Bishiyar Zumunci

    1. Rabbana ka ji ƙan zumunci,

      Don a yau mun ruguza shi.

     

    2. Babu mai duba gare shi,

      Ko ya ce zai É—abbaka shi.

     

    3. Ga shi Allah yai bayani,

      Kansa domin mu riÆ™e shi.

     

    4. Ya yi alƙawari na narko,

       Gun waÉ—anda suke katse shi.

     

    5. ÆŠaha ya yi kira gare mu,

       A Hadisai don mu yo shi.

     

    6. Ya faÉ—o falalar zumunci,

      Da azaba in ka Æ™i shi.

     

    7. Yau idan ka tsaya ka duba,

       Duka ba ma aikata shi.

     

    8. Mun yi watsi da zumunci,

     Babu mai neman a yo shi.

     

    9. Har iyaye namu mata,

       Da yawa sun bar batun shi.

     

    10. Ba su yinsa saboda Allah,

    Ya zamo tamƙar farashi.

     

    11. Wanda yai shi za su yi wa,

      Sun cire Allah cikin shi.

     

    12. Wasu dangi ne guda É—ai,

     Babu wanda ya yo zaton shi.

     

    13. ÆŠan'uwa ne shi na wane,

     Ko idan an tambaye shi.

     

    14. Kuma wando nasu É—ai ne,

       Gun zumunci ba su yin shi.

     

    15. Wani wa ne da ƙaninsa,

      Kan kudi suka tarwatsa shi.

     

    16. Rabbana ka ji ƙan mutan da,

    Gun zumunci babu ƙyashi.

     

    17. Su a loton ba salalu,

      Ga zumunci sun riÆ™e shi.

     

    18. Za su É—au harama a jaki,

    Duk gari sun zagaya shi.

     

    19. A yi ziyara a yi zumunci,

       Ba su cewa wane ba shi.

     

    20. Suka rayuwa cikin sallama,

    Arziki aka yalwata shi.

     

    21. Mu ko yanzu idan ka duba,

      Ba zumunci mun kashe shi.

     

    22. Shi ya sa yau ba lumana,

    Ga talauci ya yi goshi.

     

    23. Ga masifu sun yawaita,

       Tun da mun Æ™i faÉ—in na Arshi.

     

    24. 'Yan uwana sai mu tuba,

       Mu yi zumunci ban da Æ™yashi.

     

    25. Kar mu ware guda a dangi,

       Ko mu ce ai wane ba shi.

     

    26. Muyi zumunci don Azizu,

    Don mu tsira a ranar tashi.

     

    27. Nan nazo ƙarshen kasidar,

    Wacce nayi akan mu tashi.

     

    28. Watakil wani zai su'ali,

      Wa ya yo baiti da shi - shi.

     

    29. ÆŠanbala suna Mohammed,

       Can a Borno cikin garin shi.

     

    30. A watan Ramadana yai yo,

       Sha biyu ga wata batun shi.

     

    31. Hijirar sha huÉ—u arba,

     Da huÉ—u a cikin yabon shi.

     

    32. Wanda yai daidai da ukku,

      Ga watan April ku ji shi.

     

    33. Ashirin, Ashirin da ukku,

       Haihuwar Isa ogan shi.

     

    34. Rabbana ninku salati,

    Gun mafi daraja da kamshi.

     

    35. Alihi nasa har Sahabu,

    Sun bi Annabi babu kaushi.


     www.amsoshi.com

    Na:

    Mohammed Bala Garba
    12 Ramadan, 1444.
    3 April, 2023.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.