Ticker

Dan Bawa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ɗan  Bawa

 

 G/Waƙa: Ya tara dami mai dama,

: Ɗan  Bawa Ɗanen mai gona.

 

 Jagora: Dubun Ɗan  Bawa,

 ‘Y/ Amshi: Na manuga jikan bana.

: Kai munka sani tun farko,

: Ya tara dami mai dama,

: Ɗan  Bawa Ɗanen mai gona.

Jagora: Dubun Ɗan  Bawa,

 ‘Y/ Amshi: Nufin Allah ne,

: Allah ya yai mai huɗuba mai tasai,

: Ya tara dami mai dama,

: Ɗan  Bawa ƙanen mai gona.

 

 Jagora: Ɗan  Bawa inai ma horo.

 ‘Y/ Amshi: Kai dai ka tsare horo na.

 

  Jagora: Horon da nikai maka.

  ‘Y/ Amshi: Arna kowa ya riƙe mata tai.

 

 Jagora: Kowa ya yi dubu har ya yi rabo.

 ‘Y/ Amshi: Ya ɗau[1] maganar kaka nai,

: Ya tara dami mai dama,

: Ɗan  Bawa ƙanen mai gona.

 

 Jagora: Dogo Ɗan  Bawa.

 ‘Y/ Amshi: Hwaɗin[2] Allah ne.

 

Jagora: Kullun na zaka wurin yawona,

: Ina iske mijin ‘Yas suntau.

‘Y/ Amshi: Sai ya  ba ni dami in ɗauko,

: Ya tara dami mai dama,

: Ɗan  Bawa ƙanen mai gona.

 

 Jagora: Mai kasuwa.

 ‘Y/ Amshi: Ban dai rena ba,

: Riga ta ƙwarai ya sa min,

: Domin ka ƙanen mai gona.

 

 Jagora: Sarkin noma ƙanin ‘yar burmau,

 ‘Y/ Amshi: Ban dai raina riga ta ƙwarai ya samin dami,

: Domin ka ƙanin mai gona.

 

 Jagora: Ɗan Mairi.

 ‘Y/ Amshi: Ban dai raina riga ta ƙwarai ya samin dami,

: Domin ka ƙanin mai gona.

: Ya tara dami mai dama,

: Ɗan  Bawa ƙanen mai gona.



[1]  Yin amfani da abin da aka hore shi.

[2]  Faɗar Allah, abin da Allah ya nufa.

Post a Comment

0 Comments