Bala Makigudu

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Bala Maƙigudu

     G/ Waƙa: Ya bi maza da mania magirma,

     : A gaida bala Dauda ɗankanen sarki.

     

    Jagora  : Bala maƙigudu mai darza ɗauri ɗaurarre,

    : Darza za garka su alkali,

    : Balan rufa-rufa maganin duhu yayi,

    : Allah waddan ka gyara ɓatacce,

    : Ai ko da kayita gyaranta kayi kan banza.

     

    Jagora : Allah waddan ka va ta gyararre,

    : Ai ko da kayita kanarki kayi kan banza,

    : Allah waddan kawa biri burtu,

    : Ai ko da kayi shi dai kaga ya sani kayyi.

     

    Jagora : Ai biri na allamu dai ya daɗe da wayonai,

    : Yana bias dai kallon mutum ya kai banza,

    : Sai ya fyaɗe mutum nata waige-waige nai,

    : Arnen gonar da ba dame jaki,

    : Ai sadda ki bi shi kullum kiran shi dango nai,

    : Su dango an fara danganar banza,

    : Sai ta dangana wa zani kaba lada?

    : Bahillace babu nagge sai jiɓi,

    : Su chigi ba asha hurar mahauta ba.

     

    Jagora : Ai ka ga baya ga rorun tsu baya babu banza,

    : Nan ya ka gugar tsoda na tohi nai,

    : Ai ɗiyan runji sai su ce yana kallo,

    : Bai wuce ƙarya ba tunda ba shanu,

    : Matar ragoo ta sha bakin cikin banza,

    : Ya bar mata ta na da sabaɗi[1],

    : Ubanshi in ta ƙwaraita yana sabattashi,

    : Shi dai abasshi da ibar wuta yana kuka,

    : Ai gaya ɗauke da ihi kamar kofar kura,

    : Allah waddanka gungumen banza.

     

    Jagora: Allah waddanka gungumen banza,

    : Sannu bala dau sannu daurarre,

    : Bala ina madarawa ke nawa sabko,

    : Ai saka zunzuri ta ika zuwa gona,

    : Da kada a sari dauri ta ida zuwa gona,

    : Tan arewa ida zuwa gona,

    : Hat anyi isha’i dab dawa gona,

    : Mu tambayi Lami hanyar da zamu bi sauƙi,

    : In dai bayannai su sunka amsai ba,

    : Don mu ga ne har da zamu iskeshi,

    : Tunda dai makiyayin amale bai kwana,

    : Ya gaji muhammadun jibo dai-dai,

    : Ai Balarabe ko tsino bai ragekke ba,

    : Darzazan zarza sai duhu gona.



    [1]  Yawon banza, wato yawon ba aikin yi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.