Ticker

Danja Mai Kwana da Shirin Ma’aikata

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ɗanja Mai Kwana da Shirin Ma’aikata

Ɗanja mutumin garin Batamna ne a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Sunasa Amadu amma an fi saninsa da Ɗanja. Manomi ne na haƙiƙan a ƙauyen nasu kuma koyaushe a shirye yake da ya je gona, wana halayyar tana burge Amali har ya yi ma mai yinta waƙa.

 

G/Waƙa : Koma sakko gona,

: Kar ka tsaya zaman gida,

: Mu gaida Ɗanja,

: Mai kwana da shirin ma’aikata[1].

 

    Jagora: Kuikuyon zaki,

: Mai maida bida kake Ɗanja.

    ‘Y/Amshi: Irin gidan Ummaru,

: Ka zan zakaran ɗiya maza,

 

    Jagora  : Kuikuyon[2] zaki,

: Mai shanye dahi[3] kake Ɗanja.

    ‘Y/Amshi: Irin gidan Ummaru.

: Ka zan zakaran ɗiya maza.

 

    Jagora: Ba iyaka ba da kai,

: Ba a biye ka ga noma,

    ‘Y/Amshi: Wanda duk ka biye ma,

: Ba ya zuwa gida maza,

: Koma sakko gona,

: Kar ka tsaya zaman gida,

: Mu gaida Ɗanja,

: Mai kwana da shirin ma’aikata.

 

    Jagora: Noma da kai aka sauna,

: Ba a haye maka barde,

: Sallama kada gaba,

: Geme baban yaro,

: Garnaƙaƙi kake ɗan ja,

    ‘Y/Amshi: Wanda duk ka haye ma,

: Toggo[4] yana ganin gida,

: Koma sakko gona,

: Kar ka tsaya zaman gida,

: Mu gaida Ɗanja,

: Mai kwana da shirin ma’aikata.

 

    Jagora: Mata wadda ba a wa iba[5],

    ‘Y/Amshi: Mik kai ta zuwa masussuki[6],

 

    Jagora: Mata wadda ba mijin kirki,

    ‘Y/Amshi: Mik kai ta zuwa masussuki,

 

    Jagora: Duw wadda ba a ba damma.

    ‘Y/Amshi: Mik kai ta zuwa masussuki.

 

    Jagora: Wadda ba a wa iba[7].

    ‘Y/Amshi: Mik kai ta zuwa masussuki.

 

    Jagora: Wadda ba na albarka.

    ‘Y/Amshi: Mik kai ta zuwa masussuki.

 

    Jagora: Macce mai koda.

    ‘Y/Amshi: Abu sai mu aje ta tsohuwa.

 

    Jagora: Macce mai koda.

    ‘Y/Amshi: Abu sai mu aje ta tsohuwa.

 

    Jagora: Mijinta in Goje ne.

    ‘Y/Amshi: Ba ta yini tsakar hwaƙo.

: Koma sakko gona,

: Kar ka tsaya zaman gida,

: Mu gaida Ɗanja,

: Mai kwana da shirin ma’aikata.

 

    Jagora: Abin da ar arne.

    ‘Y/Amshi: Gero ya tsaya cikin gida.

 

    Jagora: Abin da ag Goje[8].

    ‘Y/Amshi: Gero ya tsaya cikin gida.

 

    Jagora: Ya yi matan tsara,

: Sun isa,

: Ga su hwarhwaru,

: Ga katanbiri,

: Ga hwankeke;

: Ana yi mai ƙawa,

: A shafa gazal,

: A kusanto shi,

: Ana ƙyahwat ƙyahwat,

: A shafa jan baki,

: A dibo shi ana ta washiya,

: Su shahwa kwalli.

    ‘Y/Amshi: Ka ga an buɗe ido narau-narau[9],

: Koma sakko gona,

: Kar ka tsaya zaman gida,

: Mu gaida Ɗanja,

: Mai kwana da shirin ma’aikata.

 

    Jagora: Duw wurin da yad duba. 

    ‘Y/Amshi: Daɗi yaka ji cikin gida.

 

    Jagora: Duw wurin da yad hanga.

    ‘Y/Amshi: Daɗi yaka ji cikin gida.

: Koma sakko[10] gona,

: Kar ka tsaya zaman gida,

: Mu gaida Ɗanja,

: Mai kwana da shirin ma’aikata.



[1]  Gona.

[2]  Ɗan wata dabba wanda ba a daɗe da haihuwarsa ba.

[3]  Dafi-poision.

[4]  Da ƙyar/ ƙila.

[5]  Ɗebo hatsi daga cikin rumbu/rihewa don a sussuka a yi amfani das hi wajen dafa abinci.

[6]  Ibda ake sussujar gero ko dawa.

[7]  A ɗebo hatsi daga runbu don a sussuka.

[8]  Shahararren manomi.

[9]  Hasken ido, fari cikin ido ya yi fari baƙin ɗigon cikin ido ya yi baƙI gwanin sha’awa.

[10]  Sammako.

Post a Comment

0 Comments