Barkwanci

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

     Barkwanci

    “Barkwanci zantuttuka ne na raha da wasu mutane waÉ—anda Allah ya hore wa iya raha da magana da bandariya ke wa jama’a”. ÆŠangambo, (1984:50).

    A bisa bayanin da ya gabata ana iya cewa barkwanci na nufin kawo wasu zantuttuka saɓanin yadda aka san su a cikin labari ta yadda mai ji ko gani ya yi mamaki har wani lokaci ya ƙyalƙyace da dariya. Mabarata kan yi amfani da irin wannan a cikin waƙarsu idan suna bara. Misali:

     Kura ta ga ÆŠan bara É—an almajiri,

     Bari in bika É—an bara in shawo gari,

     Tahiyata da taki ba ta zama É—ai da É—ai,

     Ni roÆ™o nikai ga mata ‘yan arziki,

     Ke Æ™wace ki kai ga mata ba su ba ki ba,

     (Daudun bara)

     

    A cikin wannan waƙa akwai barkwanci, domin a cikin firar da ta gudana tsakanin daudun bara da kura maganganu ne na barkwance masu nuna ƙyama ga wasu halaye na kura waɗan da suka hana daudu yarda da ya abuce ta.

    A wata waÆ™ar ta “ÆŠan na birgi-birgi” ana cewa:

     Jagora: ÆŠan na burge – burge,

     Amshi: Burge

     Jagora: Ga Inna ta yi baÆ™i,

     Amshi: Burge,

     Jagora: BaÆ™in da ba su Æ™oshi,

     Amshi: Burge,

     (Burge)

    A ɗa na shida da na bakwai akwai barkwanci, wato kalamai masu rikitar da tunanin mai sauraro masu nuna ga wani da abinci kaɗan ba ya isarsa har yana iya cinye ƙaiƙayin dame talatin kafin wataƙila ya ƙoshi. Ko dabba da aka sani da ci ba ta iya cinye abin da shi yake ci kuma babu tabbacin ya ƙoshi don ya ci shi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.