Ticker

Ali Na ‘Yankuzo

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ali Na ‘Yankuzo

 

 G/Waƙa: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka[1],

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Ni Maidaji gani.

 ‘Y/ Amshi: Na shirya kaya zani ‘Yankuzo,

: Dalilin Alhaji niz zaka,

: Domin in gano gida.

 

Jagora: Gonar Alhaji Ali,

: Ta yi buhun gero dubu-dubu[2].

 ‘Y/ Amshi: Kuma gonar Alhaji Ali,

: Ta yi buhun dawa dubu-dubu.

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

Jagora: Gonar Alhaji Ali,

: Ta yi buhun gero dubu-dubu.

 ‘Y/ Amshi: Kuma gonar Alhaji Ali,

: Ta yi buhun dawa dubu-dubu.

 

 Jagora: Shi buhun jad dawa an ce,

: Ya hi buhun gero tuwon Ƙwarai.

 ‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,

: Ya hi buhun dawa hurar ƙwarai,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka[3],

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Shi buhun jad dawa an ce,

: Ya hi buhun gero tuwon ƙwarai.

 ‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,

: Ya hi buhun dawa hurar ƙwarai.

 

 Jagora: Naga matana na murna,

 ‘Y/ Amshi: Kowace sai ta kwashi zamiya[4],

: Halama Alhaji Ali,

: Yai masu masha’a hatsin tuwo,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Da Ta’Allah da amai kuɗɗi.

 ‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta washiya[5],

: Halama Alhaji Ali,

: Yai masu masha’a hatsin tuwo.

 

 Jagora: Da Ta’allah da amai kuɗɗi.

 ‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta washiya,

: Halama Alhaji Ali,

: Yai masu masha’a[6] hatsin tuwo,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Akwai wani babban dam wurin Ali,

: Ya yi tsayi yai hwaɗi.

 ‘Y/ Amshi: Ni da niz zo in ebo shi,

: Na ishe[7] ya koma,

: Hwarau-hwarau,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo,

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

Jagora: Akwai wani babban dam wurin Ali,

: Ya yi tsayi yai hwaɗi.

 ‘Y/ Amshi: Da niz zo in ebo shi,

: Na ishe ya koma,

: Hwarau-hwarau.

 

 Jagora: Hillani[8] kun cika gurin ku.

 ‘Y/ Amshi: Mashayarku ta koma ruwan hura.

 

 Jagora: Hillani kun cika gurinku.

 ‘Y/ Amshi: Mashayarku ta koma ruwan hura.

 

 Jagora: Hillani kun cika gurin ku.

 ‘Y/ Amshi: Mashayarku ta koma ruwan hura.

 

 Jagora: Na game da hillanin Tsafe.

 ‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin hura.

 

 Jagora: Harda hillanin Bilbis.

 ‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin hura.

 

 Jagora: Har na ‘Yankara sun takas.

 ‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin hura.

 

 Jagora: Har na garin ‘Yammalammai.

  ‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin hura.

 

Jagora: Har na Ɗansaɓau sun tadakka.

  ‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin hura.

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 Jagora: Ashe harda ni makaɗin ganga.

 ‘Y/ Amshi: Ashe lokacin tashinmu ya taho.

 

 Jagora: Ashe harda ni makaɗin ganga.

 ‘Y/ Amshi: Ashe lokacin tashinmu ya taho.

 

 Jagora: In dai ana mana ɗan busau[9].

 ‘Y/ Amshi: Sai na tashi na koma wurin hura,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

Jagora: Ni Maidaji gani na,

: Shira[10] kaya zani ‘Yankuzo.

 ‘Y/ Amshi: Dalilin Alhaji Ali,

: Niz zaka domin in gano gida.

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Hajiya Halima tana kyauta.

 ‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.

 

  Jagora: Ina godiya hajiya Mairo.

  ‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Hajiya Sa’a na gode mat.

 ‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Hajiya Sa’a na gode mat.

 ‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Dab baya tai mani anhwani[11].

  ‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Dab baya tai mani anhwani.

 ‘Y/ Amshi: Ina yaba imani ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Lalle Alhaji na gode,

: Ya  ba ni buhu goma.

: A yi min tuwo.

 ‘Y/ Amshi: To su kau dangi nai,

: Sun ban buhu shidda,

: A yi min hura.

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

Jagora: Lalle Alhaji na gode,

: Ya  ba ni buhu goma,

: A yi min tuwo.

 ‘Y/ Amshi: To shi kau dangi nai,

: Sun  ba ni buhu shidda,

: A yi min hura.

 

 Jagora: Lalle Alhaji na gode,

: Ya  ba ni buhu goma,

: A yi min tuwo.

 ‘Y/ Amshi:  To su kau dangi nai,

: Sun  ba ni buhu shidda,

: A yi min hura.

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Shi buhun jad dawa[12] an ce,

: Ya hi buhun gero tuwon ƙwarai.

 ‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,

: Ya hi buhun dawa hurar ƙwarai,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Shi buhun jad dawa an ce,

: Ya hi buhun gero tuwon ƙwarai,

 ‘Y/ Amshi: To shi kau geron an ce,

: Ya hi buhun dawa hurar ƙwarai.

Jagora: Na ga matana na murna,

 ‘Y/ Amshi: Kowace sai ta kwashi zamiya[13].

: Halama Alhaji Ali,

: Yai masu masha’a hatsin tuwo,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Da Ta’allah da mai kuɗɗi,

 ‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta washiya[14].

: Halama Alhaji Ali,

: Yai masu masha’a[15] hatsin tuwo?

 

 Jagora: Da Ta’allah da Maikuɗɗi.

 ‘Y/ Amshi: Har ‘yar mai goro suna ta washiya,

: Halama Alhaji Ali,

: Yai masu masha’a[16] hatsin tuwo,

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Akwai wani babban dam wurin Ali,

: Ya yi tsayi yai hwaɗi,

 ‘Y/ Amshi: Ni da niz zo in ebo shi,

: Na ishe[17] ya koma hwarau-hwarau[18],

: Gonar Alhaji Ali,

: Ƙare-kallonka,

: Na ‘Yankuzo.

: Wagga gona,

: Allah yai mata,

: Ƙarhin albarka,

: Ƙwarai-ƙwarai.

 

 Jagora: Akwai wani babban dam wurin Ali,

: Ya yi tsayi yai hwaɗi[19],

 ‘Y/ Amshi: Ni da niz zo in ebo shi na ishe ya koma,

: Hwarau-hwarau,

 

 Jagora: Hillani kun cika gurin ku.

 ‘Y/ Amshi: Mashayar ku ta koma ruwan hura.

 

 Jagora: Hillani[20] kun cika gurinku,

 ‘Y/ Amshi: Mashayar ku ta koma ruwan hura.

 

 Jagora: Hillani kun cika gurin ku.

 ‘Y/ Amshi: Mashayakku[21] ta koma ruwan hura.

 

 Jagora: Na game da hillanin tsafe.

 ‘Y/ Amshi: Duk sun tashi sun koma wurin hura.



[1]  Mai yawa sosai, wanda kan kure kallon mutum.

[2]  Wato dubu saw dubu miliyan kenan

[3]  Idan duk abin da kake tsammanin ka gani ka gane shi hard a ƙari, ka ƙare kallonka.

[4]  Murna mai sa rawa.

[5]  Jiki mai kyawo.

[6]  Alkawalin za a bayar da wani abu.

[7]  Iskewa.

[8]  Fulani.

[9]  Fari.

[10]  Shiryawa/kimtsawa don tafiya.

[11]  Amfani wato bashi kyauta.

[12]  Jar dawa.

[13]  Murna mai sa rawa.

[14]  Jiki mai kyawo.

[15]  Alkawalin bayar da wani abu.

[16]  Alkawalin za a bayar da wani abu.

[17]  Iskewa.

[18]  Ruwan shad a aka zuba fura a ciki.

[19]  Faɗi

[20]  Fulani.

[21]  Wurin da suka ba dabbobinsu ruwa.

Post a Comment

0 Comments