Ticker

Arzika Kulkin Horon Jema

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Arzika Kulkin Horon Jema

Arzika Ɗan Nakahe a garin Gidan Kwando yake, cikin riƙon Galadi a ƙaramar hukumar Shinkafi. Amali    Sububu ya kai masa waƙa ne saboda irin yadda ya samu fice a harkar noma.

  G/Waƙa : Tahi gona,

: Bai san gargare[1] ba,

: Jan zaki rana mi takai ma?

 

    Jagora: Arzika kulkin ho,

: Ron jeme na Roƙo,x2

    ‘Y/Amshi: Arzika Kulkin ho,

: Ron jema na Roƙo.x2

 

    Jagora: Arzika Ɗan na kahi,

: Ɗan soren na Hantsi, x2

      ‘Y/Amshi: Alhaji Ɗan na kahi,

: Ɗan soren na Hantsi, x2

 

    Jagora: Mai shiga ramen,

: Kura ka zaƙe,x2

    ‘Y/Amshi: Babu ila shakka,

: Kura za ta ci nai.x2

: Tahi gona,

: Bai san gargare ba,

: Jan zaki rana mi takai ma?

       Jagora: Dauri ina yaro,

: Ban san kan kiɗi ba,

: In ka ban kuɗɗi in kiɗa ma,

: Kuma ko ba kuɗɗi in kiɗa ma,

: In kab ban gero in kiɗa ma,

: Kuma ko ba gero in kiɗa,

: Yanzu da nir rege,

: Na bambanta roƙo,

      ‘Y/Amshi: Amali ya rege,

: Banza ba ta sha nai.

 

    Jagora: Amali na gane,

: Banza ba ta sha na,

    ‘Y/Amshi: Amali ya rege,

: Banza ba ta sha nai,

: Tahi gona,

: Bai san gargare ba,

: Jan zaki rana mi takai ma?

 

    Jagora: Dauri[2] ina yaro,

: Ban san kan kiɗi ba,

: In ka ban kuɗɗi in kiɗa ma,

: Kuma ko ba kuɗɗi in kiɗa ma,

: In ka ban gero in kiɗa ma,

: Kuma ko ba gero in kiɗa,

: Yanzu da nir rege[3],

: Na bambanta roƙo,

   ‘Y/Amshi: Amali ya rege,

: Banza ba ta sha nai.

 

    Jagora: Duw wata kankanbab,

: Banza ba ta ja na,

    ‘Y/Amshi: Duw wata kankanbab,

: Banza ba ta ja nai.

 

    Jagora: Sada mi kac ce?

: Roƙo zai ci roƙo.

    ‘Y/Amshi: Sada mi kac ce?

: Roƙo zai ci roƙo.

 

    Jagora: Sada ina magana,

: Roƙo zai ci roƙo,

   ‘Y/Amshi: Sada ina magana,

: Roƙo zai ci roƙo[4],

    Jagora: Sada ka ban ƙube,

: Don waƙaƙ ƙanenka,

      ‘Y/Amshi: Sada ka ban ƙube,

: Don waƙaƙ ƙanenka.

 

    Jagora: Shi kiɗin masu gari,

: Sai an sami kotso,

: In ba kotso,

: Taushi za a sa wa,

: Kiɗin karuwai,

: Goge za a sa wa,

: Kiɗin ‘yan tauri,

: Sai an sa kalangai,

: Kiɗin aiki ko,

: Sai mu za mu yi nai,

    ‘Y/Amshi: Duk wani ɗan iska,

: Ya bas shan duman ga,

: Tahi gona,

: Bai san gargare ba,

: Jan zaki rana mi takai ma?



[1]  Rage tsawon kuyya wajen noma.

[2]  Da can/Lokaci mai tsawo da ya wuce.

[3]  Wayewar kai, idan a da ana cutarsa baya ganewa to yanzu yaw aye yana sanin komai.

[4]  Wato wani maroƙi zai baiwa wani maroƙin abinsa.

Post a Comment

0 Comments