Ticker

6/recent/ticker-posts

Audu Kana Da Geron Daka

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma 

Audu Kana Da Geron Daka

 

 G/ Waƙa: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.

 

  Jagora: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.

‘Y/Amshi: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.

 

  Jagora: Baban Muntari,

‘Y/Amshi: Mai baje ƙasa ta baje,

: Da ƙarhi kake.

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.

 

 Jagora: Jikan Magaji,

: Ɗan Magaji,x2

‘Y/Amshi: Na Bawa,

: Ma’aikaci sai duhu.x

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.

 

 Jagora: Mu tai Sado[1],

: Mu ishe Maikano. X2

‘Y/Amshi: Mu ba shi kiɗi,

: Ya san mun iya.x2

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.

 

 Jagora: Baban Muntari,

‘Y/Amshi: Mai baje ƙasa ta baje,

: Da ƙarhi kake.

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka,.

 

Jagora: An yi wuta kura ta biya,

: Ta ga awaki sun toye,

: An ko ja an kai daji,

: Ta ce arha gasassa,

: Na ci ɗanye balle wanga,

‘Y/Amshi: Nan muka shirin baye duniya,

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka,.

 

 Jagora: Jikan Magaji Ɗan Magaji,

‘Y/Amshi: Na Bawa,

: Ma’aikaci sai duhu.

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka,.

 

  Jagora: Baban Muntari,

‘Y/Amshi: Mai hwashe ƙasa ta baje,

: Da ƙarhi kake.

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.

 

 Jagora: Mu tai Sado,

: Mu ishe Maikano.

‘Y/Amshi: Mu ba shi kiɗi,

: Ya san mun iya.

: Ya yini gona Ɗan Amadu,

: Audu kana da geron daka.



[1]  Sunan wani gari ne na cikin ƙaramar hukumar Talata Mafara.

Post a Comment

0 Comments