Ticker

Ali Na Mani Kotoko

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ali  Na Mani Kotoko

 

  G/Waƙa: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

 Jagora: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

.‘Y/ Amshi : Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Maikano Ali  Na Mani Kotoko.

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Alhaji Ali  Na Mani Kotoko.

  ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Alhaji Ali  Na Mani Kutakutai[1].

  ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Ranar Ali  Na Mani mai galma.

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: ,Alhaji Ali mazan aiki korau.x2

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko[2].x2

 

Jagora: Ko Garba na Ammani na Huntuwa,x2

 ‘Y/ Amshi: Ya san  akwai  Na Mani Ƙanƙafai.x2

 

Jagora: Alhaji Ali  Na Mani kutakutai

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Alhaji Ali  Na Mani Ƙanƙarfai[3].

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko..

 

Jagora: Ina Ɗanmalka na sarki mai Wasagu.x2

  ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.x2

 

Jagora: Alu Ɗanmalka na sarki mai Wasagu

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora:  Ja maza a je aikin kaftu.

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Kyawon maza aikin kaftu[4].x2

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko..x2

 

Jagora: Baba Ali  Na Mani Kutakutai.

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

Jagora: Alhaji Ali mazan aikin gayya..

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Ga ƙwad[5] da ƙasa da abinci,

: taho Gwamnati biɗo taki ya isa.,

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko..

 

Jagora: Ga mai ƙwad da ƙasa da abinci.

: Ku ce Gwamnati sawo taki sosai..

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko..

 

Jagora: Alu mai ƙwad da ƙasa da abinci,

: A ce Gwamnati sawo taki shi isa.

‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko..

 

Jagora: Ke Gwamnati ki yo taki ya isa

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Ke Gwamnati ki yo taki ya isa

 ‘Y/ Amshi: Wo Ali  Na Mani Kotoko...

 

Jagora: Alhaji Ali na Mani kotoko,

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Alhaji Ali  Na Mani Ƙanƙarfai[6].

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Ɗauki galma a je aikin sosai.

 ‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.

 

Jagora: Ali ya ɗara shanu jan[7] galma.x2

‘Y/ Amshi: Ranar Ali  Na Mani Kotoko.x2



[1]  Wasu abubuwa masu wahalar canyewa. Kututu da yawa.

[2]  Laƙabinsa ne, mai nasaba da irin girman jikinsa.

[3]  Wata sifa ce mai nuna cewa mutum ƙaƙƙarfa ne.

[4]  Saran ƙasar gona domin a zakuɗa ta don a tayar da dwayarta.

[5]  Ƙosar da/ciyar da mutane ko wasu halittu har su ƙoshi.

[6]  Wata sifa ce  mai nuna ƙaƙƙarfan mutum.

[7]  Yin huɗa a gona.

Post a Comment

0 Comments