Dan Nan Kulmen da ac Cikin Gurbi ya Ansa Gaisuwa

    Dan Nan Kulmen da ac Cikin Gurbi ya Ansa Gaisuwa

    "Dan nan niko ina gaton gaɓa niƙ ƙwala gaisuwa,
    Su ko sun daƙile ni dut,
    Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi ya ansa gaisuwa..."

    Inji Makaɗa Sa'idu Faru ɗan Makaɗa Abubakar Mai Kotso (Abubakar Kusu) ɗan Makaɗa Alu Mai Kurya a cikin faifan sa mai amshi 'Gwabron Giwa Uban Galadima ɗan Sambo ginshimi, Gamshik'an Amadu Na Maigandi kai aa Uban Zagi' wanda ya yi wa Marigayi Mai Girma Dagacin Banga da ke Ƙasar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar wanda ya yi sarauta daga shekarar 1934 zuwa rasuwar sa a cikin shekarun 196Os. Ga Kifi nan a cikin Gurbi na Ruwa dake Kogi, Makaɗa Sa'idu Faru yana nufin daga cikin Kifin/Kifayen da ke irin wannan Gurbin ne da yake tsaye a kan gaɓar sa a lokacin da yake miƙa gaisuwarsa ga Tsuntsayen da ya taras a Kogin suna sa-in-sa, watau su Jinjimi da Tuji da Bubuƙuwa ƙila ma saboda lamarin ya yi tsamari ne a tsakaninsu shi ne dalilin da ya sa ba su ansa masa gaisuwarsa ba, sai da Kifin/Kulmen da ba da shi a cikin matsalar ba ya ansa masa. 😂🙏

    Daga Taskar

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    Ɗanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.