Karamin Turken Bankwana a Wakokin Amali Sububu

    Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Ƙaramin Turken Bankwana a Waƙoƙin Amali Sububu

    Wannan kalma ta bankwana tana nufin yi wa wasu jama’a wasu kalamai masu nuna mai yin bankwanan zai tafi ya bar su ya je wani wuri. Amali yana bankwana da jama’a in ya je wurin waƙarsa, dubi yadda yake cewa:

    Jagora : Ku na Arewa da ku da na nan Kudu,

      : Na Yamma da ku jama’ag Gabas,

      : Maza da mata kui mani gahwara.

    ’Y/Amshi  : Maza da mata kui mani gahwara,

    : Amali gobe gida yaka son zuwa.

    : Ko da rani baya zama gida,

    : Gidan Karimun  za ni wurin kiɗi.

    (Amali  Sububu: Abdulkarimu)

       

    A wata kuma:

    Jagora : Sai wata rana  Sa’idu zaure masha baƙi,

    ’Y/Amshi : Sai wata rana da ni da ku in ji mai ƙorai, 

     

    Jagora : Sai wata rana da ni da Kwamma da

    : Maigayya, 

    ’Y/Amshi : Sai wata rana da ni da ku in ji mai ƙorai,

      : Tahi noma  Sa’idu dokin sukan sabra,

      : Tahi gonakka raƙumi mai yini duƙe.

         (Amali  Sububu: Sai’du Zarton hwashin gaɓa)

     

    Haka nan kuma a wata waƙar ya ce:

    Jagora : Bankwana yana bani tausai,

    : Da sunka zo rakkiya ta,

      : Nid dibi jamin mutane,

      :  Za ni rabo da huskam[1] masoyana,

      : Sai zucciya taj jiye man,

      : Ka san ba ƙashi ag gare ta ba,

      : Sai niɗ ɗora ƙyallin[2] hawaye,

      : Sai wataran da ku masu so na,

      : Ko mu game da ku masu so na,

      : Ko ko dai ya zan ba gamewa,

      : Saboda ban san ta rai ba,

      : Hakanga na bani tsoro,

    ’Y/Amshi : Bai san wuyag gargare ba,

    : Ga Garba can za mu jiɗa,

    : Namijin da noma ka wa haske.

    (Amali  Sububu: Garba).   

     

    A wata waƙar kuwa Amali yana cewa:

         Jagora  : Sai wataran da ku yan  Gatawa,

        : Tahiya gidana za ni yi.

    Y/Amshi : Tahiya gidana  za ni yi ,

        : Jama’ag ga sai kuma an jima,

        : Da gaskiya yaka sa mota tahiya

    : Da lambobin gudu,

        : Allah ya tsare da tsarewa,

        : Tai ka gama da kowa lahiya.

      

    Amali ya yi bankwana da jama’ar garin Gatawa, wato garinsu isuhu direba kenan wanda ya yi wa waƙar tuƙin mota, inda yake nufin cewa bayan ya kammala waƙar tafiya gida zai yi ba zai dakata ba.



    [1]  Fuskokin

    [2]  ƙwalla- hawaye su cika ido ko da mutum bai yi kuka ba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.