Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Ƙato Yaz Zan Bai Noma
G/Waƙa: Ƙato Yaz zan bai
Noma,
: Shi da buhun kowa duɗ ɗai.
Jagora: Sarki huwallazi ya mai girma,
: Nai roƙon sarki mai girma,
: Allah gyara ya rabbana,
: Kai kiɗa
aikin noma,
: Na ce jama’a a tai a yi noma,
: A’a ke yi maza da mata baki dai,
: Ka ji Ɗankurmi can zan kwana,
: Ɗankurmi can zan kwana,
: Don in gano Mamman Sani,
: Sai na biyo ta Ɗan kurmi,
: Sai na biyo ta Tsontsomawa,
: Sai na tsomo waƙar Sani,
: Mamman sani.
‘Y/Amshi: Babin noma.
Jagora : Ai ka ji kidan aikin noma,
: Amma Yaro in yaz zan bai noma,
: Ba ni kular samnan banza.
Jagora :
Sai Yaro yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duk dai,
: Ataɓuka[1]
kuma na noma,
: Ɗan Ige shi ma na noma,
: Ali shi ma na noma,
: Ɗan ladi ashe shi ma na noma,
: Mamman sani,
: Mamman sani,
: Mamman sani,
: Babin noma.
Jagora :
Don Allah ka dakata don rabbani,
: Ga maganar aikin noma,
: An ce dan Ige na noma,
: Kuma ashe Ataɓuka ma na noma,
: Ɗan Mafara ma na noma,
: Audu ka ga yana noma,
: Sannan bilya ma na noma,
: Kasan dogon kwalba ma na noma,
: To balle mamman sani,
: Mamman koma ban noma,
: Bari Mamman in riƙe kwashe[2]
na,
: Kai Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in rike galma ta,
: Amma Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in rike hauyata,
: Mun jeki wajan gayya,
: Ka duka na duka Sani,
: In nag gaji in miƙewa ta,
: In ɗauko
kwano mai dama,
: To sai in tai kiran mai yin noma,
: Allah kawo Mamman Sani.
‘Y/Amshi: Mamman sani,
: Babin noma,
: ‘Yan mata da maza na noma,
: Ka ji kidin waƙar noma,
: Waƙar noma,
: Darajar ɗanɗa.
: Ina wani nac ce ɗan sarki?
: Ko da na ce alkali,
: Ko wani mai iko Sani,
: Yaz zan lallai bai noma,
: Ba ni kular samnan banza,
Jagora :
Kasan maganar dai-dai,
: Guda-guda kai bai yarda ba,
: Guda-guda kai mai,
: Guda-guda kai mai ganga,
: Ko can kiɗin ga ni dai ne Sani,
: Ai ka san gabas da yamma,
: Dama da hauni,
: Mamman duk wani mai noma,
: Mamman noma,
: Mamman Sani,
: Ka ga yana noma,
: Garba ka ga kana noma,
: Yaro in yaz zan bai noma,
‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duk ɗai.
Jagora
: Kato yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Ba mu kula samnan banza.
Jagora : Amma sarkin Mafara ka kyauta man,
: Don saboda albarkar noma,
: Mamman ya kyakkyauta ma,
: Ya
ba ni kuɗi don jin daɗi,
: Sai kiɗin
aikin noma,
: Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in riƙe galmata,
: Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in rike hauyata[3],
: Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in riƙe kwashena,
: Mun jeki wajen gayya,
: Ka duka na duka Sani,
: In nag gaji in mikewa ta,
: In ɗau
kwano mai dama,
: In tai kiran mai yin noma,
: Allah kawo Mamman Sani.
‘Y/Amshi: Mamman Sani,
: Babin noma.
Jagora : Ɗan maje can zan kwana,
: Dan in ga buhun dawa zalla,
: Ɗan maje can zan kwana,
: Ga buhuhuwan wake,
: Sannan sai kuma shinkahwa,
: Mamman Sani ya bakkani.
‘Y/Amshi: Hali na duniya mamman Sani,
: Birnin Kano ma na noma,
: Birnin Sakkwato ma na ji suna noma,
: Kuma na duba Mamman Sani,
: Hali na duniya Mamman Sani.
Jagora : Ka
ji ka dakata kai mai turu,
: Ga maganar aikin noma,
: Lallai arewa to duk baki ɗai,
: Mamman ka ga ana noma,
: Gara mu miƙe mu yi noma,
: Don ko noma darajar ɗanɗa,
: Amma ƙato in yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Ba ni kula samnan banza.
Jagora :
Amma ƙato yaz zan bai
noma.
‘Y/Amshi: Shi da buhun taki duk dai.
Jagora :
Wannan maganar dai-dai,
: Ka san ai ban maganar,
: Ka san ni ban maganar banza,
: Sai dai ni in maganar tsishi,
: Mamman darajar noma,
: Ka ga riga mai dama,
: Mamman darajar noma,
: Ka ga wando mai dama,
: Mamman darajar noma,
: Ka ga hula mai dama,
: Ga kuma mota baki dai,
: Ga mata Mamman Sani,
: Mamman darajar noma,
: Amma kato in yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Ba ni kular samnan banza.
Jagora :
Sai kato in yaz zan bai noma,
‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duɗ ɗai,
: Sai kato yaz zan bai noma,
: Ba ni kular samnan banza.
Jagora : Yawwa.
‘Y/Amshi: Mamman Sani,
: Mamman Sani,
: Mamman Sani,
: Babin noma.
: Kuma Ɗan Ige ban raina mai ba,
: A taɓuka
ma na fili,
: Na faɗi
lawali bizi nauwa,
: Ya biyani alheri yam man,
: Usman ban rena mai ba.
Jagora :
Ali na mani kotoko alheri yam man,
: Mamman darajar noma,
: Lallai ko ya kyauta ma,
: Kudin ka shi yab bakkani,
: Ya
ba ni kudi don jin daɗi,
: Ku dakata don rabbani,
: Bayan na ji kiɗin noma,
: Nay yi kiɗi nab bi,
: Mamman duk ko baki dai,
: A hankali kai mai turu,
: Ko da ilimin mallan kay yi,
: Kai koda tukin mota kay yi,
: Aikin gwamnati ka riƙe Sani,
: Mammam tai ka yi noma,
: Ƙato yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Ba ni kular shirgin[4]
banza.
Jagora :
Lallai ƙato yaz zan bai
noma.
‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa duɗ ɗai.
Jagora :
Yawwa.
‘Y/Amshi: Ɗan Haruna Zariya na noma,
: Birnin Tureta nake kwana,
: Sarkin tasha ya kyauta min,
: Sarkin tasha ya kyauta min,
: Ɗan Haruna mai Allah sarki,
: Ya biya ni kan halin noma,
Jagora : Ka
ji sarkin ƙaya ya kyauta
min,
: Lallai ko ya kyauta min,
: Don ko na Maradun na komai[5],
: Mamman ya kyauta min,
: Ya
ba ni kuɗi don jin daɗi,
: Mamman ya kyauta min,
: Ka ji kansila ka kyauta min,
: Babba Ibrahim ka ga ƙarin kuɗɗi,
: Adalilin babin noma,
: Mamman ko ban noma,
: Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in rike hauyata,
: Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in riƙe kwashe[6]na,
: Mamman ko ban noma,
: Bari Mamman in rike galmata,
: Mun je mu wajen gayya,
: Ka duƙa na duƙa
Sani,
: In nag gaji in miƙewata,
: In ɗau
kwano to Sani,
: Na tai kiran mai yin noma,
: Alheri shi ne yam man,
: Hassan ɗan
bawa yana komi,
: Ɗankurmi can zan kwana,
: Tsontsomawa can zan kwana,
: Amma saboda na ji suna noma,
: Aikin noma am mai daɗi,
: Amma kato in yaz zan bai noma,
‘Y/Amshi: Shi da buhun kowa[7]
duk ɗai,
Jagora :
Lallai kato yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Ba ni kular shirgin banza.
Jagora : Amma kato yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Ba ni kular samnan banza.
Jagora :
Amma ƙato yaz zan bai
noma.
‘Y/Amshi: Shi da buhun taki duk dai.
Jagora : Amma ƙato
yaz zan bai noma.
‘Y/Amshi: Ba ni kular shirgin banza.
Jagora : Yawwa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.