Ticker

Almajiri Tsuntsu Ne

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

 Almajiri Tsuntsu Ne

 Da bara da bara ɗan malam,

 Almajiri tsuntsu ne,

 Da yaj ji motsin tsaba ,

 Sai yay yi hiringi da kunne,

 Awar mataccen kusu,

 Nan ko ba kusu ne ba,

 Mutun ne ɗan aljanna,

 Ɗebo ruwa in dama,

 In dama ko ban sha ba,

 In kai gaban alƙali,

 Alƙali ɗan Mamuda,

 Mamuda bawan Allah,

 Wanda baya cewa babu,

 Sai dai taho in baka,

 In baka yaron malam.


Post a Comment

0 Comments