Ticker

6/recent/ticker-posts

Danladi Kanen Buzu

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ɗanladi Ƙanen Buzu

 

G/Waƙa: Ya kwan da shirin aiki,

: Ɗanladi ƙanen Buzu.

 

 Jagora: Sarkin yaƙi ƙanen Buzu.

 ‘Y/ Amshi: Ɗanladi miyas sallah,

: Ai bata iri daɗi[1].

 

  Jagora: Haba Ɗanladi tsare aiki.

‘Y/ Amshi: Mu kau mu tsare turu[2].

 

  Jagora: Dogo barka da yini daji.

 ‘Y/ Amshi: Barka da zuwa gona.

.: Ya kwan da shirin aiki,

: Ɗanladi ƙanen Buzu.

 

Jagora: Ƙwazon makaɗa ya gode.x2

 ‘Y/ Amshi: Bakin da ya ci ya gode,

: Mu bamu butulce[3] ba.

: Ya kwan da shirin aiki,

: Ɗanladi ƙanen Buzu.x2

 

 Jagora: Kwanakki ana shirin yawo,

 ‘Y/ Amshi: Ya  ba ni sule goma,

: Kuma da munka zo kura,

: Ya  ba ni sule goma,

: Kuma da munka dawo nan,

: Ya  ba ni sule goma,

: Komi aka yi, ya yi.

: Ya kwan da shirin aiki,

: Ɗanladi ƙanen Buzu.

 

 Jagora: Haba Arne tsare kai taki.x2

 ‘Y/ Amshi: Don Allah bari sa rani.x2

: Ya kwan da shirin aiki,

: Ɗanladi ƙanen Buzu.

 

Jagora: Ƙwazon makaɗa ya gode.x2

 ‘Y/ Amshi: Bakin da ya ci ya gode,

: Mu bamu butulce[4] ba.

: Ya kwan da shirin aiki,

: Ɗanladi ƙanen Buzu.x2

 

 Jagora: Sarkin yaƙi ƙanen Buzu.

 ‘Y/ Amshi: Ɗanladi miyas sallah,

: Ai bata iri daɗi.

 

 Jagora: Dogo barka da yini[5] daji.x2

  ‘Y/ Amshi: Barka da zuwa gona.

.: Ya kwan da shirin aiki,

: Ɗanladi ƙanen Buzu.x2



[1]  Babu wata miya mai irin daɗin miyar sallah.

[2]  Kiɗa da waƙa.

[3]  Ida nana ba mutum wani abu sai ya riƙa nuna ba a bashi wannan shi ne butulci.

[4]  Ba su ci suka ƙI nuna sun ci ba, wato suna ya Bawa ga duk wanda ya yi masu kyauta.

[5]  Zuwa gona tun da safe har yamma domin ayyukan noma.

Post a Comment

0 Comments