

: Ai Sule boka ya biya ni dai na gode,

: Alhaji Ɗanbara akwai ranak ka,

: Malan jikan kaba akwai ranak ka,

: Ai ko Goje ya biya na gode,

: Na gode Musa boka,

: Tabaraka Allah ya baku gobe ku  ba ni.

 

 Jagora: Ai Garba direba,

: Ai direban Alhaji,

: Ai Garba hag gida yak kai ni,

: Alhaji ya  ba ni buhun gero,

: Ya  ba ni buhun dawa,

: Ai ya  ba ni hwan ɗari na amsa,

: Ko masu roƙona ka gane ya cece su,

: Su ma ya basu hwan ɗari sun amshe,

: Alhaji gagara gasa,

: Ai jama’a mai hushi da Allah wawa,

: Ai Tutal mulki mai gamammen aiki,

: Mai rabo da hiyayya[2],

: Lillahi ya riga ya ba ka Alasan,

: To a ci saura da lahiya na gode,

: Roƙo cinikin kasawa,

: Abin da ba a wa kasasshe.



[1]  Babbar madatsar ruwa kamar teku.

[2]  Fifita wani a kan wani.

Post a Comment

0 Comments