Ticker

Kanen Dan Magajiya Mainasara

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ƙanen Ɗan Magajiya Mainasara

 

G/Waƙa: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye[1].

 

 Jagora: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

 ‘Y/ Amshi: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

 

Jagora: Yan mazan ƙwarai,

: Suna ƙaunatai,

: Mai geron baye,

: Ya aje gero ya aje dawa,

‘Y/ Amshi: Ga maiwa jibge,

: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

 

  Jagora: Waƙag ga na ga ta ƙeru,

: Babu karkace,

: Babu matsala,

: Babu tangarɗa,

‘Y/ Amshi: Ba wata tangaɗa,

: Na massasara,

: Ba wasu ‘yan kukkai[2].

: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

 

  Jagora: Duk randa ya yi mula daire,

: Ran talata ga kasuwar da ya yi,

: Gayya mun wuni,

: Mun ƙwan muna,

‘Y/ Amshi: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

 

  Jagora: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

‘Y/ Amshi: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

 

Jagora: Koda naji ya yi ma laifi,

: Ni ko na yi mai faɗa,

: Don mi ka basu?

: Ya kashe kuɗi,

: Laifin ga ƙarya faɗa ga nai

‘Y/ Amshi: Da sai na marai

 

Jagora: Mai rana na faɗin inda ni ne

‘Y/ Amshi: Da sai na shurai

 

Jagora: Yan ba ka koma ma kura fiɗa

: Kos a naka ba ta fiɗa ba’a ishe

: Nama balle an rago

‘Y/ Amshi: Balle Ɗan rago

: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.

Jagora: Yan mazan ƙwarai,

: Suna  gonatai.

‘Y/ Amshi: Bai san Lotto[3] ba.

 

 Jagora: Ya aje gero ya aje dawa,

: Ga maiwa cinjim[4] .

‘Y/ Amshi: Ƙanen Ɗan Magajiya,

: Mainasara,

: Mai geron baye.x2



[1]  Gonakin da turen ruwa yake wankewa na manyan gulabe ko rafuke su ake kira baye.

[2]  ‘Yan Koke-koke.

[3]  Lokaci, wato bai san lokacin zuwa ko tasowa gona ba, ma’ana kowane lokaci na zuwa gona ne gareshi don aiki.

[4]  An tara da yawa.

Post a Comment

0 Comments