Alhaji Labaran Baban Musa

    Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Alhaji Labaran Baban Musa

    G/ Waƙa: Ai irin jibo dan tsula Labaran baban Musa,

    : Su Alhaji Labbo ciwon cikin ‘yan sarki.

     

     Jagora:  Ai yaka sakwati ai yaka toron giwa,

    : Yaka sakwati ai yaka baban Musa,

    : Babban Sa’adatu Labbo,

    : Ya wa manoma nisa,

    : Ita hanyar Bena ko wabbi daidai gandu,

    : Ko mutum bai son Labbo,

    : Ai ba ya ce mai raggo,

    : Ban hana dai shi duÉ—e idanunai ba,

    : Ai zaman ijiyam mutum,

    : Na gwada mai haushi,

    : In taga abinda hat bai iyawa an yi,

    : Labbo in dai ya tai ga aiki gabakin gona,

    : Hau wata addu’a ta ya kai in ya zo,

    : Sai ya ce hatta tatiya humul bayyanatu,

    : Wajen bayyanan nomanai,

    : Waman yaƙanut kuma da kalme

    : Na tonon laka.

     

    Jagora : Aiki Æ™aro darajja ma’aikin sarki,

    : Addu’ar zurÆ™allaini ta yaj jiya yab bam mai,

    : Bayan zurƙalaini su am manoman farko,

    : Ai manomin duka duni....

    : Ya bai yi tamkatai ba,

    : Dole ka dole ko dole baban Musa,

    : Labbo ubanka cilas a ce mai sarki,

    : Kuma kakanka cilas a ce mai sarki,

    : Tun da dai lardin Bauchi

    : Duk ba a yi tamkatai ba,

    : Ai sama dagga gidanka

    : Mamman kana sauna tai.

     

    Jagora: Wanda duk ba ya da gaskiya,

    : Ba ya jin daÉ—i nai,

    : Mamman bai sai da iko jiran kuÉ—É—i ba,

    : Sanda na gwamatse Sanda toron gwari,

    : Ai Sanda na gwamatse

    : Ka yi gaba Bauchi,

    : Katsina ta Dikko,

    : Ta samu shedun girma,

    : Daga Labbo na zaya zaɓa Bauchi,

    : Tunda dai Hillanci[1],

    : Ina za ya ƙin Katsinanci,

    : Shi Katsinanci,

    : Ina zaya ƙin Hillanci,

    : Ai gidan tara ne goma,

    : Sai ta ishe ta kwana.

     

    Jagora: Ya ka sakwati ai yaka toron giwa,

    : Mai kyau bashi toshi ga matar arme,

    : Ai É—iya ka gani nai,

    : Ta ƙalge[2] ta ce ai sai shi,

    : Uwa da ubanta duk ba su cewa komi,

    : Ko sun ce ƙala duk bata dangin banza,

    : Ai mu yanka sadaki,

    : Da kowa kason armenai,

    : Ga kaɓaki ruwayye ka na kallon nai,

    : Kul badaÉ—e Labbo sai an naÉ—a ma sarki,

    : Mijin hajiya Amina,

    : Gaishe ka toron giwa,

    : Mijin hajiya Tele,

    : Ciwon cikin ‘yan sarki,

    :Ya ka sakwati kai yaka toron giwa,

    : Daga bana Haruna ka wa manoma nisa.

     

     Jagora: Ai Labbo ubanka cilas a ce mai sarki,

    : Kuma kakanka cilas a ce mai sarki,

    : Alhaji malan Isah a ciyaman alhazzai,

    : Ai babban wa,

    : Kamad dai mahaihi yaz zan,

    : Malam ya taimakai don ka toron giwa,

    : Allah dai ya cece shi domin na ci,

    : Baban Asma’u ciwon cikin ‘yan sarki,

    : Ai baban Binta ‘yan haihuwat tsohonai,

    : Ba duka É—a ka gadon uwaye nai ba,

    : Ai zalangaÉ—e[3] wane,

    : Kam ya yi ba daidai ba.

    Jagora: To ina jaka ku da jaki ma ci karmami,

    : Ina dan tara tsuhu jaki matsagi jaka,

    : Wanda duk dai ma uwasshi dai bai sanin hali nai,

    : Ni da nis san halinshi É—ibat tsumata niy yi,

    : Ban É—aga hunnunmu ko da ya na tsingilla[4].

     

    Jagora : In dai ya É—illan in zuba mai kashi,

    : Irin jaki da É—ai sai da wannan hali,

    : Alhaji Ahmad, ya taimaka don dogo,

    : Alhaji Sulaiman, ya taimaka don dogo,

    : Alhaji Isan Isa, ya taimaka don dogo,

    : Alhaji Sanin Ayyu, ya taimaka don dogo,

    : Ai Musa na Biba ya taimaka don dogo,

    : Allah dai ya cece ku domin na ci.



    [1]  Fulatanci.

    [2]  Hawan wani ra’ayi ka mayar das hi naka.

    [3] Tana sifantawa ne wato tana nufin mutum dogo musamman wanda bai san ciwon kansa ba-baya noma.

    [4]  Tsalle-tsalle. Tafiya ana soka Æ™afa ana gurgunta wajen tafiya. 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.