Ticker

Bature Na Mainasara

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Bature Na Mainasara

 

 G/Waƙa: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

 

Jagora: Ya zo da shirin,

: Gyaran[1] gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

. ‘Y/ Amshi: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

 

Jagora: Gidan Bature nikai,

: In gaisai.

 ‘Y/ Amshi: Komi nika so,

: Sai ya yo man.

 

Jagora: Gidan Bature nikai,

: Sarki.

‘Y/ Amshi: Komi nika so,

: Sai ya yo man.

: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

 

Jagora: Kartau! [2]

: Kartau!!

: Kartau!!! Noma yai.

 ‘Y/ Amshi: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai mai.

 

Jagora: Gidan zagi niz zo,

: Don mu ishe[3] mai.

: Na Ɗanmasani.

 ‘Y/ Amshi: Komi nika so,

: Sai ya yo man.

 

Jagora: Gidan zagi niz zo,

: Don mu ishe mai.

 ‘Y/ Amshi: Komi kaka so,

: sai ya yo ma.

Jagora: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai mai.

 ‘Y/ Amshi: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai mai.

 

Jagora: In Allah ya yi ruwa,

: Bature.

: Na Mainasara,

: Tsari gonakka,

 ‘Y/ Amshi: Ka tara dame,

: Shi ad daidai.

: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

 

Jagora: In Allah ya yi ruwa,

: Na Mainasara,

: Tsari[4] gonakka.

 ‘Y/ Amshi: Ka tara dame,

: Shi ad daidai.

: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

 

Jagora: Sai godiya,

: Mai kiɗi,

: Ban raina ba.

 ‘Y/ Amshi: Halin a yaba,

: Yai man kullun.

 

Jagora: Kartau yo gaba,

: Ga rana ta yi.

. ‘Y/ Amshi: Kartau yo gaba,

: Ga rana ta yi.

: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

 

Jagora: Ni dai Aminu,

: Na gode mashi.

 ‘Y/ Amshi: Halin a yaba[5],

: Yai man kullun.

 

Jagora: Ni dai Aminu,

: Ban rena mai ba.

 ‘Y/ Amshi: Halin a yaba,

: Yai ma kullun.

: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.

 

Jagora: Wada nika son,

: In ga sarkin noma,

: Haka nig ga ka,

: Bai zan ƙarya ba.

: Kartau da dame.

‘Y/ Amshi: Kartau[6] babu dame,

: Ya zan banza.

: Ya zo da shirin,

: Gyaran gona,

: Na Mainasara,

: Noma yai ma.



[1]  Yin aikin gona,

[2]  Suna ne da ake yi wa babban manomi musamman mai duƙawa ya yi noma.

[3]  Iskewa, ka tarar da mutum ko wani abu a wani wuri

[4]  Riƙa zuwa tare da kulawa da gyarawa.

[5]  Kyauta.

[6]  Manomi.

Post a Comment

0 Comments