Ɗan Amina.

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Ɗan Amina.

     Jagora: Ya bisimilla Allah.

     Amshi: Ɗan Amina.

     Jagora: Za ni yabon Muhamman.

     Amshi: Ɗan Amina.

     Jagora: Mai birnin Madina Mamman.

     Amshi: Ɗan Amina.

     Jagora: Ina masoya Muhamman.

     Amshi: Ɗan Amina.

     Jagora: A ba mu domin Allah.

     Amshi: Ɗan Amina.

     Jagora: In da rabo da niyya.

     Amshi: Ɗan Amina.

     Jagora: Don Shi za a ba mu.

     Amshi: Ɗan Amina.

     Jagora: Mai daraja Muhamman.

     Amshi: Ɗan Amina.

     (Ɗan Amina)

    Wannan waƙar a cikin taro mabarata suke aiwatar da ita sadda suke bara, amma kuma sau da yawa akan sami mai bara shi kaɗai yana rera ta. Haka kuma, a mafi yawan lokuta mabarata mata ne suka fi amfani da ita. Idan aka lura waƙar ta begen Annabi Muhammadu ce (SAW). Ga ƙarin misalin wata waƙar mai suna “Mu Tai Bara”.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.