Karamin Turken Turanci a Wakokin Amali Sububu

    Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Ƙaramin Turken Turanci a Waƙoƙin Amali Sububu

    Turanci harshe na mutanen Turai wanda Turawa suka shigo da shi a ƙasarmu Nijeriya, ana samunsa ne ta hanyar boko. Amali ya kawo waɗansu kalmomin Turanci a ciki waƙoƙinsa kamar haka:

    Jagora : Mun kwana munka yo sallah munka

    : dawo,

       : Amali na yi hul tanki[1] tun da sahe,

       : Ni dai ina ta ɗora giya babu dama,

       : Mun zo Arewa mun yi kwana,

       : Munka kwan nan.

    ’Y/Amshi : Jijjihi yakai daji baya wargi[2],

       : Kodayaushe shi dai baiu san sake ba,

    : In yi mai kiɗin aiki Garba Dauran.

    (Amali  Sububu: Garba Dauran)  

     

    Hul tanki a nan yana nufin cika tankin wani abin hawa da mai “wato full-tank” kamar mashin ko mota da sauran injinonin da ke amfani da mai. Ita kuma kalmar “kwana” da Amali ya yi amfani da ita ararriya ce daga Turanci wato “corner” wadda take nufin juyowa ko sake hanya daga wadda mutum yake a kanta tun farko.



    [1]  Cika tankin wani abin hawa mai ijnjin kamar mashin ko mota.

    [2]  Wasa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.