Ticker

Alhaji Sani Mai Eka

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Alhaji Sani Mai Eka

 G/ Waƙa: Alhaji Sani mai Eka.

: Tambazarka ta ƙasar Gwadabawa.

 

 Jagora : Alhaji Sani da gaskiya yaka aiki nai daji.

: Ai bai kula da ruwa ba,

: Kuma bai tsoron rana.

: Ya dai yarda da Allah,

: Don Allah as sarki.

: Kuma ya yarda da aiki,

: Don aiki ak komi.

: Don Allah ɗiya maza ku yi aiki,

: Don aiki ya hi.

: Tunda ya riƙa dawa,

: Ya hi takaicin tsara[1].

: Alhaji Sani ban rena,

: Tangaza  ya biya ba shi,

: Ya kyauta yai komi,

: Alhaji Sani tambazarka ban rena,

: Sani ya biya bashi

: Ya kyauta yai komi.

 

Jagora: Allah dai ya taimake ka da hairan,

: Ya ƙara ma girma,

: A she maza wuya kuka shakka,

: Shi al laihin Noma,

: Ba don wuya ba ku gane,

: Mi allaihin Noma?

: Ka sha hurakka da Nono,

: Da nononta ta gero.

: Ka ci tuwunka da nama,

: Ga kuma mai an lemo.

: Ga rigakka ka watsa,

: Sannan ga kuɗɗi nan,

: Wagga ƙarhumhuma[2] kam na gane sai noma.

: Ɗankoli sha hurrakka ga buta,

: Kullum mai daɗi dai.

: Ai wa ka yo maka damu,

: Sai kai bakin gona.

 

Jagora : Minahikaz zumag ga,

: Ka gane na gane ai ni,

: A she ga buttami[3] ya ka rura,

: Zaƙi na can baya.

: Kai kusa mani kwaɗi[4],

: Ku ɗaura mai ɓuya,

: Bari in bi baya garai,

: In ɗebe mai zaƙi,

: Sa wutakka Yawuri,

: Sai sha na koma ya ci,

: Kasan Yawuri yaro,

: ba ka gane Geshe ba,

: Inji kulu – kulu dai ne,

 

Jagora : Ai da sanin wurin bugu aka ƙira,

: Ba aikin ƙarhi ba,

: Sauki ka sauki katanga,

: Na rena ma girma,

: Du wanda bai aiki,

: Kai ak katambiri Sauna,

: Kai sauna nai,

: Alhaji Sani,

:Alhaji Sani mai eka,

: Tambazarka ya biya bashi,

: Ya kyauta yai komi.

 

Jagora: Azuhuri ayi sallah,

: Ga aikin shi na gona,

: La’asari ya yi sallah,

: Ga aikinshi na gona.

: Mangariba ya yi sallah,

: Ga aikinshi na gona.

: Issha’i ta zaka zaki,

: Dud dai bai dawo ba.

 

Jagora : Sarkin noma sarkin lada,

: Alhaji Sani mai eka,

: Tambazarka,

: Kartau[5] bada gumau ba ka biya bashi,

: Ka kyauta kai komi,

: Alhaji Sani ai tambazar ƙauye,

: Ka kyauta kai komi,

: Halima dan dubu,

: Ai ‘yaddubu ta biya ba shi,

: Ta kyauta tai komi,

: Hajiya Hadiza ‘Yaddubu,

: ‘Yaddubu ta biya bashi,

: Ta kyauta tai komi.

 

Jagora: Mata da rabin wata mata,

: Ta kyuta tai komi,

: ‘Yaddubu ka san abun gado ne,

: ‘Yaddubu mai kyau,

: ‘Ya mace guda,

: A samo goma,

: Ke kyauta ke komi,

: Allah dai ya taimake mu da hairan,

: Ya ƙara ma girma.

 

Jagora: Sani nau,

: Sani mai biredi na Ɗaki takwas, x2

: Ai cikin maza nika sa Sani,

: Ai cikin manoma ka ke Sani,

: Ba ga birodi ɗai ya tsaya ba Mamman Sani,

: Hadda aikin ga na gona,

: Maza dai ku riƙa da gaskiya bisa aiki,

: Don aiki ya hi.

: Allah dai ya taimake ka da hairan,

: Ya ƙarama girma,

: Ai Badakkare,

: Ni ka dubi,

: Bobawan ga,

: Na Bauchi.

 

 Jagora : Ashe mutaru mu sha gari,

: Yas sa hannunai,

: Kasan mutaru,

: Mu gyara shi,

: Kwaki nai annan,

: Bari in kaishi ga Kwabre,

: Ya ɓata mai rani,

: Ko da ya bi ta geron nan yunwa ta girma.

: Allah dai ya taimake ka da hairan,

: Ya kara ma girma,

: Ai mamaki ya kamman,

: Alhaji Sani.

 

Jagora : Ai mai ekaTambazarka,

: Gwadabawa,

: Na kiɗa maka zaki,

: Don aikin yak kai nan.

: A gaida gagara gasa,

: Goge ɗauke molo,

: Ai ta mace ba ta da yaji,

: Na ganekke Sani,

: Ai mace na iya yawo,

: Macce na iya iko,

: Da yaronta na banza,

: Sai ta rungume shi ta goye,

: Ta goye dam - dam – dam,

 

Jagora: Sai a ganta goye,

: Da ɗanta da dubi shi,

: In ka ce mashi shege,

: Shari’a dai kajja,

: Alƙali aka kai ka,

: Ka zana mai suna,

: Ai burum ta ci burum,

: Fatima yau dai,

: Alhaji Sani, mai eka,

: Tambazarka tsanin Gwadabawa,

: Alhaji Sani da gaskiya ya ka aiki,

: Nai daji in ya tai,

: Tun da bai kula da ruwa ba,

: Kuma bai tsoron rana,

: Don Allah ɗiya maza ku yi aiki,

: Don aiki ad daidai,

: Ɗan da ya rasa dawa,

: Ya ji takaicin tsara,

: Ba same mashi dawa,

: Y a zan soson banza.

 

Jagora: Kai ak katambiri samna,

: Kai samnan as sunanka,

: Ai masu gari da ka iko,

: Sun zangaice noma,

: Tajirrai na sana’a,

: Sun zangaice noma,

: Malaman da ka ilimi,

: Sun zangaice noma,

: Masu garin da iko,

: Sun zangaice noma.

 

Jagora: Duk da Nasara Bature,

: Mai injin nerori,

: Ya gyare mana aiki,

: Ya gasgance noma.



[1]  Wanda ake ‘yan shekara guda wato sa’o’in juna.

[2]  Wato ƙarfin hali/ ɗaukar nauyi.

[3]  Wani ɗan gidan da ake yi wa zuma da karare da ciyayi a ɗora masa a saman bishiya don ya shiga ya yi ‘ya’ya a ciki.

[4]  Kiɗi/gamga.

[5]  Manomi na gaskiya.

Post a Comment

0 Comments