Ticker

6/recent/ticker-posts

Anaruwa Dan Namudi

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Anaruwa Ɗan Namudi

Anaruwa mutumen garin Galadi ne ta cikin ƙaramar hukumar mulkin Shinkafin jihar Zamfara, a wata unguwar da ake kira ‘yar ƙofa. Yana noma daidai gwargwado amma dai maɗinkin tela ne, Amali ya waƙe shi saboda irin kyautatawar da ken tsakanin su.

 

    G/Waƙa : Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Kada ruwa su ci mai hito,

‘Y/Amshi: Tun da bami[1] bai iya ba,

 

     Jagora: Ran da bami ya iya, x2

‘Y/Amshi: Shi gwani ya hwanshi kainai.x2

 

Jagora: Anaruwa Ɗan Namudi,

‘Y/Amshi: Mijin Hana Ceci gayya[2].

 

Jagora: Anaruwa roƙi Allah,

: Ya bar ma masu son ka,x2

‘Y/Amshi: Ɗiyan maƙiyanka su ko,

: Su hude ciki da barho[3],x2

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

 Jagora: Sarki ya yi doka,

: A bar waƙar manoma,

: In bamu garza[4] su,

: Ba aiki sukai ba,

‘Y/Amshi: Dan nan am mahwarin,

: Hatci su katce ma gwarza,

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

 Jagora: Ga wasu na hwarin cikin,

: An dwaɗekke roƙo,

: Wannan mai hwarin cikin,

: Komi bai daɗa ba,

: Wasu ma baƙin cikin,

: Roƙo ba a yi nai,

‘Y/Amshi: Wanna mai baƙin cikin,

: Ba baiwa yakai ba.

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Ga sad[5] da ana kiɗi,

: Ba ni kwana ba tagari[6],

‘Y/Amshi: Da anka ruhe kiɗi,

: Ko kumallo ban karawa,

 

     Jagora: Garba ga ni tsakag gida,

‘Y/Amshi: Ga takaici na ta cin ka.

 

Jagora: Sada ga ni cikin gida,

 ‘Y/Amshi: Ga takaici[7] na ta cin ka.

 

Jagora: Labbo ga ni cikin gida,

‘Y/Amshi: Ga talaici na ta cin ka.

 

Jagora: Ga ni ba kuɗɗin awo,

‘Y/Amshi: Ga ka ba tsabad dakawa.

 

     Jagora: Tun da gero ya ɓace,

‘Y/Amshi: Dole sai mu gama da gari[8].

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Mu zo mu ga mai jiƙo,

‘Y/Amshi: Alhajin jama’ar Arewa,

 

     Jagora: A kai ni ga mai jiƙo[9].

‘Y/Amshi: Alhajin jama’ar Arewa.

 

 Jagora: Gari ya hito daz Zamfara,

: Ya dibi Gobir,

: Gari ya buga gabas,

: Ya koma ma yamma,

: Na yi amaw wata,

: Ina taɓa yawon ƙasaisai[10],

: Ina saitin gidaje,

: Ina ta awon manoma,

: Yau duk inda nib biya,

: Gari na riga na.

‘Y/Amshi: Gari na riga na.

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.x2

 

 Jagora: Kun gani yunwa tana,

: Sa mutun ya yi zam ne jangwam[11],

: Yana magana cikin zuciya,

: Tai ba a sani ba!

‘Y/Amshi: Yana magana cikin zuciya,

: Tai ba a sani ba!

Jagora: Sai ka ji zuciyatai,

: Tanai mai ebe-ebe.

‘Y/Amshi: Sai ka ji zuciyatai,

: Tanai mai ebe-ebe,

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

Jagora: Ashe yunwag ga na sa,

: Mutun ya gaza da mata,

: Ya sa a yi mai jiƙo,

: Ba ya ce mata tashi ga shi,

 

‘Y/Amshi: Ya sa a yi mai jiƙo,

: Ba ya ce mata tashi ga shi,

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

 Jagora: Ka gani yunwag ga,

: Na iske Ɗangaye ta shurai,

‘Y/Amshi: Ta ce mai tashi zanne,

 

 Jagora: Ashe yunwag ga,

: Na iske Ɗangaye ta marai,

‘Y/Amshi: Ta ce mai ya hakanga?

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

     Jagora: Na ga Ɗangaye,

: Da gayan tuwo ya sa ga baki,

: Kuɗɗin sabulu,

: Masu gari anka ba su.

‘Y/Amshi: ‘Yan kuɗɗin bula,

: Masu bakhru nar riƙe su,

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

     Jagora: Wanga irin bakin,

: Zamani Allahk kiyaye,

: Wasu na ta tashi,

: Suna tahiyas su Gwambe,

: Mu kau mun tsaya,

: Nan muna gyaran gidaje,

: In mun cimma,

: Gyaran ta ba tashi mukai ba,

‘Y/Amshi: In ta ɓaci,

: Ko singa[12] ba ta rigan mu Bima,

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

     Jagora: Shekarun ‘yan dandi[13] na,x2

‘Y/Amshi: Ba gudun kunya akai ba.x2

 

     Jagora: Yanzu karuwa tai yawa,x2

‘Y/Amshi: Ga su nan hab ba iyaka.x2

 

Jagora: Kuma ƙattan da an nasu,

‘Y/Amshi: Ba aiki sukai ba.

 

Jagora: Masu noma ‘yan kaɗan.x2

 ‘Y/Amshi: Masu ci nai ba iyaka,x2

   

 Jagora: Karuwa ke baro uwaye,

: Ke zaɓi dandi,

 ‘Y/Amshi: Wagga ɗiya uwayenki,

: Na da baƙin cikin ki.

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.

 

 Jagora: Tashi baki da gaskiya,x2

  ‘Y/Amshi: Ke baro ɗakin mijinki.x2

 

 Jagora: A a duw wata gaskiya,x2

  ‘Y/Amshi: Sai da aure za a yinta.x2

 

 Jagora: Da dub ba a gyara aure ba,x2

 ‘Y/Amshi: Ke ma ba a yin ki.x2

 

Jagora: Ke an yo ki.

‘Y/Amshi: Ko ɗa guda baki sami yi ba,

   

Jagora: In da kwana duniya,

: Babu kwana lahira,

‘Y/Amshi: Ran da kwana nac cika,

: Ban ga kwana duniya ba.

   

     Jagora  : A sai nono da mai,x2

‘Y/Amshi: Inji matam mai bisashe[14].x2

 

 Jagora: Ku sai tsabat tiya[15].x2

  ‘Y/Amshi: Inji maiɗakin manomi.x2

 

 Jagora  : Duk ku kawo in saye,

  ‘Y/Amshi: Inji matam mai sulalla[16].x2

: Ya yi halin maza,

: Ko da rani bai sake ba,

: Sauka lahiya,

: Mai batun yaƙi da sabra.



[1]  Wanda bai iya yin wani abu ba kamar iyo a cikin ruwan kogi.

[2]  Mutane da yawa.

[3]  Wuƙa mai kaifi ɗaya.

[4]  Kwarzanta su don su himmatu.

[5]  Lokacin da wani abu yake faruwa.

[6]  Hatsi kenan da ake yin gari da su.

[7]  Haushi.

[8]  Garin kwaki.

[9]  Wani mutum ne wanda yake yin sana’ar jiƙa wa mutane garin kwaki don su ci su biya.

[10]  Wurare ko garuruwa daban daban.

[11]  Zama marar dalili a rikice.

[12]  Sunan wata mota ne mai tafiya da sauri ƙwarai

[13]  Mutanen da suke barin garuruwansu suna zuwa wasu birane don yawon banza kamar karuwanci ko waninsa..

[14]  Dabbobin kiyo a gida kamar Shanu ko tumaki ko awaki.

[15]  Hatsin da ake aunawa da tiya, wato wasu kaɗan ba buhu ko buhuhuwa ba.

[16]  Mai kuɗi.

Post a Comment

0 Comments