Alhaji Na’allah Na Janbaƙo

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Alhaji Na’allah Na Janbaƙo

G/Waƙa: Bai yadda da wargin banza ba

: Mu ga Alhaji jikan Amadu.

  Jagora: Mai galma ya tahi gonatai

: Alhaji ya saba da ya duƙa sai duhu.

‘Y/ Amshi: Mai galma ya tahi gonatai

: Alhaji ya saba da ya duƙa sai duhu.

 

Jagora: Alhaji Na’alla na Janbaƙo.x2

‘Y/ Amshi: Giwa ke katce tarko ke wuce.x2

: Bai yadda da wargin banza ba

: Mu ga Alhaji jikan Amadu.

 

Jagora: Giwa mu ga Alhaji jikan Amadu

‘Y/ Amshi: Sai na zo mu ga Alhaji ɗauka ta yakai.

 

Jagora: Ka sawo mani fanda[1] Alhaji

‘Y/ Amshi: Kar ‘yan yara su tcere man ƙasa.

.

Jagora: Ka  ba ni kujera[2]

‘Y/ Amshi: Alhaji in hau arhwa[3] mu zauna lahiya.

: Bai yadda da wargin banza ba

: Mu ga Alhaji jikan Amadu.

 

Jagora: Koni maza ku ta noma,x2

‘Y/ Amshi: Ba a zama in ba a da damma an kaɗe.x2

 

Jagora: Kowas samu abinci, yaƙ ƙi ci, x2

: Yaz zan ba mai kyauta ne ba,

‘Y/ Amshi: Bari Ummaru ɓaci[4] nai mukai.x2

: Bai yadda da wargin banza ba

: Mu ga Alhaji jikan Amadu.

 

Jagora: Mai galma ya tahi  gonatai.x2

‘Y/ Amshi: Mai galma ya tahi  gonatai,x2

: Ya saba da ya duƙa sai duhu,

 

  Jagora: Ladan Gilbaɗi ban rena ma ba.

‘Y/ Amshi: Allah ya zuba mai albarka,

 

Jagora: Ladan Gilbaɗi na halin girma.

‘Y/ Amshi: Allah ya zuba mai albarka,

: Ya raba ka da sherin duniya.

 

Jagora: Allah ya raba ka da sherin duniya.

‘Y/ Amshi: Ya Allah ya raba ka da sherin duniya.

: Bai yadda da wargin banza ba

: Mu ga Alhaji jikan Amadu.

 

Jagora: Malam Abdulkarimu ban rena ma ba.

‘Y/ Amshi: Allah ya zuba mai albarka,

: Ya raba ka da sherin duniya.

.: Bai yadda da wargin banza ba

: Mu ga Alhaji jikan Amadu.

 

Jagora: Giwa mu ga Alhaji jikan Amadu.

‘Y/ Amshi: Sai na zo mu ga Alhaji ɗauka ta yakai.

 

Jagora: Ku taho kui kallon gero.

‘Y/ Amshi: Nan Janbaƙo ga jikan Amadu.

Jagora: Ku taho kui kallon dawa

‘Y/ Amshi: Nan Janbaƙo ga jikan Amadu.

.

Jagora: Ku taho mui kallon maiwa.

‘Y/ Amshi: Nan Janbaƙo ga jikan Amadu.

 

Jagora: A taho ai kallon kuɗɗi,

‘Y/ Amshi: Nan Janbaƙo ga jikan Amadu.

 

Jagora: Ku taho kui kallon iko,

‘Y/ Amshi: Nan Janbaƙo ga jikan Amadu

 

Jagora: A taho ai kallon ilmi

‘Y/ Amshi: Nan Janbaƙo ga jikan Amadu.

 

Jagora: Ba kwaramniya[5] ga daka ba.x2

‘Y/ Amshi: Ashe ‘yanyara jidali ɗai sukai.x2

 

Jagora: Na taho Mafara local gammen.

‘Y/ Amshi: Mun lura da manyan ma’aikata.

: Sun yadda da jikan Amadu.

 

Jagora: Na zo Gusau na yo wasa,

‘Y/ Amshi: Mun lura da manyan ma’aikata.

: Sun yadda da jikan Amadu.

 

Jagora: Na zo Legas na yo wasa

‘Y/ Amshi: Mun lura da manyan ma’aikata.

: Sun yadda da jikan Amadu.

 

Jagora: Na zo Sakkwato na yo wasa,

‘Y/ Amshi: Mun lura da manyan ma’aikata.

: Sun yadda da jikan Amadu.

 

Jagora: Irin wada kaz zama….x2

‘Y/ Amshi: Zaki duniya sai ka zama zaki lahira.x2

  Jagora: In bancin jikan Amadu.x2

‘Y/ Amshi: Da an muzanta gari mai fa’ida.x2

 

Jagora: Janbaƙo akwai kuɗɗi ciki.

: Janbaƙo akwai shanun noma

: Janbaƙo akwai gero ciki

: Mota ashirin ce sabuwa

‘Y/ Amshi: Mota ashirin ce sabuwa.

: Biyu gasu ga jikan Amadu.

 

Jagora: Mota ashirin ce sabuwa

‘Y/ Amshi: Ashirin ce sabuwa.

: Biyu gasu ga jikan Amadu.

: Bai yadda da wargin banza ba

: Mu ga Alhaji jika Amadu.

 

Jagora: Mai ja ma yanzu ga aiki ya bari

‘Y/ Amshi: Mai ja ma yanzu ga aiki ya bari.



[1]  Babur/Kwaɗa mai mari/Honda.

[2]  Biyan kujerar aikin hajji.

[3]  Arafat.

[4]  Zagi.

[5]  Rawar jiki/karauniya.


Post a Comment

0 Comments